BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Baby da Islam meye tsarabanku hada baki sukai Dad ina zakaje ?
Zanje inkai yayanku Bilal .mkrnta a India.
Dajin abinda Dad yace baby ko kuma magana bataiba don ta tsaneshi.matuka
Itakuwa Islam da murnarta tace Dad kasiyomana irin Kayan da yan India suke rawa dashi.
Dariya sukasa shida mamy .yace to shikenan Islam zaa siyo muku.
????????????
[11/13, 10:52 AM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATED????
INA SONKU INA KAUNARKU .
MASOYAN BABY KHAUSAR
ALLAH YABAR KAUNA❤
4⃣4⃣
Tunda Garin Allah ya waye Bilal da momynsa suke kukan Rabuwa har sanda dad yagama shiryawa yafito ko kallon hjy baiyiba sabida Tunda Ta dawo kala bata shiga tsakaninshi da itaba rungumo Bilal yayi jikinsa Yace be A man mana my son Neman ilmi zakaje dole ka jajirce kazama namijin duniya karkasa tunanin komai aranka banda na karatunka maza wuce muje karmu makara
Tunda Suka shiga jirgi Dad yakemai nasiha akan yarike karatunsa yarike addininsa to Dad kawai yake fadi
Samiola shine me mkrntr su Bilal din shi yai musu masauki cikin girmamawa
Komai daya kama anyimai anbashi daki acikin hostel An bashi uniform Da dikkan material na karatu .
Saida Dad ya ga komai ya daidaita har Bilal yafara daukan darasi sannan yai shiri yayo gida .
bangaran su baby kuwa komai yana tafiyar mata dai dai don kuwa Yanzu sun koma school itada Islam suke tafiya dikda tafi Islam da aji daya
Mamy ta dauko musu me kula dasu kama daga yimusu wanka da shiryasu hadamusu abincin da zasu tafi dashi school Shiryasu zuwa islamiyya yi musu tsifan gashi kai dik dai wani Abu da ya kama aiwa Yaro shine aikin bintu bazawara ce me tsafta da addini
dakin da akasa sauketa yana jikin nasu baby don haka basu da damuwa
Mamy ta koma bakin aikinta don dama hutun aure ta dauka yanzu kuwa ta koma
Sun sami nutsuwa sosai baby batada wata damuwa yanda mamy bata taba nuna mata wani banbanci tsakaninta da Islam shi yafi komai yimata dadi .
Ranar da Dad ya dawo sunsha murna sabida yacikosu da tarin tsaraba .
Kayan wasan da yai musu tsarabanshi ba magana haka aka kara cika musu filin wasansu da manyan jiragai ga dokuna da giwaye dik wani abin wasa daxai birgeka an shirya musu shi a filin wasansu .
Dik ranar Alhamis da jummaa a kusan nan suke yini Daga sinbaro school karfe daya nan zasuje siyita Abu daya sai dai in lokacin sallar laasar yai su shigo suyi sallah su koma
Ranar asabar da lahadi kuwa ba dama don tun karfe bakwai ake kaisu tahfeez .sai sha biyu zasu dawo
wanka da cin abinci sannan su Dan huta karfe biyu amaidasu islamiyyan sai kuma karfe shida
Rayuwa me dadi da inganci akeyi agunsu Baby kai kana ganin Baby bai zama lalle Kayi saurin ganetaba sabida ta kara wani kyau Yarinya abin shaawa da birgewa ga tsafta da aka kafa mata jikinta dashi wata nutsuwa ta ratsa ta .
Kawance su da Aysha sai karuw yake kamar ba na yara ba
Don yanzu har kaisu gidan su Aysha akeyi itama ana kawota gidansu
Acan kasar India kuwa Bilal ya dage da karatunsa don dama shi Indai a fagen karatu ne ba dama akwai kwakwalwa don haka yakejin dadin komai koda yaushe suna waya da Dad da momynsa don haka hanlalinsa a kwance yake lakadan
Hjy kuwa yanzu ba laifi sun daidaita da Alh. Amma fa. Bawani kamar daba don haryanzu yanajin bakin ciki inya tuna da irin illar data musu shida Baby
????????????????????????
6/10/2017
[11/13, 11:02 AM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????
~Na~
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
FATIMA BINTU FATIMA SAI WATA RANA, SO MAFARKI NE DABA TABBAS BA ????????????
Wannan page? naki ne
sweet Ummy y Fatima y Abdullahi
4⃣5⃣
Haka rayuwa. take garawa yau da gobe bata bar komaiba.
Yau ga Baby Yan matan mamy ana j s s.one .yayinda Islam take shekaran karshe a Primary
Ba abinda za'a cewa mami sai Allah ya saka da alkairi domin kuwa ta zama uwa ta gari ga ya'yanta
Mami ja’jirtacciyar uwa ce ga yaranta duk da kasancewar samun waje da boko tayi a gidan hakan bai hana magartacciyar tarbiyya shimfid’uwa a gunsu ba, Abin sha’awa ma sai kaga yanda yaran suke zuba karatun alkur’ani, hadisi da sauran littattafan addini .
