BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummy katsina (maman_ muhd )
- Admin – ingattattun mata
4⃣1⃣
Cike da Aji irin nasu na manyan mata .tai sallama Alh.na gabanta
Hjy halima da me gidanta ne .kadai suka amsa don Hjy Amina .kauda kanta tai gefe
Waje tasamu ta zauna .ta gaishesu cikin nutsuwa da Aji
Dik da faraarsu suka amsa
Hjy halima race sannu da kokarin girki sadiya .munga Abinci mun gode .
Allah ya hada kanku
Alh.Ahmad yai masu nasiha .ta zama lfy .a gurguje .
Sannan sukai musu sallama Direba
Yajasu zuwa airport.
Itadai hjy Sadiya .ko takan hjy Amina batabi ba ta koma sashinta
Bayan tasa masu aiki su kwaso mata filasanta daga bangaran hjy.
Tana shiga sashinnata ta Tatar dasu baby da Islam can dining aria suna was an buya .kallonsu tai da mirimishi .tace .bari In .inje in huta .
Kuma kar amin barna .
To mamy suka ce suna dariya
Sai wajan karfe .biyar Alh.yadawo gidan don daga rakiyar su Hjy halima .office yawuce
. yana shigowa ba kowa parlourn kasa su Baby suna islamiyya .
Sama ya haye . azaune .yasami gimbiyar .idonta dauke da glass .tana amfani da system dinta .don ita bazaka taba samunta .tana zaman banzaba
Da mirmishi ta tareshi.ta karbi briefcase din dake hannunsa .tace yallabai .sannu da zuwa .
Yawwa sannu .madam ya gida
Gamu cikinsa ta fada .tana bude frige. Ta dauko mai ruwa me sanyi da .lemo .
Ta zauna kusa dashi .tazuba a glass cup. Tasa mai abaki
Bayan yasha . yariko hannunta yace sadiya .ahadamin ruwa .me .zafi sosai inyi .wanka .
Ruko hannunsa tai tana fadin.angama ranka ya dade amma da Alama .yau akwai gajiya tare dakai
Hhhmmm kedai baa cewa komai .gimbiya .nayi baki sosai yau .sallah kadai ke tadani a office. Yau
Bayan ta hadamai ruwan . ta fito ta taimaka mai yacire kayansa .sannan yashiga wankan
kafin yafito ta daukar mai Kayan da Zaisa sannan ta hadomai abinci . ta kawo mai har daki .
Don tasan zaifi jin dadin ci an an tunda gajiye yake
Bayan yafito a wankan yashirya .yazauna .yanacin abinci tana mai hira
Yana gamawa ta fita da Kayan kwance tasameshi kan gado .mirmishi tayi tace .sannu da kwanciya saura fa 30minit .a kira sallar magriba
Limshe ido yai yace sadiya bari inhuta kafin akira
Zama tai kusa da kafarsa tashiga matsa mai .
Sadiya yau wani abokin kasuwancina . ba indiye yazo .bayan mungama abinda zamuyi .yake fadamin .sun bude wata makaranta .babba .agarinnasu .ta engineering. Amma sai dalibin dayayi .secondary school. Dinsu .suke dauka .amatsayin .Wanda zaiyi university. Abangaran engineering din .dik ragowar kwasa kwasai .kowane dalibi daga kowace .skull zai iya shiga .
Amma course din .engineering sai wanda yai secondary skull tare dasu .sabida itama secondary din tasu .gaba daya ta engineering din CE .
Sairai nasan mutumin .baya wasa da abinda yasa gaba .
To kuma .kinsman Bilal .burinshi yazama injiniya .naimai alkawarin yana gama secondary. Zai fita dashi waje .yayi to kuma kinga .ga wannan daga yanayin yanda yakemin bayanin .skul din hankalina ya kwanta da ita .
Don haka .nacemai inason Bilal yayi amma amma shi yana s s 2 .ne yanzu .sukuma sunfison a fara daga jss1. Ko ss1
To yanzu dai mungama komai yau harya tura .komai can ga director din mkrntar .sun amshi Bilal din amma amatsayin Dan ss1 . hakanma Dan nine mungama komai har kudadansu na tura musu .na skul Dana hostel .
Yanzu dai atakaice jibi zasu koma .zamu wuce dasu da Bilal din
???????????????? .
[11/13, 10:51 AM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
4⃣2⃣
To yanzu Alh .baka ganin andawo da karatun yaronnan baya?
A a .ba matsala ai ba saurin karatunba .ai asami abinda akeso
Kuma dika Bilal din Nawa yake .
Hhhhmmmn nasan shugaban skul dinsu zaiji ba dadi .na dauke mai .lion student nashi .don yanaji da Bilal a mkrntar nan .lokacin da najewa .Islam .registration. Yanata munna .ya kara samin Karin .student. Daga gidana .to gashi kuma ya rasa .wani .
Sai hakuri .inason Bilal yayi karatu sosai yazama wani abu da .duniya zatai Alfahari dashi…….kiran sallah ne yasashi katse zancan.yamke yashi toilet. Don dauro Alwala
Saida akayi ishai yashigo .gidan yazo .yaiwa .hjy sadiya sallama .don ba yanda zaiyi dale yau ya kwana bangaran hjy Amina .ko Dan yazama adalin .namiji agidansa.
Yana saukowa down stairs. Baby na kokarin hawowa .sungumarta yai ya dawo da ita kasa yana dariya yace kai Babyna .kin girma yanzu nadaina .daukanki .mamynku tana cikamiki ciki .da abinci
Ina Islam din .Ba tana computer room ba .tana game. Wai nace ta bani taki.
