BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 80

80

………..Ranar suna yarinya taci suna Ai’shatul-Humairah ataƙaice anma Mamie takwara dai. Kowa yaji matuƙar daɗin karar da Shareff ya nuna. Shiko yace yayine saboda Mamie uwace a garesa da bazai taɓa mantawaba. Mommy haihuwarsa kawai tayi, amma badan ALLAH yasosa da rahamar komawa hanun Abie da Mamie ba da yanzu bama asan yaya rayuwarsa take ba. Ga kawunsu nan Umar har kowama ya manta da shi a cikin zuri’arau.
      Tabbas burin su Abie ya cika wajen haɗa gagarumin taron suna daya sake tabbatarma da duniya wanene Abie ɗin. Ashe duk wani waiwai da akeji a bayan kan dukiyarsa abin ya zarce hakan. A ranar ya mallaka company ɗin dake hanun Shareff ga Anaam ɗin da Shareff halak malak, sannan ya ajiye wata gagarumar ƙyauta ga jaririya Aysha Humairah data girgiza kowa a wajen taron nan. Dan Mommy gaba ɗaya neman susucewa tayi saboda ta halarta itama bisa jagorancin Baba Ibrahim. Gwaggo Halima kanta a ranar jikinta ya ida yin sanyi da lamarin Abie. Dama gata a firgice da ganin Amaryar Baban Su Fadwa da a yaune suka fara ganin juna. Da kuwa sai dai ta ganta a television. Taci kuka matuƙa kamar yanda Mommy itama taci nata. Fadwa kam dama dai batazo ba. Amma hakan bai hanata gani a wayoyin mutane dama television da aka nunaba har a NTA. Itama dai ranar batai kwanan lafiya ba, dan kyarshe dai sai dama aka bar ƙasar da ita a washe gari saboda ciwonta yay matuƙar tashi fiye da ko yaushe. Hakanne ya sake birkita Gwaggo Halima ta koma kamar ƙaramar mahaukaciya. Abin tausayi abin dariya.
       Amaryar jego da angon jego kam sun sha ƙyau har sun gaji, dan kuwa kallo guda zakai musu kasan naira tayi kuka. Sati biyu dayin suna su Abie suka ɗauke Anaam sai malaysia. Shareff bai soba amma haka ya dake ya daurema ransa. Abinda ya ɗan ƙara sauƙaƙa masa zuciya ganin Mommy ta matuƙar sakkowa a yanzu, sai dai bayajin daɗin zagin da ake mata a dangi game da watsar da Gwaggo dake a cikin mawuyacin hali. Dan anyi aikin ƙafar an guntule, yayinda likitoci suka gano kuma tana ɗauke da kansar jini bayan ciwon zuciya mai tsanani. Kullum cikin kuka take na rashin samun haihuwa, dan kuwa rashin kulawa daga Mommy na matuƙar caccakar ruhinta. Ga ƴan uwa kuwa dama babu ta inda bata zama fitilar sharri data haska kowa ba. dan haka kowa ɗin gudunta yakeyi, tunda ma wadda ta riƙa tamkar ƴarta ta gujeta waye zai tsaya. Su dama ƴaƴan Baba Ibrahim da matansa basu zurfafaba. Iyaka su basu abinci su koma gefe, dan hatta Mommy mai lafiyar ma ba daɗin zaman gidan takeji ba sam. Sai dai babu yanda zatayi tunda nan dinnne kawai da ita ai. Idan tace zata barsa ina zataje. Da kunya dai ta koma gidan ƴaƴa ta zauna. Ita da Gwaggo Halima kam gaba sai abinda yay gaba. To take jerama Gwaggo ma ALLAH ya isa dake matsayin uwa gareta balle bare.

       Watannin Anaam biyu Shareff ya kasa haƙuri yay shiri yabi bayansu. Babu zato ko sanin zuwansa kawai sai gashi, a lokacin Anaam na falo zaune tana shayar da Muhseenah. Haka suke kiran babyn dashi. Mamie na gefenta tana gyara mata dan har yanzu bata iya komai yanda ya kamata ba. Abie na daga tsaye a ƙafar upstairs yana musu dariya dan Anaam ɗin na darune wai ita yarinyar ta cika ci ita kuma ta gaji. Sallamar Shareff ta sakasu kallon ƙofar kusan lokaci ɗaya, sai dai kowanne zuciyarsa taƙi gaskatawa sam. Abie ne yay ta maza yaje ya buɗe ƙofar. Ya waro idanunsa sosai da faɗin, “Son! Kai ne ɗin dai da gaske?”.
    Murmushi Shareff yayi idanunsa a ƙasa, zai rissina domin gaisheshi Abie ya jawosa jikinsa ya rungume. “Ja’iri ka manta gaban Abie ɗinka kake?”.