Uwa uba sallah Mami bata sassauta musu akan maganar Ibada don haka daga sunji an kira sallah zasu yi maza suje suyi ta
Ga nutsuwa Agunsu komai da akeson d’an musulmi dashi yaran nan sun samu sun mallake shi
Rayuwa tana ta tafiya rayuwa tana kara dad’i ga wasu yayin da take matsewa ga wasu
To hakama hjy Amina rayuwa taimata kunci bata jin dad’in komai don Alh ya hana kowace kawarta shigowa gidan sa kuma itama yai mata katanga da gidan kowa tunda dai batada kowa agarin.
Wannan ne yasa duk ta kara tsangwamewa in kaga fara’ar ta to suna waya da Bilal ne
Wanda shi zuwa yanzu karatun sa yai nisa don har ya kammala secondary d’in suna Hutu kuma Dad yaje ana mai duk wani shirye-shiryen Shiga university d’in
dan gida kacokam dad ya siyami shi shida wani abokin sa d’an nan kano ne shima kuma tun daga J s s .one ya fara tunda suka had’u a can suka had’e Kansu tamkar yan’uwan jini to don haka
da Dad ya siya mai gidan plart ne mai parlour da d’akuna biyu yace su zauna shida sageer d’in
A haka akaci gaba da garawa su baby ana s s .2, Islam ana 1 kuma a lokacin sunyi saukar alkur'ani mai girma .
Sun zama yan mata na gani akara kalla gakyau ga iya wanka ga nutsuwa kansu a had’e yake
kullum ka gansu a shiga iri d’aya zaka gansu don yanzu ko d’an kunne d’aya baisawa sai irin wanda d’aya ya saka .
don haka suke birge mutane da dama kowa sha’awa suke bashi sabida yanda kansu yake a had’e
A yanayin da ake na damuna. ne . yau tun karfe d'aya ake tsuga ruwan sama
Su Baby suna d’akin su suna ta hirar su har bacci ya daukesu .
Ba’a dauke ruwanba sai karfe hud’u saura kwata
Islam ce tai juyi taga hud'u tayi mikewa tayi ta shiga toilet tai wanka tare da dauro alwala, tana fitowa ta tashi baby .
dukkan su bayan sun gama shiryawa suka fito parlour islam ta shiga shirya musu abinci .
Suna zaune a dining suna cin abincin suna d’an taba hira Mami ta sauko daga up stairs. Tazo .ta zauna tana murmishi tace “um sannu yan Hutu sai yanzu kuka tashi daga baccin?”.
Dariya suka yi baby tace "Mami ruwa fa aka yi, kinga baccin yafi dad'i".
"Hhhhhmmmm hakane kam"
Hira sukeyi a nutse irin ta wayanda suka waye da ilmi
Islam ce ta dubi Baby tace "sis zo mu d'an motsa jiki mana" .
"Ok muje Mu saka kayan sport" cewar baby
Baby tasa red color yayinda islam tasa blue riga da dogon wando ne sai hula me kama dana sanyi
Sai fararan combus.
Kai whl sunyi kyau kallo daya ba zai isheka ba matukar kai musu shi
Layuza ????
????????????????????????
[11/13, 11:04 AM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Na
LAYUZA KABIR ADAM
DEDICATED TO U ALL SISTERS
1-ZAINAB KABIR
2-MARYAM KABIR
3-AISHA KABIR
4-ZAKIYYA KABIR
AND LITTLE AISHA SAHLA ❤
4⃣6⃣
Fitowa suka yi da d’an gudu gudu hannun su rike da juna haka sukaita zagaye filin sannan Suka zube kan kujeran dake kasan wata bishiyan fruit .
Sosai yake kara leko kansa daga jikin window d’in dayake a tsaye kasancewar a saman bene yake shi ya bashi damar kallon su sosai
“to wayannan su waye suka zo gidanna su haka yan’mata kyawawa dasu kilama yan biyu ne, don gasu kusan Kansu daya”.
Wannan itace maganar da Bilal yake ta mai-mai tawa a ransa
Saida suka huta sannan suka tashi Suka shiga yin snooker sosai suke kyalkyala dariya Wa junansu sabida yanda Kowanne yake yi da iya karfinsa nason cinye d'an uwansa
Islam ce ta fara doke baby aikuwa nan da nan itama ta kara kaimi akaro na biyu tana shirin kara zirawa baby ta saki sandanta akan na islam d'in yar bol din tayi gefe aikuwa baby tace me zatai ba dariya ba ganin rainin hankali ne abin yasa islam ta kaimata cafka aikuwa ta zura da gudun gaske itama ta bita wai saita rukota ya bigi kafadarta
Gajiya baby tayi da gudun don Harsin shige can cikin gidan Kusan sashin su Hjy Amina jikin wani window baby ta jingina tana fadin
" I'm sorry sweet sis na tuba ki barni haka da gudun nan"????
Dariya islam d’in tayi “ok sannu sarkin tsoro na hakura mu wuce ciki”.
