BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Nanma andau tsawon awa guda sannan police din suka dawo da wancan likitan na gwamnati .ya kawo result din baby akan cewa baby wata alamar anmata fyade .saidai cutar ulcers da nimonia da tyford daya gano.

Kasancewar dik yanda sukabi sungano sharri su hjy sukaiwa umar me wanki .kuma sukeso suyi amfani da wannan damar don bata rayuwar. Baby . su bata sunanta a duniya tun tana karama
Don haka DPO yace asaki umar kuma su hjy su bashi tarar naira dubu Dari biyu sakamakon sharrin da sukaimai

Don badanma Alh yace baya son tada maganarba .dasai sin kwana a sale cewar DPO kuma yace suje .washegari karfe Tara na safe su tabbatar .sunkawo kudin nan office din

(Hhhhmmmmm bahaushe yace inzaka gina ramin mugunta ginashi daidai kai don bakasan ko kai zaka fadaba )

Suna fitowa daga police station anfara sallar magriba don haka .Alh .yatsaya yai sallah sannan ya wuce asibitin don dik hankalinsa nakan khausar .

 Yana shiga yaganta a kwace har sannan bacci takeyi ga ruwa ana samata .wani kuka ne yakwacewa Alh ganin irin rama da bakin da khausar  tayi gashinta yakallah .gaba daya yafita daga siffar baki yakoma ruwan kasa kasa ja ja ja ja  ga wata Riga ajikinta ta jeens ce amma tayi fari ta kode ta jeme . 

Kuka yake yana fadin babyna ki yafeni kiyimin afuwa naci amanar maraicinki naci amanar mahaifiyarki .na wofantar dake .wlh bansan meke faruwa daniba naji na tsaneki lokaci guda bansan ya akaiba baby kimin gafara na cuci maraicinki khausar ????. Nasan tabbas dani na mutu mahaifiyarki bazata bari rayuwarki ta tozarta ta wulakantaba
Amma gashi ni nakasa kasencewa uba me adalci agareki baby

Sheshshekar kukaansa ce ta farkar da ita .tana bude ido kamar amafarki taga Dad dinta akusa daita rike da hannayanta
Tureshi tashigayi .tana fadin ni baruwana dakai dad tunda kadaina sona baka kulani yaya Bilal kadai kakeso nima bana sonka katafi abinka Aysha kawai nakeso tafada tana rushewa da kuka

Gaba daya ya gigice yarasa me zaice mata kawai shima saiya cigaba da kukan
Tsam ta tsaya tana kallonshi ganin yanda yake kuka harda shashsheka .tana kallonsa cikin dashashiyar muryanta na marasa lfy
Tace Dad mene kake kuka bakaci abinci bane kaima kanajin yunwane kake kuka?
Dad waye yadakeka me akaima kake kuka

Ahankali ya tsagaita .yashiga shafa bayanta yace Baby kece kikace bakya sona shiyasa nake kuka
Zunburo baki tai tace to dad ai kaima baka sona Ya bilal kawai kakeso bakamin magana .baka bani ice cream. Agabanka su momy da ya suke dukana .amma baka hanasu .
Share hawayan daya kara sauka a idonsa yayi yace is OK my sweet baby .na daina bari kowa yadakeki .zan rika suyomiki . biscuit. Sweet. Chocolate. Ice cream. Zeeza .and dik abinda kikeso .zanje dake .unguwa zanmiki doki .kinji baby
Dariya tai tace Allah dad yace da gaske baby .
To shikenan dad yanzu nadawo sanka .kaima tunda ka dawo sona .
Kwallar idonsa yakara gogewa .ya kalleta .gani yai harta .kara rufe ido alamar baccin nakanta

????????????????????????
29/9/2017
[10/2, 11:44 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY. KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

              3⃣2⃣

Tsakanin da da mahaifi sai Allah wani dadi baby takeji intai baccinta ta farka taga Dad dinta zaune kusa da ita

Dik bayan Dan lokaci sai likita yazo yadubata
Yacewa Alh yaje gida akwai wayanda zasu kula da ita Amma yace a a zai zauna da abarsa donshi kam yanzu yadaina zuwa ko nan da can yabar babynsa

Da safe wajan karfe bakwai yadauki wayansa ya lalubo number din Mlm Khalil wata kunyace ta rufeshi daya tuna iya tsawon lokacin daya dauka baikira Mlm ba .
Gabansa ne yafadi dayai tunanin anyama kuwa Mlm yana raye tsawon wannan lokaci .?
Da sauri yadanna number din can. Tafara ringing gabansa naci gaba da faduwa don baisan .wazai dagaba .
Gada can bangaran yaji sallamar Mlm .wata ajiyar zuciya yasaki tare da amsa sallamar .ammafa daga nan yakasa furta komai .don bakinsa yamai nauyi

Daga daya bangaran Mlm yai mirmishi yace Alh.ka dawo ne .ai nazo gidan kwanaki akace baka kasar

Shiru ba amsa .

