BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Mirmishi yai .yace. Sadiya me kikace
Nace don Allah ka daukomin baby tarinka tayani zama .inka fita sai gidan yamin shiru .kaga inda ita zata rinka debemin kewa
Ok karki damu bari u kammala cin abincin saimuje tare gidan Mlm din kema ki gaisheshi .
Yawwa ko kaifa .yallabai .
Suna shiga gidan Mlm suka sami baby sai rigima take .itadai akaita gun dad dinta .ta gaji da zaman gidansu .tana so tai wasa su kuma gidansu ba Kayan wasa
Jin sallamar Dad dinta a bakin parlour yasa ta zuwa da gudu ta rungumeshi
Shafa kanta yai yace baby
Ya dai . turo baki tayi na shagwaba tace bakaine .ka tafi kabarni ba tun kwana da yawa .ruko hannunta yai suka shiga cikin parloun .
Bayan an gaggaisa .suka kara musu Allah yasanya alkairin aure .
Khausar ta dubi Dad dinta tace Dad wannan ce Sabuwar momyn da kace .zaka kawomin ?
Eh itace baby jeki gaisheta .da sauri tazo jikinta tace momy sannu da zuwa kema kina bulala da mari ?
Girgiza kai tayi tace a a .bana duka da mari saidai in anyi rashin ji .
To ina sonki tunda bakya duka .nikuma bana rashin ji ki tanbayi Dad dina ma ko dad ta fada tana kallonshi .
Dariya yai yace kai baby sarkin surutu .kiyi shiru haka
Shidai Mlm nasiha yai misu sosai .mussam ga sadiya ya kara nuna mata falalar da daukakar da mutum yake samu .inya kula da maraya .don haka yaja hankalinta sosai da ayoyi da hadisa .
Sosai takajin .son kula da khausar yashiga ranta dik da dama ita da niyar riketa amana tazo gidan .
Bayan sunje gida . Lokacin goma tayi .don haka kawai shirin kwanciya sikai .
Da safe .bayan sungama .yin break. Taiwa baby wanka .tacewa Alh .kayan babyfa .zuwa yai ya bude bangaranshi ya kwaso dikkan kayanta na wajan .sannan ya debo na bangaran hajiya . har Kayan wasanta baibai komaiba
Aranar suka shirya mata daki guda .Asama da kayanta . kana ganin dakin kasan na yar gata ne
Haka rayuwa take in wani yakika da yini wani saiya soka da kwana .
Gashi yanzu Baby kulawa take samu kamarme don sadiya akwai tsafta da kwalliya
Bayan kwana biyu da gamma suna .zaune akasa .hjy sadiya tana karanta jarida yayinda baby ke kallo . Alh yai sallama yashigo .Islam na rike da hannunsa . wata kara Islam tasaki taje ta rungume Mamanta tana fadin mamy na oyoyo .saikuma
[10/2, 11:45 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
3⃣9⃣
Dawowar Islam gidan yakara dadada. Ran Baby don tasami abokiyar wasa tare mamy take musu komai nuna ban banci ko kadan tsakinsu haka suka koma tamkar yan biyu .Wanda bai sani yagansu zaice .yan biyu ne
Don haka Alh ya dage wajan yimusu don yanda yaga mamynsu namusu kwalliya abin na burgeshi. Ta kara samun fada a wajansa
Shi Alheri danko ne Wanda yaishi xai dawo mai .Wanda baiba ma zai gani
Tun randa Hjy Amina taji sanarwar daurin Auran Alh.da sadiya ta gigice .hankalinta yakara tashi .ba shiri .yabi jirgi zuwa Lagos gun yayarta don adacan bataso tasan maganar sakin .amma yanzu tunda gashi harya kaishi ga aure .ai yazama .dole .taje ga yayarta ta .
Karya da gaskiya ta kwashe tafawa yayartata . atake .hjy halima tadauki waya takira .Number din Alh. Amma akashe . tundaga ranar kullim saisun kira wayanshi yakai sau hamsin baya Shiga .do haka hjy.halima tace bari me gidanta yasami sauki don baida lfy .saisu taho .tare yaji meke faruwa har zaiyi saki kuma bayan sati uku ya daura sabon aure
Yau da magriba Alh.yana zaune kan kujera tunani yakeyi .meke faruwa tunda yasaki Amina .baiji hjy halima ta nemeshiba .kodai Amina bataje Lagos ba .
To koma mene itasu .donshi gobe .zai tura sarkin gida yabi jirgi ya dauko Bilal don saura kwana hudu akoma skul
To wajan sha daya na dare .harsun kwanta .yaji ana bude babban gate .wayarsa ya dauko ya kira me gadi .yake tambayarsa waye yashigo gidan yanzu .
Cikin girmamawa yace Alh. Baki ne .suke tare da Bilal .da su uku ne dai harda namiji.
Kashe wayan yayi yazira jallabiyansa .
Alh lfy .ina zuwa da darannan .mamy ta fada .
Ina zuwa wai baki ne suka shigo zanje inga su waye
Yana fitowa suna shirin kwankwasa tsohon .part dinsa
Da sauri ya karasa ganin hjy halima ne da me gidanta .sai hjy Amina da bilal
Da gudu Bilal yazo ya rungumeshi yana fadin Dad oyoyo. Shima hannu yasa ya runhumeshi .yana oyoyo my son .ai da gobe sarkin gida zaizo ku taho .
Jagora yai musu zuwa cikin gidan
Bayan yan gaishe gaishe .