Bakin fanfon dake gefan gun Baby taje
Hulan kanta ta cire ta fara watsa ruwa a fuskar ta tare da girgiza kanta gashin ta duka ya baje a a gadon bayan ta da gefen fuskar ta
Sannan Islam ma ta wanke fuskar ta suka juya zuwa cikin gidan
Duk abinda suke yi akan idon Bilal wani irin yanayi yake ji a jikinsa da ransa don yanzu hakama daya koma kan gado ya kwanta komai dawo mishi yake tindaga fitowar su da d'an gudu gudun nan harzuwa sanda suke koma wa fart d'insu
Ammafa yaga d'ayar data danfi tsayi da siranta kamar baby khausar
"Kai A'A ba ita bace yaushe baby zatai wannan girman da kyau haka"
Yana wannan tunanin yaji anfara kiran sallan magriba
Jiki a mace ya mike ya shige toilet don dauro Alwala
Yana zaune a masallaci har akayi sallan isha'i sannan ya shigo gida shigowanshi yai dai dai da shigowar motan Dad don haka yaja yatsaya har motan tai farking da sassarfarsa ya karasa jikin motan shikuma shima Dad da sauri yafito suka rungume juna cikin tsananin farin ciki
"Ur welcm son ka zo tunjiya katarar bana gida ko, ina can duk hankali na yana kan ka kawai dan dai meeting dinnan yanada matukar mahimmanci ne. Dana zauna Na tareka my son"
Rike hannunsa yayi suka shiga cikin gida dukkan su fuskokin su d’auke da fara’a
Suna shiga part d'in sa yace "my son bari inyi wanka infito mu zauna yau ai a bangarena zaka kwana".
duka 15 minuts ya fito yasa prayer mat ya tada sallan magriba da isha'i dake kansa
zuwa lokacin mami harta cika mai dining t , da kayan abinci don itace da girki sanda ya shigo sunji shigowar motansa to duk suna sallah bayan Ta idar kuma ta shigo ya shiga wanka sai Bilal ta gani zaune a parlour suka gaisa dukda batasan yazo garinba anan ta tsinceshi
Ta juya zuwa part d'inta tunda yashiga wanka sukaci karo dasu Islam sun taho mai sannu da zuwa tace "ya shiga wanka Ku koma zuwa anjima "
"Mami amma dad yasan muna son ganin sa amma shine kafin mu idar da salla muzo harya shiga wanka".
Cewar Baby sanda take zama kan kujeran parlourn su .
Murmushi Mami tayi tace "to baby meye abin bata rai Dad dinku gajiya ya d'auko yanzu zai fito Ku gaisa".
Layuz ce
????????????????
[11/13, 1:01 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Na
LAYUZA KABIR ADAM
GODIYA NAKE MASOYA NA,
MAKIYA KUWA INA ROKAR MUKU SHIRIYAR ALLAH????
4⃣7⃣
Mami d’akin ta ta shiga ta kara fesa turare ta fito ta koma part d’in Dad d’in
Kai tsaye d’akin tashiga ta same shi tsaye yana balle Link’s d’in hannun jallabiyar dake jikinshi Yar asalin baharain
Ja tayi ta tsaya jikin kofar d'akin ta hard'e hannayan ta a kirji ta kafeshi da wani kallo na kayimin lefi
Mirmishi yayi yana had'e hannayan sa waje d'aya alamar ban hakuri ????
"Ayi hakuri madam nasan ban kyautaba, na dawo nashiga wanka banjira kinzo kin taimakamin ba
Uziri namiki nasan kila sallah kike tunda naga daga ke har yan matan naki ba Wanda yazo tarana a bakin mota, amin afuwa ranki ya dade ???? “
“sarautar mata Halima hali dubu cikinsu babu na yarwa, amarya gidan A A mama ga emmata baby da Islam”
Batasan sanda dariya tazo mata ba najin dad’in kirarin nasa Wanda yasaba yimata duk sanda yaga tana fishi
Rungumeshi tayi. Tace "sannu da zuwa yallabai Andawo lfy ya gajiyan hanya"
“Ga gajiya kam sadiya tari guda, sai kinmin tausa” ya fad’a yana leka Idonta
Bata tanka mishi ba ganin sun fito parlour ga Bilal
Mikawa Bilal hannu yai alamar yazo suci Abinci da sauri Bilal yabi bayansu suka zauna a kujerun dining din mami ta shiryawa kowa nashi ta mikawa bilal a gabanshi yaja yafara ci
Hakama Dad yanaci suna zuba Hira da santi harsuka gama
Parlour suka dawo suka zauna kasancewar mami wayayyiyar mace yasa tasaki jiki sukai ta hira da Nilal yana bata lbrn zaman India yanda suke karatu dadai yanda yake rayuwa a can
Hhhhmmmm tsakanin d’a da mahaifi sai Allah duk hiran da ake tafkawa Dad hankalinsa naga baby Me yahana ta zuwa gaishe shi har yanzu yau kwana biyu Kenan be gantaba nan da nan yadau wayansa yakira ta ,Islam CE ta daga “hello Dad”
“Islam ya akai naga bukuzo wajena ba tun d’azu?”