        Murmushi yayi dajin ƙaunar Abie ɗin matuƙa. Suka ƙarasa cikin falon inda suka iske Mamie riƙe da Baby Muhseenah da Anaam ta manna mata ta gudu sama tun jin Abie ya Ambaci sunan Shareff. Cike da jin nauyi da kunya ya ƙaraso gaban Mamie ya durƙusa. Mamie dake murmushi tace, “Oh oh Babana miye haka. Tashi mana ni bana son wannan sinne sinnen kan, ko baka iyayen damune yanzun ka ɗauka wani babi daban kuma?”.
     Da sauri ya girgiza kansa. Mamie tace, “Ato gara dai ka gyara kafin mu fara fushi da hakan”. Ta kare maganar da miƙa masa Baby. Gani yay ta ƙara masa girma da wayo, wataninta uku kenan a duniya, kamaninta da Anaam ya sake bayyana matuƙa. Abubuwa ƙalilanne nasa ta kwaso. Ya rungumeta a ƙirjinsa yana maijin sonta da ƙaunarta ta musamman, kafin ya kai lips dinsa ya sumbaci goshinta yana mai ambaton , “ALLAH yay miki albarka NoorulAyn”.
     “Amin ya rabbi”. Abie dake ta bayansa batare daya sani ba ya amsa masa. Ji yay duk kunya ta lulluɓe sa. Amma tuni Abie ya kaudata ta hanyar zama kusa da shi. Dai-dai nan Mamie ma ta dawo ɗauke da tray tana murmushi….

     Duk yanda yaso ganin gimbiyar tasa taƙi bashi daman hakan. dan ƙiri-ƙiri taje ɗaki ta ɓoye abinta, har yaci abinci ya gama bata fito ba. Mai aiki ta kammala gyara masa ɗakinsa dake gidan ya shiga domin watsa ruwa ya ɗan huta. Sai dai kuma hakan ya gagara. Wankan kawai ya iya yi ya fito cikin sanɗa. Sai da ya tabbatar su Abie basa a falon yay wuff sama ɗakin Anaam..
        Tana kwance rigingine ta kifa Muhseenah a saman cikinta waya manne a kunnenta, yanda taketa faman murmushi zai baka tabbacin wayar na sakata nishaɗi. Dan ko motsin shigowarsa ma bataji ba. Ɗakin yana a yanda ya sanshi, komai na cikinsa kalar da tafi so da ƙauna. Tsaf cikin ƙamshi. Sai dai an samu ƙarin wasu abubuwa na Muhseenah. A ɗan zabure ta buɗe idanunta dake lumshe jin an ɗaga yarinyar daga jikinta, cikin ido suka kalla juna, ta lumshe nata tare da ƙoƙarin kaudasu gefe tana sallama da Aysha da suke wayar, wadda itama take faman da laulayin ciki a yanzun. Kwance ya kai kusa da ita shima tare da ɗaura Muhseenah a saman cikinsa kamar yanda ya samesu. Tai ƙoƙarin tashi ya jawota jikinsa.
    “Kai Yaya”.
“Shiiii!!. Ni kikema wulaƙanci ko?”.
Baki ta tura gaba, “Ni wulaƙancin mina maka?”.
  “To fushi ne?”.
Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan, sai ta fara masa kukan ƙarya. murmushi yayi da sauke Muhseenah gefe ya rungumeta jikinsa da ƙyau har sai da ta saki ƴar ƙara, kafin ta sami damar cewa wani abu ya manne lips ɗinsu waje guda ta yanda abinda take son faɗa bai sami damar fita ba. Tun tana masa bori harta amsa ɗari bisa ɗari. Sai da suka cakuɗa junansu matuƙa tafiya zatai nisa Baby Muhseenah ta fara kuka. Da ƙyar ya iya raba jikinsu ya ɗauketa. Ya lakace mata hanci da sumbatar goshinta cikin furzar da numfashi. “Mamana am sorry laifin mamanki ne fa”. Yay maganar yana kallon Anaam. Hararsa ta ɗanyi da juya musu baya. Yay murmushi. Itama dai koda ta juya ɗin murmushin takeyi, ƙaunarsa na sake ratsa mata dukkan jijiya da ɓargon jiki. Sai da ya tabbatar Muhseenah ta koma barci sannan ya sake kwantar da ita ya kwanto jikin Anaam da duk tana jinsu, a tare suka saki ajiyar zuciya.
      “Kazo lafiya?”.
   “Baki so sanin hakan ba ai”.
“To amma Yaya zakazo koka sanar min, sai kawai na ganka kamar daga sama?”.
