BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Baa dadeba .suka gama .
Daga nanma . Wani Katon. Boutique sukaje Yamata siyayya kamar hauka .tundaga suturu takalma . abindai baa magana sannan wajan Kayan wasa daga nan sukai wajan Kayan ciye ciye
Komai katan guda yadaukar mata su chocolate biscuit. Cheese balls.

Sannan sukayo gida .sanda sukazo gida hjy bata nan danhaka kai tsaye part dinsa sukayi . da kansa ya kwabe yashiga gyaran wajan .bayan yagama .yaiwa baby wanka yashiryata . shima yayi bayan yashirya .yadauko musu kazar daya siyo musu .sukaci sukasha fruit. Zuwa lokacin anyi sallar magriba .
Masallaci yatafi yarufeta adaki.

Bayan ya idar yana shigowa .Tatar hartayi bacci
Daukanta yai yadorata kan gado.

.to itadai hjy bata dawoba sai wajan goman dare .don haka batare da damuwa ba tashige bangaranta .

Layuza kabir Adam ????
[10/2, 11:44 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

        3⃣4⃣

Karfe takwas na safe yafito yake zaga gidan da maaikata .anan yaga umar yakara bashi hakuri akan abinda yafaru
Ba komai Alh .Allah dai yatsare gaba

Ahaka yazagaya .yarabawa kowa kyautar 10k

Dik zagayan dayake baby na biye dashi ya rike ahannunta .
Dik Wanda suka gaisa saiyawa baby yajiki.aransu suna .jin dadin ganin yancinta yadawo

Yajuyo zai koma part dinsa itakuma hjy tafito daga nata .da shirin fita .sukai kicibis

Dam dam taji gabanta ya buga don bata taba tsammanin ganinsa .

Da in ina .tace Dadyn Bilal dama kun dawo ne .

Wani wulakantaccan kallo ya wulla mata .baice kala ba yashige tare da banko kofarsa

Jiki amace murus taja kafa takoma .sashinta
Wayanta ta dauka takira .hjy Maryam .tabata labarin abinda Alh .yamata
Catai ke dallah kidaina nuna tsoro .ko ba asiri ai akwai kissa in kinyi kissar kinga ba ja .kizama mara kunyar karfi da yaji ki nuna mai bakya tsoronsa .to zai hada naman jikinsa waje daya .

Yawwa kawata na gode .ina alfahari dake .Allah yabarmin ke .kinga yanzu nafasa fitar .kawai mu bari gobe sai muje

Tashi tai tashiga part din Alh.ta kofar parlour nta .a parlour tasamesu .suna kallo baby ta kwanta kan cinyarsa .tana tamai tanbayoyi .shikuma yana bata amsa kamar .yana hira da babba.

Sallama tayi tazo tasami waje tazauna
Inya kalleta to Wanda bai wajenma .yakalleta .tausasa mirya tai tace Alh.yajikin babyn .taso kizo nan baby .inga jikinnaki
Ai kamar dodo kemata magana haka ta gigice ta rukunkume Dad dinta .tana fadin dad ni bana kulata bazanje guntaba .dukana zatai

Ganin irin gigicewar dataine yasa yace Amina .fita daga nan bansan ganinki kin gigitamin Yarinya .

Haba Alh nazo mata sannu zakace ———- ke gate aut in my side

Bansan maganan banza wuce daga nan sum sum tamike tai waje .

To haka hjy.tashiga shishshigewa Alh .da kissa Kala kala amma kallo bata isarsa balle yatanka .

Dik bidirin da ake Bilal dai yanacan Lagos gurin mamansa yaje musu Hutu.don haka baisan wainar da ake toyawaba agidannasu

Yau dai da rashin kunya hjy. Ta tashi tunda taga kissar taki shiga bari tai fitsara ko zaiji tsoronta .

Don haka tana tashi .tashiga part dinnasa ko tashi abacci basuyiba .
Da karfi tafar fadin .Alh. Wai wannan wane irin baccin asara ne kakeyi haka
Ga ya ka nanika ajiki kamar wata jinjira .
Juyi yai yaganta akansa .kawai yakara Rungumo baby yai yaja blankcate yarufesu .

Salati tasaki tana fadin wai Alh wane irin sabon addini ne wannan ka saka ya agaba .kana runguma .yarda in a kauyene anmata miji .ah gaskiya da sake nikam banyardaba
Kaito waima meye naka nakarinka kwana da ita adaki daya harkasata agdo ka runguma .
. wai inama magana kayimin banxa ko dik kunyace ta hanaka magana
Aikin banza kawai .kadai rinka tunawa yarkace .eheeee

Tashi yai yazauna .yace ke wai Amina wace irin dabba CE tinkiya .wadda bikisan me kikeba balle me zaki fada .