To ya iyalin ya Khausar da Bilal dik suna lfy ko .
Da kyar ya bude bakin yace .eh Bilal lfy .saidai khausar dince ba lfy .yanzuma muna asibiti an kwantar da ita
Subhanallahi .a wane asibiti kuke
Nan yafada mai

To insha Allah zanshigo inga jikinnata Allah yabata lfy .
Ameen Mlm na gode

 Ajiyar zuciya yasauke yana fadin waito me  yasameni .ne .Mlm ma da yake tamkar uba gurina shima na yardashi .kai Allah ya shiryeni shine kawai abinda yafadi .yajuya .yana kallon baby 

Kasancewar asibitin bana wasa bane yasa dik wani Abu da Mara lfy zaici su zasubashi .irin abincin daya dace da jikinsa
To sannan gana me jinya nan zaa kawo mai ga flasck nan zaa zubo ruwan zafi akawo muku .ko wanne daki

Don haka ana kawowa yatashi baby yahada mata ruwan tea yana bata abaki tanasha .sannan ga sakwara da miyar agushi nan taji ganda .shima yabata taxi kadan ta koma ta kwanta
Shikuwa ba abinda yaci acikin abincin donba cimarsa

Kiran sarkin gida yai yace maza yaje hotel ya hadomai dik kan irin abicin dayasan yanaci yakawomai asibiti

Wajan karfe biyu saiga Mlm yazo asibitin da kyar Alh. Yagaisheshi.don kunya
Dik abinda yake Mlm yana ankare saibayan yagama yiwa baby sannu .yajuyo Kansa yashiga masa nasiha akan ruko da addini. Yace kaga Alh.dik sakaci dakai da addua shiyasa Sihiri yai tasiri akanka .
Hakika asiri akai maka aka Shiga tsakaninka da Baby .don ka tsaneta ka fita harkarta

Jan numfashi yayi yace Mlm yanzu wa kake ganin yamin wannan aikin hakika saina dau mataki akansa

    Abinka da Mlm yasan abinda yakeyi .sai yayi mirmishi yace  kawai kabar tanbayar waye .bashi da amfani . tunda dai anyi nasarar karya sihirin

Haka dai Mlm yaitaiwa Alh nasiha akan ya rike azkar sosai don bawai kyaleshi akaiba wayannan masu asirin zasu ci gaba da bibiyarsa

????????????????????????
30/9/2017
[10/2, 11:44 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

          NA

LAYUZA KABIR ADAM

           3⃣3⃣

Kwanansu uku A asibiti amma Alh ko gidama bai jeba .dama jakar kayansa daya dawo da ita daga tafiya tana bayan mota Dan haka yasa sarkin gida yakawomai ita .
Baby kuwa kudi yabawa sarkin gidan yace yaje baby love na nan zoo road yasiyo mata dogayan riguna da pant.
Dik dai abinda zasu bukata yabayar ansiyo musu .
Kullum shida sarkin gida suke a asibitin sabida yan aikace aikaicen da baa rasaba

Zamansu a asibitin yasa shakuwarsu da Mahaifinta ya dawo kullum zai mata wanka ya wanke mata wannan dankararran gashin daya hada uwar dauda
Hira sosai sukeyi .taita bashi labarin irin bakar wahalar da hjy da Bilal suke bata agidan da rashin bata abincin da sukeyi .wani labarin inta bashi sai dai yaji hawaye yana gudu a idonsa .don tausayinta .

Haka zaita cewa kiyi hakuri babyna ki yafemin dik ni najamiki laifina ne . sakacina da addua har yasa akaimin asiri yacini .na dauke hankalina akanki .aka samu damar cutardake
Yanzu na gano Amina ce ta aikata komai kuma wlh saina dau mataki akanta .

Yanzu dai Burina kisami lfy dik zanyi gyara zan dawo miki da farin cikinki da jin dadinki.kinji Babyna
Inya fadi haka mirmishi take. Tace
To Dad

Ita kuwa Bidimar banzar .ko tunanin zuwa asibitin duba. Baby bataiba .tana ta yawon kara Dora asirinta daga inda ta tsaya .don ta fahimci wancan ya karye ba dare ba rana. Kullum suna yawon bin bokaye
Abinda basu sani. Ba yanzu Alh.ya dage da azkar safe da yamma kullum cikin salati da hailala yake .

Adaya bangaran kuma Mlm Khalil yanacan yana kara .yin aiki .akansa kuma yana kara bashi wasu adduoin yanayi

Shikuwa  umar .ma iya cewa  gaba takaishi tunda gashi anbashi   dubu dari biyunsa .amatsayin Tara .

Randa sukai sati Daya a asibiti aka sallamesu akan cewa kullum Doctor zairinka zuwa gida yana dubata dikda cewa ta warware har tayi yar kiba
Kai tsaye daga asibitin. Sabon gari yace direba yakaisu .
Kudi yasakarwa masu saloon yace a wanke mata gashi a mata kitso.
Aikuwa kafin me nan da nan suka Shiga gyaramata kai yafito yai fes .cayai kar suyi mata kananan kitso .suyimata manya don bazata iya zaman kananaba .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button