BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Uban gidana ai tun tafiyarka zazzabi yarufeni nake kwance anan
OK sannu
To ina yarinyar dana ajiye an an

Kai aini nama manta da ita .Donni tunda ka tafi ban waiwayi wajanba ina fama da kaina

Ok bani kye din dakin birin .
To yamike jiki na bari ya mikomai .
Kamar me ciwon gaske

Da shigarshi gun yaganta kwance kasan bishiya tana ta bacci .gamai hankali yana kallonta yasan baccin kwanciyar hankali take .don taci ta koshi .batada wata damuwa a lokacin

Amma shi mamaki yake yanda yaganta a waje shida ya sata a dakin biri
Kafa yasa ya mangareta .da karfi

Aikuwa da sauri ta mike tana mutsika ido.

Ubanwa ya baki ikon fitowa daga dakin .monkey dinnan dana saki

Karkar jikinta yadau rawa
Wlh Yaya xan fada maka gaskiya

Kaga can wajan naga kofa wayan ta tattare .shine na fito taciki.

Sabida kin rainani ne yasaki fitowa ko

A a yaya wlh tsoro ne nakeji kayi hakuri
Dalla rufemin bakinki kamar na tsutsa .

Wuce muje banxa barauniyar abinci wlh nakara ajiye Abu kika je ko kusa dashi ne saina ballaki gida biyu
Kinji ko a a

Naji yaya wlh naji bazan karaba

Hannu yakai ya bige mata baki.

Danne bakin tayi da hannayenta .

Suna shiga parlour tashige dakinta da gudu.

Kai tsaye tai toilet. Don. Uban fitsarin dake cinta

Dik da kasancewar Baby Yarinya karama . tanada san sallah .

   Abinda zai baka  tausayi da rayuwarta .  inka shiga dakinta. Ita kadaifa take  kwana acikinsa  it's takewa kanta tsarkin kashi tayiwa kanta wanka . 

Wankanma ba da sabulu ba kawai ruwa take watsawa tunda wa ya kula da rayuwarta balle yasan bathroom dinta ba sabulun wanka

Rabon da kanta yaga ruwa da sunan an wankeshi tun randa iya Abu zata tafi .ta wanke matashi .don yawanci baa fiyemata kitsoba kasancewar .kanta me santsine don haka yanzu dikya . tattare ya cure gu daya

Abinka da yarinta .komai na dakinta inka shiga a hargitse yake . kamar ba wannan dakin da aka aka Tarawa dukiyaba lokacin da zasu dawo cikinsa ita da iya Abu ba
.uwa uba haka kowa zai haye sama ita kadai dakinta na kasa
Dikda kowa 2 bedroom gareshi agidan akwai a sama akwai a kasa

Dik irin tarin uban Kayan datake dashi bazaka siyeta naira dariba don kuwa ba sawa takeba . wardrobe dinta me hudu cike take da Kaya amma kasancewar tsayinta baya kaiwa ta dauko Kayan yasa .iya na steps din farko kawai ta zubo dash kan gado .intasa wannan saita canja .kuma dika Kayan guda biyar ta zubo dogayan rugu a uku Riga da wando biyu
Sune intaga me wanki yazo tadiba takaimai ya wanke mata .insu bushe.ta kwaso abinta
Amma kodewa agunsu baq magana

Yarinyar da bata wuce asata a gado ta kwanta jikin mamanta ba

Kai rashin uwa baiyiba wlh musamman inba Wanda zai dauki nauyi hidimominka

????????????????????????
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????

BABY KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

GODIYA NAKE MASOYA LITTAFIN BABY KHAUSAR DIK INAJIN SAKONNINKU .
ALLAH YABAR KAUNA

         2⃣5⃣

Zuwa yanzu takai ko a school bata wani kokari don inma ana musu lesson. Bata wani maida hankali .

A tinani irin na yaro baya zurfi .iya abinda yazo kwakwalwarshi shiyake tunani kawai
Don haka baby tasa aranta kawai momy .da Dad da ya Bilal basa sonta .don haka itama bata .sonsu ta daina kulasu yanzu frnd dinta Aysha M shareef ce kadai take .sonta itama yanzu bata son kowa sai Aysha

Don haka yanzu taja jiki .ko nacin magana datakewa Bilal ta daina .inma suka hadu ko a gida ko a skl saitai kasa da kanta bata ko kallansa .wai ita a tunaninta .hakan zaisa ya gane bata sonshin.
Shikuwa intai hakanma dadi yakeji .yana ganin kara tsoronshi takeji.

