TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAAKA 4

 

*_Typing????_*          *_????TAKUN SAAƘA!!????_*

                *_Bilyn Abdull ce????????_*

_ZAFAFA BIYAR 2K22_

_________________________

*_Chapter Four_*

………..Suna baro cikin asibitin Muhibbat ta kashe wayarta dan ma kar Yah Ammar ya sameta. 

        Tun farkon shigowa anguwar tace a saukesu. Amma sai Zahidah tace sam basu yarda ba a kaisu har ƙofar gida. Zata fara masifa Hafsat ta ce, “Kiyi haƙuri ya kaimu saboda bazan iya taka ƙafarnan ba Hibbah”. 

       Shiru tayi bata sake tankawa ba har suka iso ƙofar gidan su Hafsat daya kasance a farko, sai nasu Zahidah, Muhibbat ce ƙarshe. Saboda ciwon dake tare da Hafsat ɗin ya sakasu cewa a tsaya ƙofar gidansu. Zahidah ta bama mai taxi kuɗinsa tana godiya. Amma sai yaƙi amsa. Mamaki ƙarara a fuskar Zahidah da Hafsat. Sun buɗe baki zasu magana yay musu alamar suyi shiru.

       “Basai kunce komai ba, inhar da wannan mai bakin tsiwar tare da ku anta kaiku waje ƙyauta kenan babu ko sisin ku”. Yay maganar idanunsa akan Muhibbat yana wani sassanyan murmushi.

          Hararar da yay tsammani ta watsa masa, cikin takaici tabar wajen batare da tace komai ba. Kira Zahidah da Hafsat suka shiga ƙwala mata suna dariya, amma ko waiwayensu batai ba harta ƙarasa gaban wani gida mai baƙin gate. Sai da ta kama murfin zata shiga ta waigo, ganin har yanzu mai taxi ɗin na tare da su yasata jan tsaki akan laɓɓanta ta ce, “Maye kawai”. Daga haka ta shige ciki.

         Gida ne da zamu iya kiransa babba a girma da ginuwa. Dan a ƙalla akwai ɓangarori biyu zuwa uku a cikinsa. Ɓangarori biyu na farkon shiga gidan sunfi haɗuwa da tsaruwa, zakaga hakan tun daga wajema kafin ka kai ga shiga ciki, sai dai kuma ɗayan dake daga ciki ya fisu girma, amma bai kai su ƙyawu ba.   

      Harara ta zubama sashen guda biyu tana taɓe baki, tana gab da wucesu taja tsaki a zuciyarta wanda batai zaton ya fito har waje ba.

     “K!! Dan ubanki wa kikema tsoki!!”. 

Wata buɗaɗɗiyar murya mai cike da hargowa ta faɗa. Cak ta tsaya ƙirjinta na bugawar tsoro, tabbas da ace tasan mugun nan ya dawo gidan da bazata shigo ba sai magriba. Jin takun tafiya a bayanta alamar ya taso ya sakata juyowa. Ƙiris ya rage ya iso gareta, babu shiri ta kwasa da gudu zuwa sashen can ciki tana ƙwala kiran sunan Ummi!.

       “Ya ilahi! Tanee lafiyarki kuwa? Wai sai yaushe ne hankali zai game jikinki kisan girma ya fara zuwa miki!”. 

      Ummi dake ƙoƙarin fitowa a kitchen riƙe da ludayin miya a hannu ta faɗa. Dai-dai isowar Hibbah cikin falon itama a guje. Bayan Ummi taje ta maƙale.

      “K da wa kuma?”.

Ummi ta faɗa tana juyowa gareta fuska a ɗaure.

      “Wannan mugunne fa Junaid Ummi. daga na shigo ina tsaki ya hau zagina kamar nasan da zamansa ma a gidan”.

          Baki Ummi ta buge mata, tai saurin ja da baya daga jikinta tana dafewa. 

        “Wannan bakin naki da kanwa bata jiƙa a cikinsa shi zaisa kiyita shan wahala a wajen mutanen gidan nan Tanee. Mara kunyar banza matsamin a hanya”.

       Gefe Hibbah ta matsa gudun kar Ummi ta sake kai mata wani dukan hawaye cike da idanunta. Sai da taga ta koma kitchen ɗin sannan ta nufi ɗakinta zuciyarta na ƙara jin tsanar mutanen gidan nasu. Da ace zata samu wata dama a hannunta koda ta yini guda ce sai ta bisu da bulala hansin-hansin, musamman ma Hajiya Mama da Abba da wannan azzalumin Junaid ɗin. Mukulli ta murza a ƙofar tata dan batason sake magana da kowa.  

