BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 35

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

35

ASSALAM ALAIKUM DEARIES … BARKAN KU DA KOKARI .. KAMAR KODA YAUSHE. WANNAN KARON MA MUNA BARAR ROKON KU WAJEN TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS DAKE MANHAJAR YOUTUBE

YARO NE DAYA TASHI DA SON KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE KUMA KWADAYIN GADON ME SUNAN SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE. A KUMA YI VIEWING DA LIKING. A TEMAKA DA SHARING MA… JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO…????

Assalamualaikum dear sisters and brothers.

Welcome to ummu sudais YouTube channel????
A channel where the Holy Quran is been recited from different Angles.
Click on this link and listen to the Beautiful recitation that will melt your heart
https://youtu.be/Lafgc749sK8

Your subscription to our channel is of Great important. Please help us grow our channel by subscribing and liking our videos fisabilillah.
Thank you so much


……….Cak numfashin Fadwa ya ɗauke daga ƙirjinta, idanunta suka fara ganin duhu-duhu, tai baya luuu zata faɗi dan wani irin mugun hajijiyace ta lulluɓe ganinta da jinta saboda maganar tazo mata ne tamkar saukar nokiliya…. Laɓɓanta matuƙar rawa suke na alamar sonyin magana, amma bushewar yawun dake taimakawa maƙoshinta ya hanata damar hakan. Sai faman raba idanu take a tsakanin Mommy dake tsaye tamkar bajimar zakanya taga abin farautarta da Shareff da alamu suka nuna shima yayi ƙamewar wucin gadi ne saboda wani dalili na mamakin furicin Mommy ɗin ko wani abu daban da bata hasaso ba…..
     Shigowar Daddy ɗakin tamkar an jehosa ta maido Shareff a tashi sumar tsaywar jinin data riskesa tabbacin hasashen Fadwa, dan shima dai jinsa da ganinsa a take suka rabu da gangar jikinsa baki ɗaya, sai idanunsa ne kawai tsaye ƙyam akan Mommy na tabbacin bashi da maraba da sumamme.
        “Bazan hanashi bin umarninki ba, sai dai nima a nawa umarnin, wlhy! Wlhy! Wlhy!! Idan har Al-Mustapha ka saki Mamana! Nima zan saki uwarka dai dai da adadin sakin da ta sakaka ka rubuta!!…….”
    “Dana haɗa jini da Usman da Ai’sha gara na barka har abadan abidina Muhammad!!”. Mommy ta tari numfashin Daddy a tsawace.
“Okay fine! Haka kikace ko?. Kai Al-Musta……….” Shigowar Abba da Dr Jamal ta hana Daddy ƙarasa faɗar abinda ke bakinsa, sai dai wani irin mugun kallo da yake bin Mommy da shi, har cikin ranta yake ratsata, sai dai zuciyarta tayi bushewar da take jin zata iya ɗaukar koma minene daga garesa akan wannan auren da rabashi shine kawai samun nutsuwar ruhi a gareta. Gwaggo ta riƙo hanunta tana faɗin, “Altine kina lafiya kuwa? Kai Muhammadu karka sake cewa komai kumuje gida”.
       Mommy ta fusge hanunta daga riƙon da Gwaggo taimata. “Wlhy Gwaggo babu inda zanje sai Al-Mustapha ya saki yarinyar nan, dan bana buƙatar auren nan ya sake minti guda a kansa!!”.
        Dr Jamal da gaba ɗaya ya rikice cikin roƙo yace, “Dan ALLAH Mommy kiyi haƙuri, bara na basa sallamar sai aje gida wannan maganar bata nan bace ba”. Kafin tace wani abu Gwaggo taja hanunta suka fice, ganin shima Daddy ya fita ya sata yarda ta bita. Abbah ya kama Shareff shi da Doctor Jamal. Wata Nurse kuma ta kama Fadwa da har yanzu babu alamar ta dawo hayyacinta…….

