AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 53-54

??53and54??

Kaya afham yashiga hadawa, saida yacika akwatinsa kaf, sannan ya tsaya yana tunanin idan yafita ina zai dosa, ina zaije,
Kofar dakinsa yaji anturo, yakurawa kofar ido yana jiran yaga wazai shigo,
Aneesah ce tayi tsaye tana kallon yana yinsa, akwatin data gani a gefensa ta kurawa ido cike mamaki tace “yaya afham mekake shirin aikatawa ne, naga kahada kaya”

Afham yakauda kai daga kallon datake masa yaci gaba da rufe zip din akwatinsa, saida ya kammala rufewa yadaga kai yasake kallon aneesah “gidan nan zan bari, kuma idan natafi kigayawa su abba karsu nemeni, domin nabar gidan nan har abada, domin nayi shawara da zuciyata barin gidan nan shine kadai katangata agareni akan auren amal “

Mamaki yacika aneesah sosai, tarike kugu tana kallon afham “hmm yaya afham zuciyarka bata baka shawarar kwaraiba, domin tanema maka saukankiyar hanya wadda zata saka mahalincinka (Allah) Fushi dakai, domin yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye, yaya afham kayi gaggawar chanza wannan gurguwar shawarar taka, mezaka cewa Allah yanzu idan katafi kaddara takiraka kasamu matsala atafiyarka, zakacene kayi fushi da iyayenka shine kabar musu gida, mafi aka sarin irin wannan tafiyar bata zama alkhairi, yaya afham karkaje, kazauna cikin ahalinka shine mafi alkhairi agareka “

edon afham yayi jajir cike da masifa yace “yakikeson nayi kenan natsaya a auramun wacca bana so, nifa kwata2 bana son amal, wlh matukar ba’a rabani da amal ba to wallahi zanbar gidan nan”

Aneesah tayi ajiyar zuciyar, tana mamakin irin zuciyar afham shi baya daukar nasiha, a duk lokacin da kake masa nasiha shi a lokacin yake kara zafi,

Aneesah tasaukar da murya tace ” Bana son katafi, kazauna ni zanyi abba da momy magana, zan fahimtar dasu cewa bakason amal, kuma insha Allah zasu saurareni, kabani nan da kwana biyar”

Afham yaja numfashi sannan ya ajiye akwatin akan gado yace “kwanar biyar kikace, nabaki, amma kisani cewa matukar ya wuce kwana biyar to tabbas zanbar gidan nan” yana karasa maganar yanufi hanyar bandaki,

Aneesah tana murmushi, takarasa kusa ga akwatin, tadauketa takaita cikin drowar tasaka, koda tajuyo yashige bandaki,

Kida kai tayi tana murmushi tabar dakin…
*** ***
Bayan hilal yabar daki ameelah cike da zafin zuciya, airtel office yakoma, koda yaje sunkarasa komai, an rubuta duk wani detail akan number, yakarba yafara karantawa, mai number bama gari daya sukeba, nisa yake dasu sosai,

Hilal yaja tsaki jiyakeyi kamar ya yaga pepar, miyakai ameelah waya da maza, meya rageta dashi meye baya mata, duk zuciyarsa yake yiwa wannan tambayoyin, saidai kuma ba amsa, 

Cen kuma wata zuciya tafara kawo masa wasu wasi,
Ayya kuwa ameelah zata iya masa haka, tunawa yayi da irin soyayyar da sukayi abaya kafin aure,…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button