         Tunda Ummi ta jiyo ƙarar rufe ƙofar Hibbah sai tai murmushi, tasan hakan na nufin tayi fushi, ba kuma zata buɗe ba sai Yah Abubakar yazo ya lallasheta ko jarabar danna Computer ɗin tata ta motsa. Watsar da ita tai ta cigaba da aikinta saboda bataso magriba ta sameta. Cikin ranta tana tunanin yaushe Junaid ɗin ya dawo ƙasar? Dan bataji alamun murna da ga yaran gidan ba sam. Rashin mai amsa mata zancen ya sata watsarwa ta cigaba da aikin gabanta.

      Harta kammala ta shige babu wanda ya shigo a cikin samarin ƴaƴan nata, fatan dawowa lafiya tai musu sannan ta shiga wanka.

       A ɓangaren Hibbah ma wankan tayi, kasancewar tana fashin salla tana kammala kintsawa ta fito, dan ta tabbatar Ummi ta shige. bakuma zata sake leƙo falon ba sai bayan sallar isha’i. Yayunta kuwa bata tsammanin yau zasu kwana a gidan ma. Musamman Yah Abubakar da Yah Usman da yace yana katsina.

          Study table ɗinta ta haye dake can gefen falon a wani ɗan lungun. An shirya mata wajen tsaf da kayan karatu na musamman saboda kasancewarta ƴar gata, sannan haziƙa wajen sanin sirrin sarrafa Computer.   

      Tun ana ɗaukar lamarin nata shashanci har takai yanzu Yayansu Abubakar naci da ga tagomashin ƙwazon nata ta hanyar aikinsa na tsaro. Dan yasha sakata ayyuka masu muhimmancin gaske ana kuma samun nasara tunma bata kai haka shekaru ba. Wannan dalilin ne ya sakashi tsaya mata wajen ganin ta cika burinta akan zurfin nazari game da na’ura mai ƙwaƙwalwa.

         Cike da ƙwarewa ta kunna Computer ɗinta saboda aikin data tarkatarma kanta na bibiyar masu power bike. Dan ta ɗauka alwashin kosu ɗin ƴaƴan uban waye sai ta gano su insha ALLAH.

         Babu wanda ya shigo gidan sai Ummi data fito bayan sallar isha’i tace ta tashi taje taci abinci tunda babu wanda ya dawo a yayun nata har yanzu. Da to ta amsawa Ummin, tana gani ta koma ciki ta cigaba da aikinta cike da zaƙuwa.

      Ummi dake jiyo motsin Hibbah ta shiga ƙwala mata kira ganin dare ya farayi. ta tabbatar kuma inba da gaske tayi mata ba, zata iya kaiwa biyun dare akan Computer ɗin batare da gajiyawa ba.

        *_Tanee! Tanee!!_* wai bazaki tashi a gaban Computer ɗin nan kije ki kwanta ba sai na ci ƙaniyarki ko?!”.

       Hibbah dake zaune a cikin falon daga can gefen study table ta ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka. A kallo ɗaya zaka fahimci tarin ƙuruciyar dake tattare da ita, dan kwata-kwata bazata gaza shekaru goma sha tara a duniya ba. Jin tahowar mutum ta bayanta ta miƙe da sauri a gaban Computer ɗin tana faɗin, “Wayyo Ummi nafa kusan gamawa wlhy”.

      “Ai ba Ummi ɗin bace, mai kunnen ƙashi nine”..   Ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tsananin kama da ita da bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba ya faɗa a bayanta tare da kai mata ranƙwashi bisa kai. Tsalle tai zuwa gefe tana fasa ƙara duk da kuwa bai sameta ba. Ya balla mata harara yana kai hannu kan mouse ɗin Computer ɗin ya kasheta baki ɗaya. Dai-dai lokacin da yake ɗagowa ya nuna mata hanyar ƙofar ɗakinta yana faɗin, “kama gabanki kafin jikinki yay tsami anan”.

        Idanunta dake tara ruwan hawaye ta shiga ƙyaƙyƙyaftawa. Cikin narkewar fuska tace, “Yah Umar dan ALLAH ka barni wlhy zuwa 12 zan shige na kwanta. ALLAH akwai abinda nakeyi mai muhimmanci a ciki”.

            Charger ɗinta dake jikin socket ya fizga da nufin kai mata duka. Da sauri ta dirga wani uban tsalle da ihu tare da kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin nata.

        “Wai wane irin salon iskanci ne haka za’a dinga damun mutane da ihu kamar ƴaƴan rashin ƙwaɓa!”.

    Wata murya mai kauri da amo ta faɗa daga bayansu. Basai an sanar musu wanene ba, dan haka Tanee dake gab da shiga ɗakinta ta ida afkawa da sauri tana rufo ƙofar.  Umar yaɗan rumtse idanunsa yana cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi alamar son saisaita kansa dan jin zafin furucin mutumin da aƙalla zai iya kai shekaru Hamsin da huɗu zuwa da biyar

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button