BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 29


     Ita ta tada Anam sukai salla, suna idarwa ta koma gado ta kwanta. Kyaleta Aysha tai sai da aka ƙara kiran sallar isha’i sannan ta sake tadata. Koda suka kammala babu yanda batai da itaba akan suje falo taci abinci tasha magani amma taƙi. Dole Ayshan ta barta ita ta fito. 

Fitowar tata kusan dai-dai ta fitowar Fadwa daga kitchen tare da mai-aiki. Sannu tai musu dan suna faman shirya abincine a dining, itama tayasu tayi, suna tsaka da shirya abincin ya shigo falon yana waya. Kai tsaye dining ɗin ya nufo dan yana son ya ɗanci abincin yaje ya kwanta da wuri a gajiye yake matuka. Mai-aiki tabar wajen da sauri saboda hararar da Fadwa ta zuba mata. Aysha dai kujera taja masa baya.

Zama yay idonsa akan matarsa dan sabuwar kwalliyar tata ta masa ƙyau sosai. Ta ɗan duƙo ta sumbaci gefen fuskarsa. Hannu yakai ya ɗan shafi tata fuskar ya cigaba da wayarsa. Aysha dai ta ɗauke idonta a kansu tun sanda Fadwa takai masa kiss……..✍????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button