         Sun sami gida ya gama hargitsewa shima. Dan Gwaggo Halima da komai yaje kunnenta gaba ɗaya ta haukace, sai zagin Abie take da tone-tone, dan waje ta fito tana faɗar maganganu marasa daɗi, Abie ya miƙe ya shige cikin gidansa, amma sai ta bisa har can. Jin zagi da tonan asirin yayi yawa Aunty Mimi ta kasa haƙuri duk da kowa ya santa mutumce mara faɗa da son hayaniya. Amma zagin mahaifiyarsu da Gwaggo Halima keyi bazata iya jurewa ba ta fara tayata. Cikin ƙanƙanin lokaci hayaniya mai tsanani ta tashi dan dangin Mommy irinsu Samira tuni sun shigo gidan suna taya Gwaggo Halima.
     Ran Daddy ya ƙara ɓaci, yayinda hankalin Abbah dana Shareff sukai matuƙar tashi su kuma. Da ƙyar Gwaggo ta hana Mommy shiga gidan, yayinda Dr Jamal ya taimakawa Shareff zuwa ciki, wasu mata kuma suka kama Fadwa da zuwa yanzun ta fara kuka sai dai babu uhhm babu uhhm-uhhm.
      Daddy kam daya faɗa gidan Abie lafiyayyun maruka guda biyu ya sauke akan fuskar Gwaggo Halima. Tamkar ƙiftawar idanu gidan yay tsittt, ya kuma sauke mata wasu biyun da suka saka zukatan mafi yawan mutane girgiza. Gwaggo Halima maiji da kanta, Gwaggo Halima babbar mace hamshaƙiya mai taƙama da tunƙaho da sunan mijinta da muƙaminsa koda a tsakkiyar cikin dangine, yau itace ake saukema waɗan nan marukan, dole ne gida yay tsit. Daddy ya ɗaga hannu zai sauke mata na huɗu Abie ya riƙe masa hannu. Cikin tsananin damuwa yake girgiza masa kai alamar roƙo. Ɗagowa Gwaggo Halima tai tare da ware hannu zata mari Abie taji an riƙe mata hannu tare da murɗesa. Abbah ne da wannan aikin, ransa a matuƙar ɓace tamkar bashi ba…..
“Ko’a mafarki kikai tunanin wannan kuskuren sai mun tabbatar da nadama a rayuwarki Halima!!”. Kalaman Abbah dake amsa sunan ƙani a gareta sukai matuƙar ratsa kunnuwanta dama duk wanda ke a wajen.
      Sosai fa gida ya ƙara harmutsewa da ruɗewa. Har hayaniyar ta saka Anaam dake barcin wahala farkawa. Tun farko ma Mamie ce da hankalinta ya tashi ta rurrufe windows yanda bazai kawo kunnen Anam ɗin ba, sai dai ƙurar data sake tashi a yanzu tafi ƙarfin ta farko. Da ƙyar aka fidda Gwaggo Halima dake cigaba da ɗurama Abie da Mamie da Aunty Mimi harma da su Daddy zagi daga gidan. Sai dai can cikin gidan ma Mommy ce ke borin sai Shareff ya saki Anam. Shiko ya shige bedroom ɗin Daddy ya kulle kansa sai faman dukan ƙofa take da tabbatar masa zata tsine masa.
       Yana jinta, sai dai baya gane mi take faɗa saboda hajijiyar dake juyawa da kansa. Yana zaune bakin gado hanunsa dafe da kansa hawaye na zirara akan fuskarsa. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin makamancin irin wannan tashin hankaliba. Daddy da gaba ɗaya idanunsa sun rine da ɓacin rai ya fisgo Mommy dake faman jijjiga ƙofarsa tana jaddama Shareff ya buɗe kota tsine masa. Babu zato ko tsammani ya sakar mata nata lafiyayyun marin itama da iyakar ƙarfinsa. Dan tsabar azaba da firgita sai da ta faɗa kan kujerar dake daura da ita hannunta duk biyu dafe da wajen da ya maretan.
      “Muhammad ni ka mara?!!”.
“Idan kika ƙara cewa tak ma, zan iya miki dukan mutuwa ba mari kawai ba!!”.
Kalamansa sunyi matuƙar razana duk wanda ke’a falon. Sai dai shi a garesa babu ko gezau ya sake tabbatar mata ta hanyar faɗin “Idan kuma kinji ƙarya bismillah gwada na tabbatar miki!!”.
     Bakin kuwa tai shirin buɗewa zatai maganar dan zuciyarta ta rigada ta bushe Gwaggo tai saurin toshe mata shi, dan ita kam taga tsantsar wutar bala’in dake ci a cikin idanun Daddy irin wadda bata taɓa ganiba a rayuwarta. Duk yanda Mommy taso Gwaggo ta sakar mata baki taƙi, nanfa suka hau kokawa, sai dai ALLAH ya taƙaita abun a dalilin shigowar yayun Mommy maza da Abbah yay kiransu a waya harda wanda ta kira ɗazun taji komai a bakinsa da ƙanin mahaifin Fadwa.
      A tsakar gida dai ƴan biki masu gudun tashin hankali tuni sun fara zare jikinsu suna guduwa dama Magrib tayi, wanda kuwa zasu kwana anan da ƴan son ganin yaya za’a ƙare na zaune jugum-jugum, ƴan bani na iya kuma nata ƙus-ƙus. Fitowar su Daddy zasu wuce massallaci ya saka gidan ɗaukar tsit dan ko’ina akwai hasken wutar nefa, sai dai wasu basu daina magana ƙasa-ƙasa ba sosai musamman waɗanda ke’a ɗan nesa da su…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button