Shikuwa Dad ma baya kasar gaba daya .tunda yai tafiya tsawon wata uku .yau bai dawoba .yanacan harkar kasuwancinsa

Yau wani teacher dinsu yashigo yana musu lesson. Kasancewar karancin shekarunsu yasa dole .sai da wasa zasu dauki abinda yakeson .koya musu .don haka
Dayashigo .saiya fara tafawa da yan maza .da yazo kan mata .Akwai wata hanan a ajin bata son karatu .
Don haka yashiga tafawa ma da matan yana tsokanarsu .yana zuwa kan hanan saiya harareta .ya kauda kansa .
Tanata mikomai hannu ya wuceta .saita sa kuka .tace sir.baka sona ka tafa da kowa ni bandani .baka sona
Matsowa kusa da ita yai yace hanan kinsan me yasa bana sonki?
Ta girgiza kai alamar a a .

Yace sabida bakya son karatu .wasa yamiki yawa .don haka indai .biki daina wasa lokacin lesson ba .kullum nazo saina harareki .na mirguda miki baki
Yafada yana mirguda bakinsa

Dik abinda yake baby na kallansa

Saida aka tashi .sunje gida .kawai tazo fita a mota shima Bilal ya bude gaba zai fito .ta bugamai harara da murguda baki waifa ita yagane bata sonshi yanzu

Ai kuwa caraf akan idonsa

Wata wawiyar danka yakaimata ya makata da jikin motar yana fadin ni zaki harara don uwarki shegiya yar gidan hadiza me aiki .shegiya dangin .Fulani yan gudun hijira .ya karashe yana kaimata naushi abaki

Ya daga kafa zai boll da ita yaji an janyeshi gefe

Da zafin nama ya juyo yaga cikin maaikatan waye da wannan danyan aikin

Ai kuwa idonsa caraf akan Mlm khalili .
Cak yatsaya yana kallonsa don da farko ma bai ganeshiba
Saida ga baya tunaninshi yakai .ai Mlm Khalil ne

Ba yabo ba fallasa ya gaisheshi .ya juya zuwa hanyar ckn gida

Shikuwa Mlm cikin tausayi ya daga khausar yana rarrashinta

Yanzu yakara tabbatar da labarin da masu gadi suka gama bashi na sauyawar gidan .da halin ko inkula da Dad yakeyi ga Baby.

Jijjiga kai yashigayi .yana wani tunani aransa .
Haba shi dama tuntuni ya fuskanci da matsala sosai
Na yanda shima Alh. ya watsardashi tsawon wannan lokaci tun kafin yatafi garunsu gashi har saida yai shekara guda cif ya dawo

Don haka yatako yazo gidan yaga ko Alh lfy
Amma daga zuwanshi

Maaikatan gidan maza suka shiga bashi labarin .yanda rayuwar baby ta koma a gidan

???????????? Takuce Layuza kabir Adam ????
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

        NA 

LAYUZA KABIR ADAM

Da sunan Allah me Rahma me jinkai yabo da godiya sun tabbata ga sarki Allah . tsira da aminci su Kara tabbata ga manzon tsira Muhammad Rasulillahi .

DEDICATED DIS PAGE TO U MY LOVELY GRAN FATHER
ALH.ADAMU JAOJI
ALLAH YAJA DA RAI YAKARA LFY ????

              2⃣6⃣

Yana shiga gidansa da azama ya daura Alwala .yashige dakinsa .ya Dade yana jero salloli daga bisani yadauki Quran yafara yakaranta wasu surori daga cikinsa nanma yadau tsawon awa guda .sannan yafito yakara Alwala yajeasallaci yai sallar laasar

Dakinsa ya koma yadauki casbaha dinsa. Yaita wuridi

Har lokacin sallar magriba .yafito yaje masallaci
Baishigo gidanba saida akai .ishai

Bayan yaci abincinsa ya gama
Dakinsa yakara komawa donya fuskanci many an shedanu aka hada Alh dasu .suke juya akalar rayuwarsa sai yanda sukai dashi

Aikin zaiyi wuya kasancewar. Alh baya kasa .don akwaibukatar ace yana nan don akwai ayoyin da zaa rubutamai .kuma atofa masa wasu aruwa yasha

To kuwa tunda haka ne .saiya dage yafara karkato da hankalinsa yayo gida

Don haka kwana yai yana salloli da wuridi .na Neman nasara sannan yana rokon Allah yasa adace .bashi ya runtsaba sai bayan gari yai haske .washe gari .sannan ya kwanta ya huta

Ka’in da na’in yake aiki akan Alh .har tsawon sati guda

Yana can China yaji garin yamasa zafi ya isheshi kawai so yataho gida don haka yahada dik wani abubuwansa yayo gida

Baby tana kwance a daki sanyi ya isheta sabida zazzabin daya rufeta tun safe

Jijjiga dikkan jikinta yakeyi .sosai sai kuka take
Batasan ya zatayi ba don haka taga kukan shine magani .yinshi take iya yinta .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button