BABU SO 82
82*
………Ranar wata alhamis dake dai-dai da saura kwana ɗaya cikar shekarar Muhseenah ɗaya a duniya su Abie suka iso Nigeria domin halartar bikin Amrah da angonta Muzzaffar. Anaam tayi farin ciki matuƙa, dan itace taje tarbarsu da Shareff da Muhseenah. Anaam ce ke tuƙi Shareff na kusa da ita Muhseenah a cinyarsa. Sai gwaranci take da tsalle-tsalle a jikinsa ita a dole zatai magana, sai dai kuma babu abinda ta iya sai gunguni irin na alamar yaro mai son surutu. Babu baki amma tayi ƙafa, dan kuwa tana tafiya sai dai bata gama nuna ba. Shareff dake dariyar son tura masa biscuit da take a baki ya lakace mata hanci, “Mamana wai dole sai naci biscuit ɗin nan ne?”.
Anaam dake ƙoƙarin ɗaukar titin airport tai dariya da ɗan juyowa ta kallesu ta maida kanta. “Kunfi kusa ai, yanzu da nice da yanzu an fara ƙananun magana, da zaka tsunkule hanun ai data barka ko”.
“Oh oh Noorie bana son zuga, Maman tawa zan tsunkula. To anƙi”.
Ya ƙare maganar da sumbatar Muhseenah a goshi, ita dai dariyarta take tana ƙara mamuƙesa dan tsaye take a jikin nasa tsoronta karta faɗi. Anaam data cigaba da tuƙinta batace komai ba ta taɓe baki. Shiko zaunar da Muhseenah yay. “Sweetheart ɗina, idan kinga su Abie ki taka da ƙyau dan tun a airport ɗin nan nake son su san kemafa kin faso munyi ƙafa”.
Anaam ta kwashe da dariya tana ɗan dukan steering. “Badai girin-girinba ALLAH, kwaje wajen iyayi ku ci da ka”.
Shareff ya harareta, “Tufff bakinki ya sari kashi”.
Dariyarta ta cigaba dayi ita dai tana ƙoƙarin yin parking. Koda suka fito kai tsaye wajen da zasu tarbesu suka nufa, kowa ya gansu sai sun baka sha’awa su da ƴar ɗiyarsu.
Basufi zaman mintuna goma ba jirgin su Abie ya sauka, suka zuba idon dakon fitowarsu. Shareff na hango su Abie ya sauke Muhseenah, mi Anaam zatai inba dariya ba, ya dalla mata harara da kai mata mintsini ta kauce, su Mamie ɗinta ta nufa ta rungumesu. Abie dake dariya yace, “Oh oh mamana bata girmaba har yanzu dai”. Fuska ta ɓoye tana dariya, dai-dai nan Idon Abie yakai akan su Shareff. Mamie ya zungura itama. A tare suka sanya dariya.
Mamie tace, “Ayya ana mana yanga da tafiya, to mungani duk da bata nuna ba”.
Shareff dake ƙarasowa yace, “Haba Mamie karki bamu kunya gaban ƴan adawarmu”. Yay maganar da nuna Anaam. Dariya Abie da Mamie sukeyi, Anaam kuwa ta taɓe baki da faɗin, “Waifa dole da tsiya-tsiya sai an nuna muku sun fara tafiya, bayan basa iya taku goma zai sun faɗi”.
“Adai ringajin tsoron ALLAH hajjaju” Shareff ya faɗa yana harararta. Nanma dai dariyar sukayi, Abie ya ɗauka Muhseenah yana ɗagata sama, saita sanya masa kuka ita ƙiywa wajen Abbanta zata koma. Ya dungure mata kai, “Haba ƴar daru ni zakima ƙiywa, to garama mu daidaita tun anan dan indai nine kinta ganina kenan daga yau”.
Mamie dake dariya tace, “Kaima kenan. Balleni kishiya”.
Cike da farin ciki suka bar airport ɗin, kamar koyaushe sun sami tarba ta mutuntawa gasu Mom. Duk da dama dai Anaam ta shirya musu abinci na musamman a wannan karon da kanta itama. Ranar duk yanda Shareff yaso lallaɓata su koma gida ƙi tayi, dole ya barsu nan ya tafi shi kaɗai ya kwana cike da kewarsu. Dan yasan dai ba sake ganinsu a gidan zaiyi ba sai kuma bayan biki. Hakan yasa shima ya tattaro inasa-inasa washe gari ya dawo nan gida. Sam daga Anaam har Shareff basuyi waniyi niyyar yima Muhseenah birthday ba, amma sai ga bazata gasu Mamie dan da alama da shirinsu sukazo. Anko sha shagali mai ƙayartarwa, aka kuma sha hotuna masha ALLAHU. Ranar sai da Gwaggo Halima tai hawaye, dan haka kawai taji tana taya Fadwa jaje matuƙa. Mommy ma dai ba’a barta a baya ba sai da tazo, tunda tabar gidan wannan ne karo na farko da tazo, duk da kuwa kullum cikin yima Daddy waya take da bashi haƙuri kamar yanda Gwaggo Halima kema Daddyn su Fadwa. Da gaske sunyi laushi kowacce burinta a yanzu ta koma gidan mijinta. Shareff kansa da su Maheer kullum cikin bibiyar iyayen nasu suke, dan suna tausayawa Mommy sosai dake zaune a raɓe duk da baba Ibrahim yaya yake a gareta uwa ɗaya uba ɗaya. itace kuma tace subi umarnibsa na hanawa susai mata gida da yayi, tace zatai haƙuri ta zauna a gidan nasa.