Mijin hjy halima yai gyaran murya yace .Alh.Aliyu ba tare da jan lokaci ba Amina tazo da maganar saki .ya akayi me yahada Ku .
Alh.ya kallil Bilal yace my son je dakinka .ka kwanta
Don bai son jin abinda zaice
Yamike yashige dakinsa don dama agajiye yake
Nan Alh.ya kwashe komai yafada musu bai rageba
Aikuwa hjy halima ta inda tashiga ba tanan take fitaba .daga karshema kuka tasaka don ta bata mata rai
Me gidantane yashiga bats
Hakuri hartai shiru.
bayan ta tsagaita .me gidan ya kalli Alh yace to Aliyu kayi hkr Amina tayi kuskure kuma ta gane kuranta don haka inaso ka maida matarka dakinta .
Bazai iya mai musuba sabida matsayinsa na aminin yayansa marigayi .kuma ga hjy halima azaune ya dubeta yace bazai maida Amina ba abin da kunya
Anan dai aka sasanta yamaidata
Dakinsa yakai Alh Ahmad.ya kwanta anan .
Shikuma Ya koma bangaran sadiya .don ko son kallon Hjy Amina baiyi
????????????????????????????
[10/2, 11:45 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
4⃣0⃣
Sanda ya. Koma bangaran sadiya. . samunta yai zaune da system dinta tana ta research
Zama yai kusa da ita. .yace. Sadiya biki bacciba haryanxu . kalli agogo fa 1pm
Ahankali ta dago takalleshi tana rufe system din tace .ya zanyi bacci. Ka fita tundazu baka shigoba
Mirmishin jin dadi yayi yace yi hakuri madan ina can hankalina na kanki .
Wlh maman Bilal ne suka Zo da megidanta sun dawo da Bilal .kuma sukazo kan maganar Amina
Yanzu dai an daidaita ta dawo .kiyi hakuri da dik abinda zaki gani agun Amina
Nasan halinki Sadiya kuma ina alfahari da ke .kiyi hakuri kinji
Mirmishi tai tace to mene abin ban hakuri Yallabai dama ai gidanta ne .taje Hutu ne kawai ta dawo .kasan ance fadan masoya Hutu
Kallonta yai don ya hango tsantsan kishi a idonta
Tabdin dama dik kyan halin mace baa rabata da kishi
( To banda abin Alh. akayi kishima agidan manzan Allah gidan dayafi kowane gida mata masu kyan hali )
Bai kara maganaba ya tashi yashige toilet.
Tun sallar asuba Hjy sadiya bata koma ba .tashiga kitchen . abinci kala kala ta shirya .wajan karfe Bakwai ta fito .daga kitchen din .tana shiga dakinta taga Alh.yanasa Kaya alamar yai wanka Kenan .karasawa tai tana mai mirmishi .tace .barka da safiya . um um bazan amsaba .yau kinbarni ni kadai na shirya kaina .kina can gun yaranki ko
Mirmishi takara yi .ta dau hularsa ta sakamai .sannan tace ba gun yara najeba .ina kitchen. Na shiryawa bakinmu abin break ne .
Kallonta yai tsawon lokaci kallo me cike daso da kauna
Yace sadiya wai dama akwai mata irinki da yawa a duniya sadiya Allah yaimiki Albarka
Kinga yanzu saurin da nake .infita .insa direba yaje 7:30 restored yasiyo musu abinci
Ashe ke kina kitchen kina .kina hada musu .sannu da kokari sadiya sannu Allah yasaka miki da Alkairi .
Da mirmishinta da yazameta .dabiarta .tace .Na gode da adduarka .hakika inhar zanci gaba da samun wannan adduar daga gareka. Nasan .tsakanina da Aljanna mutuwace kawai .
Lakace mata hanci yai yace .hhhmmm sannu .bari inje mu gaisa dasu.
Zan turo adauki abincin yanzu kema ki shirya saiki zo Ku gaisa .
Ok to shikenan bari inyi wanka zanzo
. yana fita .kai tsaye .yai part dinsu
Dik A parlour yasamesu .zama yai suka gaggaisa .ya juya yace My son jeka .kira masu aiki mata guda. Biyu .ka kaisu gun sadiya .kace wai tabada abincin
Mikewa yai yafita
Sukuma sukaci gaba da hiransu
Baafi minti biyarba suka shigo dauke da Warmer’s na abinci .da . flask sin tea Dana kunun gyada .can gefe kuma ga kosai .da hadaddan farfesun .Kayan ciki.
Bayan sun ajiye suka fita
Alh yadubesu .yace bisimillah .kuci abinci nima bari inje ciki inkarya .
Alh .Ahmad ya amsa masa da to afito lfy.
Sanda yashiga .Hjy sadiya harta fito a wanka da sauri Saudi ta shirya .taje ta tashi baby da Islam .tai musu wanka .sannan ta basu Kaya sukasa .suka fito parlour don suyi break sanda tazo .shikam me gidan harya gama nasa .
Tazubawa yaran sukaci tare .sannan ta koma dakinta ta kara gyara fuskanta ta dauko .mayafinta .
Tana saukowa daga .stairs. Alh .yashigo parlour yace .sadiya zoku gaisa da wuri zasu wuce yanzu don jirginsu karfe .Tara zaitashi.gashi yanzu takwas ma ta gota
[11/13, 10:48 AM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY. KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
DOLE INGAIDAKE .UWAR DAKINA .????
????????????????????