BABU SO 41
Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO????????AREWABOOKS
41
……….Gaba ɗaya tsiwar dake bakin nata ta maƙale akan harshenta, ta juya baya da sauri tana rumtse idanu ƙirjinta na bugawa da karfi. Duk abinda takeyi yana kallonta ta cikin mirror, cigaba yay da goge sumarsa kamar bai ganta ɗin ba, keys ɗin dake ajiye saman mirrorn ya ɗauka ya miƙa mata. “Je ɗakina ki samomin kaya….”
Kafinma ya rufe baki tai gaba har tana neman yin tuntuɓe. “Da haƙwaranki zaki buɗe ƙofar?”. Ya faɗa cikin katse mata hanzari. Jitai kamar ta fasa ihu, amma sai ta daure idanu a rufe ta juyo tare da miƙa masa hannunta. Kansa ya ɗan girgiza ya ajiye keys ɗin ya cigaba da abinda yake yi. Kaɗan ta buɗe idanunta, tana tura baki gaba ta ɗauka batare data yarda ta kalli inda yake ba ta fice da hanzari. Haka kawai abin nata ya bashi dariya, amma sai ya haɗiye baiyi ba.
Baki ta shiga taɓewa tana bin ko’ina na sashen da kallo. Babu dai tarkace babu kuma mugun datti, amma yana buƙatar gyara dan da alama shi yake aikin gyara da kansa tunda taji ance Fadwa na gida sai jiya aka dawo da ita. Bakinta dai bai furta komai ba ta buɗe wadrobe nashi. Anan kam komai a tsare yake, ga kuma ƙamshi kayan nayi. Taja wasu mintuna tana bin kayan da kallo daki-daki kafin dai ta zaɓi wanda suka kwanta mata a rai, cikin ɗan taɓe baki take faɗin, “Ko basu makaba dole ka saka, ko kunyar zama da towel a gabana baiji ba tirr” sai kuma ta taɓe baki, “Mutumin nan fa Sassaƙeƙen ƙato ne fa yasin” tai ƴar dariya da kai hannu ta buge bakinta.
Tafiyarta take hankali kwance batare data lura da su ba, daga aunty Malika har aunty Safarah, Fadwa aunty Suwaiba sun saki baki suna binta da kallo harta wucesu, baya Fadwa tai kamar wadda jiri ke neman kwasa ALLAH ya sota akwai bango bayanta “Aunty kenan wajenta ya kwana fa?”. Ta faɗa hawaye na rigegen sakkowa. Su duka kallonta sukai, a ɗan hasale aunty Malika ke faɗin, “To ke kam dai lallai takaicin kishiya zai karki idan baki nutsu ba, kuma in har kika bari ta gano lagonki wlhy kin mutu. Mi kwanan nasa wajenta ya amfana masa tunda gata nan tsaye kan ƙafafunta babu alamar tanada daraja na mace a wajensa. Ashema kina kokwanto akan maganin nan?”.
“Aunty ki fa……”
Cikin katseta Aunty Safarah tace, “K washe garin da aka kawoki gidan nan a haka kika kasance?”. Wata wawiyar ajiyar zuciya Fadwa ta sauke mai ƙarfi saboda tuno wahalar data sha a hanunsa a daren da aka kawota, washe gari kam komai bata iya hasalama kanta ba sai da taimakonsa, dan ko tafiya sai da taita cin azaba kafin ta dai-daita bayan kwanaki biyu, ta share hawayenta tana murmushi, tabbas ta yarda mijinta bai taɓa yarinyar nan ba, dan babu macen da zataje hanun mijinta a karon farko a ganta a haka, shi ɗin namiji ne, idan tace namiji, tana nufin namijin gaske… (????dama akwai mazan ƙarya? Ƴar uwa kisa a ranki kema mijinki namijin gaske ne????????).