Kuma ba ruwana da ita .a a .baby wayace miki ana fada da dan uwa .itama wasa takemiki.data hanaki.
Jekice injini .inta gama ta baki aro
Ko xansa ma akaro muky daya .mu huta da fada.shigewa dakin dake gefansu. Tai da gudu tana fadin .Islam dad yace nima kisammin in danyi
Kallon hjy sadiya yai yace madam bari in fice .karda wannan yar rigimar ta kara fitowa
To yallabai saida safe Allah ya tashemu lfy .
Ameeen matar kirki .ya shafi kanta ya fice .dik jikinsa amace don yasan bangaran hjy Amina cike yake da tarin bakin ciki..don ko kallonta baisonyi
Lokacin daya shiga main parlour din suna zaune itada bilal suna kallon tashan arewa 24
Da sauri Bilal yaje yamai oyoyo Dady
.shafa kansa yai yasami kujera yazauna
Baiko kalli inda hjy take ba yace my son.
Yace na’am dadh
Nasama maka admition.a India .
Da sauri yadago yace dad saura fa 2 years .yarage .muyi graduation amma har ka nemamin admition yanzu
A a bani hankalinka nan Bilal kaji .nan dai dad ya zaiyanewa Bilal tsaf abinda .yayimai na shirin mkrnta.
Shiru Bilal yai yarasa ma me zaiyi farinciki kome .
Yanaji kayi shiru. Bilal my son ko baka so ne
Girgiza kai Bilal yai yace dad nama rasa me zance ne wlh .na gode Dad Allah yasaka da alkairi Allah yaja da rai .
Mirmishi Dad yai yace karka damu my son farin cikinku shine nawa . donkai da kanwarka baby nake Neman komai aduniya sabida rayuwarku ta inganta .yanzu tashi kaje daki kafara shirya kayanka don gobe .kana tashi kazo inba ka kudi kaje kasuwa kai siyayyan dik abinda kakeso mikewa yai yai daki ya yana fadin to Dad mu tashi lfy
Tunda yashiga daki bakin gado kawai yasamu yazauna .tunani yashigayi da dad yace kanwarsa shifa harga Allah yamanta da wata baby khausar inbanda yanzu da Dad yai maganarta amma abinda yabashi mamaki yanzu baiji tsanarta aransaba daya tunata
Ganin tunanin bazai maiba yatashi yashiga hada kayansa acikin akwatina
????????????
[11/13, 10:52 AM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY. KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
DEDICATED. THIS. PAGE TO U ALL MEMBERS
.BABY KHAUSAR .FANS .GROUP
4⃣3⃣
Yana Barin parlour din shima Alh.yamike .yashige part dinsa batare daya kalli ko gefan datakeba
Jiki a mace itama. Tamike .tabi dakin Bilal . bakin gado tasamu ta zauna fuskar nan cike tam. Fishi .tace wato Bilal yanzu ka amince da Maganar Dad dinka .tafiya mkrnta zakai kabarni agidannan cikin kunci ko Bilal kasan sarai kai kadaine hasken idaniyata .kaine farin cikina agidannan .kai kadai ke kaunata Dad dinkuma .yanzu ya tsaneni .kaga ai kofadamin baiyiba zai kaika skul kai kawai ya fadawa .
Bilal inaso kayi karatu sosai kazama jarimin namiji amma banso kayi nisa dani ko kadan ta karashe tana zubarda kwalla ????
Shiru yai yama rasa me zaice mata amma dik jikinsa yai sanyi ganin taki daina kukan yasa yace momy nafasa zuwa kara incigaba da katartuna a nan tunda hankalinki baiso . mikewa yai yana shirin fita .ta ruko shi tace ina zakaje Bilal
Momy zanje wajan Dad infada masa na fasa zuwa school din yabarni anan kawai
A a Bilal .karka fadamasa .kaje Allah yabada SAA ya tsareka sharrin makiya
Rungumeta yayi yashiga kuka. Sosai don harya fara. Jin kewarta .
Sundade suna kukansu sannan .ta tashi ta tayashi suka karasa hada Kayan nashi .
Sai wajan karfe daya
Take ta kwanta tana sakar zuci .da bakin cikin irin sauyin data samu ga Alh.
Karfe .tara na safe Alh.yabawa Bilal kudade masu yawa .ya hadashi da direba yakaishi kasuwa dik abinda yake bukata yasiya na dangi sutura da takalma .Kayan gayu dai irin nasamari
.basu dawo gidaba sai yamma lis sabida saida yaje dikka gidajan friend dinshi yamusu sallama .har gidan shugaban makarantarsu yaje .da sauran gidajan daya sani na malaman su
Dama tun safe Dad yaiwa shugaban school din nasu waya yafada .komai . sosai yaji ba dadi .amma dake kauwace .saiyai mai fatan Alkairi
Ko minti goma baiyi dashiga dakinsaba aka kira magriba don haka .da sauri ya watsa ruwa yai alwala yatafi masallaci
Tare suka shigo da Dad. Sukaci Abinci. Sunata hira yanamai nasiha akan yayi riko da addininsa indai yarike addininsa to yafi karfin shedan da dikkan sharrin me sharri .
Ahaka sukaje ishai suka dawo Dad yace jeka kwanta son naga ka gaji .gashi gobe 7 jirginnamu zai daga .
Dakin momy yashigq sunata hira ta bankwana .har sha daya sannan .tace yaje yakwanta.
Shikuwa Alh bangaransu baby yayi a parlour yasamesu suna sanaar tasu ta game .mamynsu kuwa tana duba jarida .tsakiyansu ya zauna .sunata hira .yamikawa mamy calk na banki .yace dik abinda ya kama kuyi kafin indawo .sati daya zanyi insha Allah .