An shiga hidumar biki, dan dama dai aunty Mimi sun iso tuni suna Abuja ne gidan yayan baban su Amrah ɗin. Suma sai juma’ar da akai birthday ɗin Muhseenah suka ƙaraso kano, sai dai acan gidan mijinta daya siya shima suka yada zango. Sosai biki ke bada citta, su Anaam ƙirjin biki babu zama ko ina sune. Bata da matsala da Muhseenah tana wajen Mamie, dan haka ta sami damar yin komanta hankali kwance har aka kammala biki amarya Amrah ta tare a gidanta da kowa keta sambarka.
Sai da Shareff yayma Anaam jan ido washe gari ta yarda suka koma gida. Sati biyu da gama hidimar biki akai taron family. Duk wani da ake buƙata ya hallara. Tun rabuwar Fadwa da Shareff sai yau ne suka haɗu da Anaam dama Shareff ɗin kansa, dan ya toshe duk wata hanya da zata iya ganinsa kojin labarinsa. Duk ta rame tayi wani irin sanyi. Anaam tayi kamar bata gantaba tanata ma Muhseenah data maƙale mata wasa, dan kuwa dai yanzu a hanun su Momie take tama yaye kanta, dama Anaam ɗin ta gaji sai hakan yay mata dai-dai. Fadwa ta tsira musu ido hawaye na silalo mata a kumatu, ji take inama Muhseenah tata ce. Hankalinta bai sake tashi ba sai da Shareff ya iso wajen. Yayi wani fresh da shi ga ƙiba da zama alhajin gaske da yayi, sai ƙyalli yake cikin shadda irin ta jikin Anaam ɗin. ko kunya bai jiba ya ƙarasa inda matarsa da ƴarsa suke. Duƙowa yay jikinta yana mai yima Muhseenah wasa tana ɓangale masa baki da miƙa hannu ita a dole ta gane Abbanta.
Anaam ta kallesa da murmushi. “ALLAH Yaya kai ne ka koyama yarinyarnan ƙiywa ba wani ba. Ita a dole duk inda ta ganka saita ganeka”.
“Toya son ranki? Jealousy woman”.
Ya faɗa yana mai kashe mata ido ɗaya. Murmushi tai baki a taɓe. “Fess mana, miye abin jealous anan nima nawa na zuwa zan rama”. Shima murmushi yay idonsa akan lipstick ɗin bakinta. Sarai ta ganosa, dan haka ta tura lips ɗin a baki ta shanye tas. Kafin fitowar nan tasu ta saka yafi sau biyar yana tsotsesa, yanzu ma anan gidan ta saka.
“Kije ke da ALLAH kuma zan rama”.
Ya faɗa cikin langaɓe mata kai. Dariya take gimtsewa ita dai, ya ɗauke Muhseenah suka bar wajen. Da kallo ta bisu cike da so da ƙaunar ƴar da uban.
Bayan kammala halartar kowa aka buɗe taro da addu’a. Abbah ya fara da nasiha mai ratsa jiki game da muhimmancin da zuminci keda shi a rayuwarmu, tare da son zuciya akan abinda kai baka isa sakawa ko hanawa ba a ƙaddarar waninka ko kai a karan kanka. Ya ɗora da roƙo da fatan su zama 1family, tsintaiya ɗaya maɗauri ɗaya. Tare da illar nunama juna wani abu wai shi ƴan ubanci. Ƴan ubancin nan babu abinda yake zama a family sai kassara rayuka da maidasu koma baya. Duk family ɗin da babu haɗin kai bazasu taɓa zama masu cigaba ba, dan kuwa zasuyita gabane suna taɗo juna akan ƙanƙanin abu. Sannan iyaye mata na Family ɗin su kiyayi kansu wajen tsaurara ƙiyayya tsakaninsu da ƴan uwansu har ƴaƴansu su fahimta hakan kuskure ne. Kowa yay haƙuri da ɗan uwansa yayin daya ɓata masa rai, dan mai haƙuri baya taɓa faɗuwa sai cin nasara a rayuwa. Su Abie sun isa zama manuniya a garesu. Sosai nasihar ta shigi kowa. Sai faman sauke ajiyar zuciyoyi akeyi musamman Gwaggo Halima. Bayan gama jawabin Abba Abie shima ya amsa. Ya ƙara da musu tashi mai ratsa jiki, tare da shawarar sakama yaranmu ido domin sanin abinda suke aikatawa a wayoyinsu. Dan sakacin rashin bibiyar shike saka yaran ɗoruwa a hanya irin wadda Fadwa tabi a baya. A yanzu tangal-tangal din tarbiyyar yaranmu ta riga ta koma ne a tsinin ƙaddarar yanar gizo da wayoyin hanu suka kawo mana, kenan ya dace iyaye su sakama wayoyin hannun ƴaƴansu ido, karkuma suce bazasu basuba dan in kin hanasu zasuje suga ta ƙawaye ko aboki ko saurayi, baki san kuma minene a ciki ba. Sannan tarbiyya babu ruwanta da inda ka taso, a duk duniyar da kake, a kuma kowacce ƙasa idan kaso ɗanka ya zama na ƙwarai zai zama. Bawai dole sai ya shiryuba, a’a ALLAH ne kaɗai mai shiryarwa, suma waɗanda nasu ƴaƴan suka kauce ba’a son ransu bane, karka ga