Anam da batasan sunai ba koda ta isa sashen nata bayan tayi sallama a ƙofar ɗakin cogewa tai taƙi shiga, sai ƙofar data buɗe ɗan kaɗan ta zira hanunta da kayan a kai. Yana zaune a bakin gadonta yana waya ya hango hanunta, ɗauke kansa yay kamar bai gani ba ya cigaba da wayarsa. Jitai hanunta yana neman sandarewa, ta harari ƙofar tamkar tana ganinsa, cikin tunzura baki ta shiga ɗakin, da baya-baya ta dinga tafiya a hankali harta iso gaban mirror, ido suka haɗa da shi ta ciki daga inda yake zaune dan ya gama wayar, da sauri ta kauda kanta ta ajiye kayan a kujerar mirror ɗin tai gaba. “singlet da boxer kuma fa?”.
“Yayaaaa!”
Ta faɗa da sauri dajan sunan cikin salon kai bakajin kunya tana juyowa. Suna haɗa ido tai saurin sake juya baya “Ni dai babu ruwana”. Jin motsin tashinsa tsaye ta fice da sauri. Sai da ta gama yima ƙofar harara kala-kala sai kace wata ƴar yarinya sannan ta wuce ɗakko masa. Shima daga can ƙaramin tsaki yaja da faɗin, “Girma ba wayo”.
Yanzu kam bata kai ɗazu daɗewa ba ta dawo, cikin dakiya da ɗaure fuska ta shigo ɗakin kanta tsaye, har gabansa taje ta ajiye ta juya ta fita batare data yarda ta kallesa ba. Da kallo kawai ya bita a ransa yana raya (anya yarinyar nan bata da aljanu ma kuwa?) rashin mai basa amsa ya sashi sake jan wani tsakin ya ɗauka kayan ya saka. Tana zaune a falon ta wani tsume kamar sarauniya a kujerar mulki ya fito, da farko tayi kamar bata gansa ba, sai da ya ƙara matsowa sosai taji ƙamshin turarenta a jikinsa. “Yaya satar turare ka koma kuma?”. Ta faɗa tana tsatstsaresa da idanu. Shi rasama mizaice mata yayi, zata ƙara magana akai knocking. Ɗauke idonsa yay daga kallonta ya nufi ƙofar ya buɗe. Cikin girmamawa Mubarak ya risina ya gaidashi. Kai ya jinjina masa yana amsawa.
“Yaya dama breakfast ne akace a kawo”.
“Okay ya mutanen gidan?”.
“Kowa lafiya yake”.
Komai bai sake cewa ba ya matsama Mubarak ɗin ya shiga, shi kuma ya nufi sashen Fadwa. Taso sharesa amma kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewar sa namijin tsayayye da bazai ɗauka raini ba ya sata nutsuwa, idanunta a ƙasa tace masa ina kwana. Falon yake ɗan bi da kallo batare daya amsa mata ba, sake gaisheshin tayi a ɗarare, sai dai bai amsa ba yanzun ma, saima tambaya daya jeho mata…
“Masu zugakin sun tafi kenan?”.
Saurin ɗagowa tai ta kallesa, ganin ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifi ga fuskarsa a tsume matuƙa ya sata saurin maida idanun nata ƙasa sai dai ta kasa cewa komai. Ya furzar da numfashi mai zafi da zurfi. “Daga yau na haramta musu zuwamin gida, idan kuma sukai kuskuren sake zuwa ɗin zan ɗauka kowane irin mataki a kansu. Kema bazance karki ɗauka huɗubarsu ba, amma ki sani idan naci karo da wani hali a gareki saɓanin wanda na sanki da shi kamar jiya zakisha mamaki na”.
