BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 81

81*

………Da asuba yay wuf ya koma nasa ɗakin, lokacin da Abie ya sakko ƙasan har yayi shirin massallaci suka fita tare. Koda suka dawo anan falo suka zauna shi da Abie suna tattauna abinda ya shafi company har gari yay haske.
Mamie na Kitchen tare da mai aiki suna haɗa breakfast Anaam ta fito. Da ga Shareff har Abie kallonta suke da murmushi, ta miƙama Abie Muhseenah da itama akai mata gayu tanata zuba ƙamshi kamar uwar tata.
Abie dake murmushi ya lakace hancin Muhseenah. “To ni dai baza’a ɗauka hankalina da wannan kwalliyar ba. Matata ma ƴar gaye ce”.
Dariya Anaam da Shareff dake satar kallon juna sukayi, kafin Anaam takai zaune tana gaishesu. Ganin mayataccen kallon da Shareff ke binta da shi ƙasa-ƙasa ya sata barin wajen tana ɗan masa hararar wasa. Kitchen ta nufa wajen su Mamie ta cigaba da tayasu itama.

   Yauma kamar jiya tare sukai breakfast gaba ɗaya, kamar yanda Shareff ya kasa daina satar kallon Anaam haka itama ta kasa daina satar kallon nasa. Yauma dai iyayen nasu na lure da su. Dan haka suna kammalawa sun koma falo Abie ya maida hankalinsa ga Shareff. “Babana akwai aikin da zan turaka Indonesia kuwa, ni naso wucewa a yau sai kuma wata ta tasomin anan ɗin, kaga zuwan naka yamun daɗi ai, dan haka sai ku shirya zuwa dare insha ALLAH zaku wuce na kammala muku komai”.
  Gaba ɗaya Shareff ya daburce, dan kuwa abinda zuciyarsa ke raya masa Abie ya gama harbo jirginsa ne. Kafin ya samu damar yin wata magana Abie ya miƙa masa file ɗin hanunsa. “Duk abinda zaka buƙaci sani yana anan. Sai ku fara shiri ni yanzu zanje ana jirana....
  Anaam dai kanta a ƙasa dan itama ta tsargu, daga ƙarshe ma tashi tai tabar wajen kawai, tana mai jin cewa Shareff ya gama da ita kawai. (????kamar ba haka take so ba dama????)

 ★★Kamar yanda Abie ya faɗa a wannan dare suka wuce Indonesia, basai an tona irin farin cikin da suka tsinta kansu ba a ciki game da wannan tafiya, domin kuwa abin yazo musu ne tamkar wani gift da baka san mizaka gani a ciki ba. Ba wani kaya suka ɗiba ba, dan bama su san adadin kwanakin da zasuyi ba. Shareff na ɗauke da Muhseenah a kafaɗa Anaam na gefensa cikin abaya blue datai mata matuƙar ƙyau. Sai ƙaramin trolley da kayan Muhseenah sukafi yawa a ciki a hanunta. Dolene su burgeka domin kuwa sunyi matuƙar dacewa da juna. 
    Sun sami tarba ta mutuntawa ga wanda Abie ya tura musu, ya kwashesu zuwa masauki na musamman. Gidane madaidaici da komai na more rayuwa akwai a cikinsa. Komai tsaf fiye da yanda suke buƙata, hatta da abincin da zasuci an ajiye. Bayan wanda ya ɗakkosun ya gama nuna musu tsarin gidan yay musu sallama ya wuce. Shareff ya rungumo Anaam yana murmushi. “Yarinyar nan Abie ya riga ya harbo jirginki shiyyasa ya turomu nan”.
  “Ya dai harbo jirginka Yaya, zaka ƙala mun ni salihar nan dani”.

