BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 61-65

Page 6⃣1⃣
to 6⃣5⃣

Bata zame ko ina ba sai gidan malamin ta haka ta kwashe komai ta fada masa,,kulli magani ya bata sannan yace mata ta tabbar fatima ta tsallake wannan maganin idan har ta tsallake shi cikin zai zube kuma itada kara haihuwa har abada,,,cikin murna ta ciro kudi ta bashi,,,

haka ta kara kamo hanya buguzum buguzum tana tafiya tana sake saken mugunta cikin ranta,,koda ta isa ta tarar da fatima zaune bakin dakin,,yaranta kuma kowa ya tafi yawon shi,,ko kallon inda fatima take bata yiba ta shige dakinta,,,ita dai fatima baiwar allah tunda ta mata sannu da zuwa taji bata amsa mata ba taja bakinta tayi shiru,,daga karshe ma dakinta ta shige tayi kwanciyar ta

asabe na daki amma sake sake take yi a ranta na yadda zata zuba wannan maganin a kofar dakin fatima,,,lekawa tayi taga tsakar gidan ba kowa komawa daki tayi ta dakko maganin sannan ta fito ta fara tafiya a hankali har takai kofar dakin fatima da take can daki tana barci bata san wainar da ake toyawa ba,,,,bude kullin maganin tayi sannan ta barbada shi a duk kofar dakin sannan ta juya ta koma tana murmushin nasara…

kiran sallar la’asar ne ya farkar da ita daga barcin da takeyi buta ta dauka domin zagawa bandaki kafin tayi alwala,,bata ko kalli kofar dakin ba ta tsallake tayi wuce,,,tana wucewa taji kamar an tsikare a mararta bata kawo komai ba a ranta ta shige bayi,,,,ta tsugunna da niyyar yin fitsari a maimakon ya fito sai jini taga yana fita kamar anbude famfo,,,cikin tashin hankali ta mike da sauri amma kuma sai taga jinin nabin cinyoyinta ga wani murdawa da mararta keyi,,dakyar ta lallaba ta fito ta koma daki duk inda tabi sai jinin ya zuba…
i
asabe na daga kofar window din dakinta tana ganin komai farin ciki ne ya kamata ganin aikin ta yaci,,,murmushin mugunta tayi tana fadin ni asabe wazai ja dani ya kwana lafiya ballantana wata karamar alhaki wai fatima kinta gani kenan keda haihuwa har abada sai dai kiga mata nayi…(nidae nace ta allah bata kiba asabe????????)

muhammadu kamar yasan abinda ke faruwa yau yaji yana son dawowa da wuri haka ya kamo a er kekensa ya taho gida,,,dakin asabe ya fara shiga,,kallon da yaga tana mai ne yasa shi kara kallonta,,ganin zai dagota ne yasa ta fara magana,,sannu da zuwa ai yanzu na dawo daga wajen kawu yace yana gaesheka,,,toh kawai yace ya fita ya nufi dakin fatima,,,asabe bata so ya dawo yanzux tasone jinin ta yayi ta zuba har azo a samu gawarta,,,,(MUGUWA????)

jinin da ya gani kofar dakin ne ya sashi karasa wa da sauri cikin dakin inda anan ne yaga tashin hankali,,,kwance take cikin jini shame shame sai numfashin ta dake fita kadan kadan,,,cikin tashin hankali ya karasa inda take tare da tallafo yanayin daya ganta ne yasa shi fashewa da kuka,,,,da yaga haka bazata mai ba sai ya sabeta a kafada yayi waje da sauri,,haka ya rinka ratsawa har ya isa da ita karamin asibitin dake garin,,,da sauri aka amshe ja aka shigar da ita ciki,,,shi kuma ya koma gefe yana zirga zirga tare da tinanin me ya jawo mata hakan shidai yasan lafiya lau ya barta kafin ya fita,,,,

sai dai aka share awa biyu a kanta da kyar likitan ya samu ya tsayar da jinin dake zuba sannan aka mata allurar barci,,,likitan na fitowa muhammadu ya taso da sauri yabi bayan shi sai da ya shiga office din likitan kafin ya fara tambayar shi halin da fatimar ke ciki,,,,bayani ya fara cikin nutsuwa,,,,gaskiya duk iya dubarwa da mukayi bamuga wata matsala ba da har yasa wannan jinin zuba ba,,,sannan kuma har yanzu cikin nanan bai fita ba sai dai zaka bari zuwa gobe sai a sallameku,,,farin cikin da muhammadu yaji a lokacin bai misaltuwa,,,gidan su fatima yaje ya fadawa mamanta abinda ke faruwa tare suka tawo asibitin sannan shi kuma ya koma gida dakko kayan da zasuyi amfani dashi,,,

sai da fatima tayi kwana2 a asibiti jiki kam alhamdulillah taji sauki sosai,,ba wanda baije gaisheta ba amma banda asabe,,,,dan tunda taji ance fatima ta samu sauki take cikin takaici da bakin ciki

haka sanda fatima ta dawo duk makota na shigowa yi mata ya jiki asabe naji tana zaune a dakin tana fama da bakin cikin da ya cika mata zuciya,,,

haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin fatima na girma amma daga ita sai muhammadu suka sae tanada ciki kowa yana tinanin cikin ya zube ciki kuwa harda asabe,,,wadda keta murna shiyyasa yanzu kota kanta bata bi
ita a tinanin ta ai tariga ta gama da ita

????????????Asabe sai dai kiji kukan baby aradu

Pls kuyi hakuri da wannan

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button