Amina ina kyaleki ne wlh sabida Abu uku
Sabida inna tuna yayana ne .yadauramin aure dake sai inji bazan iya kunceshiba
Na biyu inna tuna rukon da yayarki tamin tsakani da Allah .sai kici darajarta

Na uku inna tuna cewa Bilal dake kadai yasaba matsayin uwa sai inji bazan iya sanyashi maraiciba

Wannan dalilanne yasa kike zaune gidannan amma wlh hakurina yakare kin kureni .kibini asannu
[10/2, 11:45 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA 

LAYUZA KABIR ADAM

         3⃣5⃣

Shigewa toilet yai zuciyarsa cike da bacin rai don Amina takaishi makura wlh. Badan yayartaba da tuni yarabu da ita
Sabida bata sonsa bata kaunarshi .eh mana tunda bata son Gudar jininsa aikuwa bata sonshi
Kuma wlh ko Bilal taiwa haka irin matakin da zai dauka akanta Kenan
Dikda yasan bazataiwa Bilal dinma haka ba tunda tasan shi jinintane dan yayarta

Wanka yai yafito ya shirya don yanason zuwa gidan Mlm yau don tunda suka dawo daga asibiti baya fita ko ina .komai ta computer yake turawa office dinsa agudanar da abinda yadace.

Tashin Baby yai yamata wanka yasamata wata .gown red .da kwalliyan fari Me Dan siririn mayafi fari yadauko mata wani takalmi fari yasamata

(Nace Alh.kamar mace ya iya had a marching????)

Fes dasu suka fito parlour. Ruwan zafin dake tea flask ya dauko yahada musu tea .yadauko musu cake
Nan da nan sukayi break .
Baby tanata murna zasuje unguwa

Yafito Kenan daga parlour dinsa .yashigo ta part din hjy don yanasan yasa fad lock. Yarufe kofan don baisan ma tana shigarmai bangare

Abinda yaji suna tattaunawaya ne yasa yaja yatsaya cike da dinbin razana

Kinaji na maryam .daman kamar yanda kika fada inna bata poising taci tamutu inbincike yazo takaina zai fara to nabar wannan shawarar
Yanxu muna kan taki shawarar

Inzai fita salla ai rufeta yake to kinga .yana fita sallar magriba .sai sushigo .su dauketa .da kudade da takardu sabida kar agane ita kadai sukaje dauka . suyi sata sosai .sannan inbude musu kofar baya tacan daji su fice .inyaso ma ni insunzo sundauketa dik yanda sukaga dama suyi da ita. Donni banson ko sunanta naji an anbata .sai inji kamar zan mutu .
Saida tagama sakin baki tafadi dik abinda yake ranta sannan sukai sallama ta kashe wayar .
Juyowar dazatai taci karo dashi tsaye kam sosai ta firgita da ganinsa . don haka tashiga fading ehto meye kazo min sashina.iyye

Ke dama kinada wani. waje agidannan dazakimin iyaka .to wajan da kike cewa naki yau zaki barshi 

AMINA KI BARMIN GIDA NI ALIYU NA SAKEKI SAKI DAYA

Kuma banso ki kara koda awa guda agidana

Wani ihu tasaki tana fadin kaci karya Aliyu kace kasakeni .karya kake ba inda zani .wlh
Banza Wanda bai San hallacciba kan wannan yar iskar yartaka me kama da mayu zaka sakeni

Wayyo ni Amina ???? zuwan hadiza gidannan masifa ce agareni.shegiya kilama diyar mayuce matsaf————
Bata karasaba yadauketa da mari ya hankadata daki yace maza hada kayanki kibarmin gida .

Wani tinani tayi nan da nan taja wani dogon mirmishi ta ja. akwatuna tashiga jibga kayanta .saida tacika guda uku .sannan tafito tasasu  a motarta tabar gidan 

Ganin tabar gidan yasa Yakima yarufe ko ina sannan yafito shima. Direba yajasu sai tarauni gidan Mlm Khalil kamar yanda yacemai
.
Mlm da faraarsa ya taresu bayan sun gaisa Babah matarsa ta leko suka gaisa sanna taja khausar dakinta ta zuba mata dumaman tuwo
Aikuwa. Tazage tashiga ci

Komai daya Faru yau Alh. Ya kwashe yafadawa . Mlm

To bazance baka kyautaba Alh amma dai daka kara hakuri da ita .kasa mata ido sosai ba abinda zai kara samun khausar da yardar Allah

???? takuce Layuza kabir Adam

????????????????????????????
[10/2, 11:45 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button