Ta faɗa tana mintsininsa da dariya. Dariyar shima yakeyi da kaiwa zaune ya ɗaurata a cinyarsa. “Su saliha anji jiki fa, ALLAH har naji kunya kamar daga nan na gudu da ku Nigeria kawai”.
“Kaga sai Mamie da Abie su ƙara yarda bakajin magana”.
Kai ya dungure mata da faɗin, “Bama ji dai”.
Ta ƙyalƙyale da dariya tana mai ɗanewa saman jikinsa. Shima dariyar yake tayata da sake ƙanƙameta. Da ƙyar ya iya haƙurin sukaci abinci sukai wanka.
Tana zaune tana shayar da Muhseenah ya tasasu gaba yana kallo da murmushi. Birgesa suke matuƙa, ji yake kamar ya haɗasu ya haɗiye kawai ko zaiji sassaucin ɗunbin so da kaunar da yake musu. Ɗagowa Anaam tai cikin ɗan waro ido. “Oga karka saka ta ƙware mana”. Idanun nasa ya kauda yana mai sakin wani tattausan murmushi. Ta zunguresa da ƙafa kaɗan, ya sake ɗagowa yana kallonsu. “ALLAH murmushi namaka masifar ƙyau Yaya MM. Amma baka sonyi”.
Wani murmushin ya sake saki yana mai girgiza kai, ya ɗan juya idanunsa dake kallon tsakkiyar nata cikin wani salo mai nuna tsantsar ƙaunarta dake ransa. “Indai ke kina gani ai ya wadatar basai kowama ya gani ba bugun zuciya”.
Murmushi ta saki itama da gyara Muhseenah datai barci. Fahimtar bazatace komaiba ya sashi amsar Muhseenah ɗin daga hanunta, shine ya kwantar da ita tare da mata addu’ar barci. Ya ɗago bayan tayi barci dai-dai Anaam na shirin barci, igiyar rigar barcin da take shirin ɗaurewa ya riƙe. Ta kallesa kai a langaɓe tana marmar da idanu. Matsota yake a hanakali yana mai narkar da nasa idanun cikin nata, harya haɗe jikinsu waje guda. A tare suka sauke ajiyar zuciya, cikin salon shagaltar da ita ya zame rigar saman tai ƙasa ta faɗi, zatai magana ya ɗagata cak zuwa kan gadon yana mai manne lips ɗinsu waje guda. Dole ta haɗiye maganar ta amshe mijinta hannu bibbiyu cike da kewa da tsoron abinda zai iya biyo baya ita dake da ƴar laɓuɓuwar yarinya (????????kuji gulmammiyar yarinya fa).

