BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 35

  Bayan sallar isha'i duk wani mai faɗa aji a gidan ya hallara a sashen Daddy ne. Dan hatta Anam da bayan farkawarta kunnenta ya jiye mata wasu maganganun da harta ɗan fahimci abinda ke faruwa da akema jidalin tana wajen. Sai dai kuka take har muryarta bata fita, dan kunnenta ya jiye mata wasu manya-manyan zagi da Gwaggo Halima ta dinga jifan iyayenta da su. Gashi kuma Mamie na kuka ita da Aunty Mimi da babban yaron Aunty Mimi ɗin da Amrah. Tsabar kukan da take har amai tayi dan ji take kamarma ta mutu itakam ta huta, sai dai taci alwashin bazata taɓa zaman aure da Shareff ba itama.....

        Yayan Mommy da suke kira da Baba Ibrahim ne ya gama ƙarema kowa kallo, ganin babu Shareff a wajen ya tambaya. Anan ne Abbah ya mike ya nufi ƙofar bedroom ɗin Daddy. Zaune yake a kan sallaya hanunsa dafe da kansa dake matuƙar sara masa kamar zai faɗi, sallarma da ƙyar ya iya tashi yayita ganin lokaci zai shige dan har magtib ya haɗa. Jin muryar Abba ta sashi miƙewa da ƙyar ya nufi ƙofar ya buɗe, Abba dake kallonsa cike da tausayawa ya ɗan riƙo kafaɗarsa.
       “Yaya dai Babana kanne ke ciwo?”.
   A hankali ya iya jinjin kan nasa da ɗago idanunsa da sukai jazur ya ɗan kalli Abban. Murmushin ƙarfin hali yay ya maida kansa ƙasa ya risinar. Sannu Abban yay masa cikin tausayawa da riƙosa suka fito, kusan kowa sai da ya zuba masa ido a falon, shi kam bai yarda ya kalla kowa ba ya zauna kusa da ƙafafun Abba.
       Baba Ibrahim ya buɗe taro da addu’a, kafin ya fara magana cikin nasiha dajan hankalinsu akan muhimmancin zuminci a musulunci da zamantakewar rayuwa. Ya ɗora da faɗin, “Wannan aure a ganina abin alfaharine a gareku dan koba komai ya dunƙuleku ne waje ɗaya a matsayinku na jini guda. Fatan alkairi da ƙarfafa gwiwa kawai ya rage kuyi ga shi Shareffuddeen da nauyin ya rataya a kansa, amma ba wannan shirmen ba, gaba ɗaya yaran nan fa a ƙarƙashin ikonku suke, bazakuyi fatan bijirewar waninsu gareku ba in har kunada hangen nesa. Amma ke Nafisa minene naki na tada jijiyar wuya yaro ya saki matarsa??”.
       Mommy dake cike fam da nasihar Yayan nata ta saki kuka, “Wlhy ni dai Yaya bana buƙatar wannan haɗin, inhar nice na haifi Shareff to ina umartarsa ya saki yarinyar nan hakan zaifi mana zaman lafiya a gidan nan bana buƙatar wannan kwamacalar. Taya yana auren ƴar wajen Halima kuma ace ya auri wannan ai an haɗa husumane dan kishi ba wasa bane, babu wani zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya da hakan zai kawo sai ma wata sabuwar musibar. Kuma wannan ai munafunci ne, inba munafunci ba miyasa zasu ɗaura auren bada sanin kowa ba….”
      “ALLAH ya rabamu da ita. Ban san hujjarki na kawo wannan misalan ba, ba kuma na buƙatar sani, sai dai zan miki adalci ɗaya, shine jin ta bakin shi Shareff da ayanzu ikon zartarwa ke hanunsa akan matarsa, dan nasan su dai su Muhammadu da yardarsu da son su sukai wannan haɗin alkairi, kuma basu ɓoye dan munafuntarku ba sai dan kawo masalaha saboda sanin halinku. Dani kuma aka ɗaura auren tun waccan ranar kafin a ɗaura na ita ɗiyar halima da kike magana, domin kuwa da safe muka ɗaura na ita Juwairiyya iya mu kaɗai batare da sanin ko shi kansa Shareffuddeen ba, kafin a ɗaura na ita wannan yarinya Fadwa bayan sallar juma’a……”
  Baki ta buɗe zatai magana ya ɗaga mata hannu, dole tai shiru dan tana bala’in shakkarsa. Kallonsa ya maida ga Shareff da kansa ke ƙasa har yanzu bai ɗago ya kalli kowa ba, sai dai komai na shiga cikin kunensa kamar kowa, yayinda jawabin na Baba Ibrahim ke shigarsa tamkar almara, taya ya kasa gane an ɗaura masa aure da Anaam? Miyasa kuma aka zaɓi ɓoye masa shima?…… “Shareffuddeen!”. Ya kirayi sunansa cike da kulawa.
      Bai ɗago ba, sai dai ya amsa da “Na’am Baba”. Cikin dasashshiyar muryarsa dake tabbatar da baida lafiya. “Nasan kanajin komai basai na ƙara maimaici ba, iyayenka sun baka mata domin ƙoƙarin ƙara ƙarfafa zuminci a tsakaninsu da ku da suka haifa, shin kai ka amince da hakan a matsayinka na ɗa a garesu ko kuwa kanada ja tamkar mahaifiyarka?”.
      Tsitt falon yayi kowa ya zubama Shareff ido musamman Fadwa, Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima………✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button