      “Dama idan mutum zaizo gidansu sai ya shelantama duniya zaizo?. Noorie na na kasa haƙurine kewarku ta isheni ALLAH”.
   “Ni ban yarda ba”.
“Sai na nuna a aikace kenan?”.
Da sauri ta zabura dan tasan ina ya dosa. Ya fara dariya yana maidata ya matse. “Kefa na fahimci matsoraciya ce ALLAH”.
   “Ai tsoro halak ne kuwa, ina zan iya da kai da wannan yankan a jikina. Nifa ba ruwana yanzu an daina wannan dani kaje ka dawo da Fad….”
   Ganin fuskarsa ta tsuke lokaci ɗaya ta haɗiye sauran maganar. Ƙoƙarin janye jikinsa yay a nata ta sake lafe masa. “Miye kuma na tsuke fuskar? ALLAH ko ƙyau bakayi”.
     Muryarsa a ɗan tsaurare yana mai kallon tsakiyar ƙwayar idonta. “Idan ina tare dake bana buƙatar maganar wata, inba hakaba zan hukuntaki”.
   “Am sorry sir, baza’a sake ba ok”.
Ta faɗa tana mai sakar masa kiss a ƙirjinsa. Dole ya saki ajiyar zuciya da sake ƙanƙameta tsam dan dauriya kawai yakeyi. Cikin kunnenta ya raɗa mata, “Zaki rakani wani waje?”.
     Itama a hankali tace, “Ina kenan?”.
“Ba’a faɗa ai”.
   “Mu cema su Abie mi?”.
Cikin tsakkiyar ido yake kallonta yana murmushi. “Zaki raka mijinki mana”. Sosai ta waro masa Raunanannun idanunta dake cikin gilashi. “Tab badani ba wannan ta’asar”.
       Murmushi yayi mai bayyana haƙora sosai, “Shikenan sai muyi zamanmu anan ɗakin kawai to”.
   “Kamar ya?”.
“Kamar yanda kikaji mana. Kina nufin zan iya cigaba da haƙurin nesanta kaina da zumata. Ina kewar garden matuƙa autar mata”.
    Sosai maganar ta bata kunya, ta cusa kanta a ƙirjinsa. “Ni dai babu ruwana ALLAH”.
        “Shiyyasa naga kina maƙaleni”.
Turesa ta farayi yana riƙota suna dariya. “Wasa nake Sarauniya. Ai ke Ustazah ce na sani babu ruwanki, Mamana ma fa a ruwan gidanmu kika shata”.
    Dariya takeyi sosai da kai mata ƙananun duka yana ƙoƙarin riƙe hanun shima yana dariya. Haka suka kasance a cikin ɗakin tare cikin farin ciki mara misaltuwa har sai da akai kiran sallar magrib. Koda ya fito suka haɗu da Abie sai yayta sinne kai. Shiko Abie yay tamkar baima fahimcesa ba. Atare sukai dinner cike da farin cikin. Muhseenah na jikin Abie. Anaam da Shareff sai faman zinguran ƙafan juna sukeyi ta ƙasan table. Daga Mamie har Abie na lure da su sai dai babu wanda ya nuna ya gani ɗin har aka kammala. Falo suka dawo aka buɗe sabon babin hira cike da farin ciki irin na kammaluwar family. Anaam ce ta fara guduwa dan ita bata iya doguwar hira ba, Mamie ma ta ɗauka Muhseenah dan tai mata shirin barci tabar Abie da Shareff. Sun ƙara ɗaukar lokaci suna hira kafin su tashi suma.
    Duk yanda yaso yin barci sai ya kasa, haka yayta juye-juye cikin tausayama kansa. Ya kira Anaam kuma bata ɗagaba, yasan tayi barci dan ita kasa ce bata jimirin doguwar hira. Kasa jurewa yay ya miƙe ya fita, gidan shiru alamar kowa yayi barci, ɗakin Anaam ya shige cikin sanɗa. Tuni kuwa tayi barci abinta, bayan ya shafa kan Muhseenah dake barci cikin ɗan gadonta ya haye gadon tare da ɗage lallausan duvet ɗin da take ciki ya shige abinsa. A jikinsa ya nutsata yana mai sauke ajiyar zuciya, itako da bata san yanai ba tuni ta gyara kwanciya da sake shigewa jikinsa. Sake ƙanƙameta yay yana maijin nutsuwa na saukar masa. A ransa kam yana godiya ga UBANGIJI ne daya mallaka masa wannan halittar daya girma da sonta da ƙaunarta mara misali a zuciya da ruhi, yana fatan su tabbata tare har ƙarshen numfashi batare da wani gagarumin saɓani da zai taɓa zuciya ba………✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button