Wannan dare ya kasance wani dare ne na musamman a cikin darare masu nisan zango. Dan kuwa Anaam da Shareff sun tabbatar ma juna suna kewar junansu mara iyaka. Muhseenah ce kawai ke taka musu birki idan sukai nisa. Washe gari ma tare suka yini manne da juna sai ƴar ɗiyarsu sanyin idaniyarsu. Babu mai damunsu koda a waya ne. Zuwa dare suka ɗan fita shan coffee.
Sai da suka kwana uku suna hutawarsu ana huɗu Shareff ya samu ganawa da wanda Abie ya turosa wajensa. A ranar suka gama komai da shi, ya kira Abie ya sanar masa an gama komai zasu taho gobe. Sai Abie yace suyi zamansu har sai garin ya ishesu dan kansu. Tabb ba’ace suyiba ma sunyi inaga an basu dama. Lokacine da suka kirashi na gwangwaje juna fiye da wanda suka riska a baya. Dan kuwa sabon babin Honeymoon aka buɗe tsakanin waɗan nan ma’aurata dake jin tamkar su haɗiye juna su huta. Basu da wata damuwa saita bama junansu farin ciki, sai Shareff dakan ɗan taɓa ayyuka ta system ɗinsa a wasu lokutan. Watansu uku cirrr a ƙasar Indonesia kamar wasa, dan da sunce zasu taho sai Abie yace su ƙara dai, sun zagaya wajaje da dama tare da yin hotunan tarihi kala-kala. Zuwa yanzu baby Muhseenah ta ƙara ƙyau da girma. Dan har zama anayi tayi ɓul-ɓul da ita abin sha’awa. Su Abie nata mamaki su kansu. Sati biyu sukai anan Malaysia bayan sun je sunma Aunty Mimi sati guda itama suka nufo Nigeria. Sun bar su Mamie da kewa mara misali, sai dai suma suna shirin zuwa Nigeria ɗin bikin Amrah da Muzzaffar insha ALLAHU. Dan yanzu sun ƙulle abinsu suma tunda Anaam ta kufce masa ya kama Amrah ya riƙe ram.
Tarba suka samu ta musamman ga zuri’arsu. Kowa sai nannan yake da su musamman Muhseenah. Gwaggo Halima ce dai bata zafafa ba, tana daga gefe dan yanzu ta zama sai a hankali, zaman gidan yay masifar isarta, badan bata samun komai ba, sai dan a girman shekarunta ya wuce na zaman gida. Ga mijinta yana ƙoƙarin ɗarewa kujerar mulki dan kowa na hasashen shine zai zama gwamna. A koda yaushe cikin nunasa akeyi shi da amaryarsa ƴar ƙwalisa. Wannan kaɗai ya isa saka zuciyarta a ƙunci, balle ga damuwar Fadwa da maimakon sauƙi kullum a cikin tashin hankali take, zuwa yanzu ita da kanta ta yanke shawarar duƙawa gaban Shareff da Mommy da su Daddy akan su tamaketa Fadwa ta koma ɗakinta koda ita bazata koma nata ba, Fadwa na cikin mawuyacin hali na rashin Shareff, babanta kuma yayi alƙawarin bazai taɓa roƙa ko tilasta Shareff maidataba sai in shine yay ra’ayin hakan a karan kansa. Kasancewar saukar safe sukai zuwa dare suka nufi gidansu daya sha gyara, dama su kawai yake jira da alama. Washe gari sukaje gaida Mommy aka kuma kai mata jikarta dan yanzu Daddy ya basu damar zuwa suga mahaifiyarsu kamar yanda Baban su Fadwa ma ya barsu zuwa ganin Gwaggo halima. Hakan duk ƙoƙarin Abie ne na ganin dai komai ya wuce. Sosai tausayin Mommy ya kama Anaam, dan duk ta zube babu ƙibar nan tata, tayi duhu sosai. A yanda ta tarbesu zai tabbatar maka ba Mommy ɗin da bace ba. Muhseenah kam tasha gata a wajenta har da su goyo. Sun shiga sun duba Gwaggo dake kwance ana faman jiyya. Tayi masifar tsotsewa a kwance, ɗakin da taken ko shiguwa bayayi saboda warin fitsari da takeyi, masu kula da ita dasu Daddy sukasa aka samo suna biyansu shi da su Abie sai sun gadama suke gyarata. Baba Ibrahim ba zama yakeba shiyyasa, matansa kuma basayi basa faɗa masa abinda ke faruwa. Anaam har hawaye tayi kasancewarta mutum mai tausayi, dan duk wanda yaga Gwaggo dolene ya tsarkake sunan ALLAH mai rinjaye akan komai. Sai ya barka yay maka talala kaita aikata tsiyatakun ka a ban ƙasa, randa ya shirya damƙarka kuwa hummm. Ga dai Gwaggo a halin ha’ula na jiyya, da za’a bata zaɓin mutuwa ko rayuwa zata zaɓi mutuwar ko zata huta akan wannan azabar da take a ciki. Sai dai mutuwarma ta zama mai tsada a gareta dan taƙi zuwa kwata-kwata. Kullum cikin hawaye take idan ta tuna irin rayuwar data taka a wannan duniyar, kishi ya rufe mata ido da raɗaɗin rashin samun haihuwa ta cutar da matan mijinta, bata taɓa son su Daddy ba a ranta, kamar yanda uwarsu ma ba sonta tai ba. Kawai dai lumbu-lumbu take mata, dan taso ace ta tarwatsa rayuwar su Daddy ne kamar Umar, yanda itama bata haihu ba su Umma karsu mora nasu ƴaƴan. Tsanar mahaifiyar su Abie kuwa ta ƙara ƙarfine a ranta saboda tausayi da kullum mijinsu ke nunawa a kanta, sai take ganin ai yafi son bebiya ma a kanta, dan bata damu yaso umman su Daddy ba ko karya sotan, ita dai kawai a sota ita ɗaya. Sai dai kuma har yabar duniya da son bebiyan data tsana ɗin ya tafi, shiyyasa tafi tsanar su Abie fiye da su Daddy. Babban burinta tarwatsa family din MD Shareff gaba daya, su dinga tsanar juna da sukar juna ta yanda bazasu taɓa morar kansu ba kamar yanda itama bata mora zama da shi ba tunda bata haihuba a wautarta, sai dai hakan bata kasance ba da yake UBANGIJI shine mai zartar da hukunci akan ƙaddarar kowa. Duk ƙoƙarin ka, duk walarka sai dai kayi a banza a wofi babu abinda ka isa ka saka ko ka hana a karan kanka balle rayuwar waninka. Ba Gwaggo kaɗaiba, duk wanda zai sakama ransa ganin bayan wani, ko taɗe rayuwar wani, ko ruguza nasarar wani, ko baƙanta hasken fuskar wani, to ya tabbata shine zai dawwama cikin rasa waɗan nan abubuwan a cikin nasa rayuwar, dan baka halicci wani ba baka isa zartar da komai a kansa ba sai abinda ya kasance a ƙaddararsa. (ALLAH ka rabamu da mummunar zuciya, ka nisantamu daga son kammu da son ruguza waninmu. Ka hanamu nasarar cutar da kowa koda a lafazin bakine ko kallo da ido. Duk mai burin taɗemu a rayuwa ALLAH ka zame mana garkuwa a tsakaninmu da shi. Ya rabbi ka wajabta tsoranka a zukatanmu da soyayyar ANNABIN mu ????????????).

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button