“Humm” kawai tace a ƙasan maƙoshi, dan ta ɗauka zantukan nasa da suna borin kunya irin mazan da sukaci amanar matansu wajen ƙara aure. Sai dai kamar yanda su aunty Malika sukai mata huɗuba bazatace da shi komai ba, zatabi komai a sannu harta cimma nasara akansa daga shi har amaryar tasa. Humm ɗin tata ta matuƙar zafarsa da ɗaukarta raini, sai dai a yanzu baya buƙatar wani tashin hankali dan haka baice komaiba yay ficewarsa. Sashensa ya nufa, ya ɗauka key ɗin mota da lap-top bag ɗinsa ya sake komawa sashen Anaam, har yanzu Mubarak na nan bai wuce ba, yana tsaye daga bakin ƙofa yace, “Ni na wuce office”.
Ɗagowa tai ta ɗan dubesa, ganin fuskarsa babu alamar wasa ya sata shanye abinda ke bakinta, a taƙaice tace, “ALLAH ya bada sa’a”. A kan laɓɓa ya amsa mata ya juya ya fita. Miƙewa Mubarak yay shima, “Aunty Anam bara naje nima akwai aiken aunty a wajena kar taita jira”. Fuska ta ɓata cikin damuwa, sai dai batace masa komai ba ta gyaɗa kanta kawai. Tanaji tana gani ya fita ya barta ita ɗaya. Sai taji gaba ɗaya sashen ya mata girma da faɗi na rashin sabo, haka kawai kukan da taketa fatan kartayi ya kufce mata, sai da tayi mai isarta sannan tai zaman cin abincin da Mubarak ya kawo, tana kammalawa barci ya kwasheta a falon batare data shirya hakan ban.
Cikin barci sautin mahaukacin kiɗa dake tashi a gidan ya karaɗe mata kunne, ta tashi a ɗan zabure tana dafe kanta daya sara mata, a dai-dai nan su Amrah suka shigo falon. Su duka kanta sukai suka rungumeta, cikin dauriya da jin daɗin ganinsu ta janye hanunta tana kallonsu fuskarta da murmushi. Aysha tace, “Uhhm su Blood matar Yaya Shareff, wlhy har kin canja dare ɗaya”.
Kai kawai Anam ta girgiza tana hararta, Amrah ta kwashe da dariya ita da Husnah. Cikin salon ƙara tsokana Aysha tace, “ALLAH karkiji wasa blood, sai sheƙi kikeyi kamar hasken farin wata, ba kamar matar Yaya Maheer ba da muka tarar wujiga-wujiga da ita tana faman kuka”.
Kafin Anam da zancen ya tsikara tace wani abu Husnah ta karɓe da faɗin, “ALLAH nima taban tausayi, kamar ma wadda bata cikin hayyacinta, daga ganinta zamuyi sa’anni da ita amma kamar bata da wayo sosai wlhy, ko ƴar 18years bazatai wannan sakaka ɗin nata ba ai balle ita”.
Amrah da batace komaiba ta ɗan girgiza kanta, “Ni kam sai naga ba laifinta bane wlhy, kamar matsalar daga Yaya Maheer ne, kugafa yanda yaketa mazurai kamar ba shi ba. Anya kuwa auren soyayya sukayi sisters?”.
Tsitt sukai lokaci guda kowa na nazarin maganar Amrahn, Anam ta fara furzar da numfashi tana faɗin, “Inaga kubar zancen nan haka dan ALLAH kamar zaifi. Wai shi wannan kiɗan daga ina yake fitowa?”. Aysha ce ta taɓe baki da jan tsoki, “Daga ina kuwa inba sashen aunty Fadwa ba, shaggun ƙawayen nan natane su Sima fa kamar a gidan. Halan Yaya baya nan ne ko?”.
Kai kawai Anam ɗin ta jinjina batare da tace komai ba, ta kuma daƙile maganar duk da ta fahimci tana cin bakunansu. Basket ɗin da suka kawo ta jawo gabanta tana buɗe kulolin ciki, da haka ta ɗauke hankalinsu da zancen abincin babu wanda ya ƙara sakko maganar kidɗan dana gidan Maheer.