BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

"Dad munzo kashiga wanka amma yanzu zamu shigo"
Suna shigowa da gudu baby taje ta fad’a jikinsa tana shagwaba Islam gefan damanshi ta zauna da riko hannunshi tace “Dad sannu da zuwa ya hanya”
“Alhamdulillah isy baby”
Dago kan baby yayi da take jikin ahi a lafe yace “to baby yau kuma rigimarce ta motsa?”
Kallan Mami yayi yace “madam keda yarinyarki yau rigima kukeji”
Dariya suka sa dikansu har baby tace
"Dad ai Kaine daka shigo baka nememu ba ka taho nan kuma mukazo ka shiga wanka kasan kuma muna kewanka"
"To its okey Dad yayi lefi amai afuwa , bukuga yayanku Bilal bane yazo Hutu ko kun gaisa"
Sai asannan suka kula da Bilal dake zaune ya afka kogin tunani namai yahana momynsa Zuwa gun dad tun shigowarsa.ko dai haryanzu bata daidaita da Dad Bane
Yana wannan tunanin kuma bai gamaba su baby suka shigo nan yakara lumtsimawa a wani sabon tunanin kuma ya tabbabtar dai wannan siririyar Baby ce dayar kuma Yar Miami ce data zo da ita gidan
Layuza
????????????????????????????
[11/13, 1:35 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
Na
LAYUZA KABIR ADAM
BANI DA BAKIN YI MUKU GODIYA
MY AUNTY’S
1- AMA ALHJ KABIRU
2- NASMATU (Yar’mutan arkilla)
Wannan shafin nakune don kaunarku gareni ????????????
4⃣8⃣
A tare suka kai kallonsu inda Bilal ke zaune Wanda tun farkon shigowarsu basu kula dashi a gunba.
Islam da fara'arta tace "ya Bilal sannu da dawowa ya hanya".
"Yawwa sannu da gida Na sameku lafiya”.
“Lfy qlau Alhamdulillah bro”.
Kasancewar islam me saurin sabo yasa suka shiga hira da Bilal
Amma Baby kaida baka wurin inka kalleshi to itama ta kalleshi,
Don tunda tami shi kallo d’aya ta d’auke kanta ta d’auki wayan dad tashiga game da ita.
Kowa a gurin ya lura da halin ko inkula da tayiwa Bilal amma ba Wanda ya tanka mata
Sai da agogon dakin ya buga alarm na karfe goma sannan baby ta ajiyewa Dad wayansa Tamike tana fad'in
“Dad zanje in kwanta, good night nd sweet dreams”.
“To baby Allah ya tashemu lfy”.
Juyawa tayi ta kalli Mami tace "Mamina zanje in kwanta mu tashi lfy"
"To Baby Allah ya tashe mu lfy kar amanta da addu'a"
Ko kallon islam batayi ba tasa kai ta fice
Bata jima da shiga d'akinba saiga Islam ta shigo tana fadin "sis shine kika Taho ko magana babu ko "
Ko kallon ta bata yiba ta shige toilet tai wanka da brush sannan ta d’aura Alwalan kwanciya bacci , daure da towel ta fito kai tsaye ta nufi gaban mirror tashafa mai da Dan body spray tasa night gown ta haye gado.
Duk abinda take bata kalli inda Islam take ba, itama bata tanka mata ba saida tagama shirin kwanciyarta sannan ta hayo bed d’in tana fad’in “sweety wai laifin me nayi ne kike wani shareni haba mana tun d’azu sai wani kaudamin kai kike”
"Niba sweetynki bace ki matsa ma a kusa dani dalla"
Da mamaki Islam ta kalleta "sis wai meye hakanne ko dai kinyi gamo ne A parlourn Dad" ta fad'a tana gimtse dariyar da ke ko'karin subuce mata.
“Eh gamo nayi, gamo da mugu ba, azzalumi Mara tausayin marainiya
Amma shine sabida bakya kishi na baki damu da damuwa ta ba kina ganin ko kallonsa banyiba Amma wai ke uwar azakwai harda wani takarkarewa kina zumabai hira
Wlh kinban haushi”
Mirmirishi ☺ tayi tace "haba sis yanzu akan wannan kika d'auki fishi haka? kinga ai umarnin Dad nabi shiyace muyi masa sannu da zuwa kuma kinga bazaiji dadiba ke bikimai magana ba ni banmaiba ai ba dadi".
“To dama ance miki inaso yaji dad’i ne? mutumin da bai son jin dad’ina shida momynsa suka zalinci maraicina suka rabani da mahaifana,nida gidan ubana amma saida nayi rayuwar sama da shekaru uku cikin tsananin azaba ,ina fad’a ina kara fad’a bazan yafewa mutanan ba har abada sun cutar da ni ????”.
"Islam bazan manta zaluncin da akamin ba"
Ruko Hanna yenta Islam tayii tana fad'in "kiyi hakuri sweety na ki zama me yafiya Allah yana son bayin sa masu yafiya "
Zare hannun ta tayi cikin nata ta juya tana rufe ido har yanzu inta tuno rayuwar da tayi agun momyn Bilal da zalincin da Bilal yai mata sai taji kuka na zuwar mata na bakin ciki da tausayin kanta.
Ta Dade bata yi bacciba
Tana sakawa da kuncewa kafin daga baya bacci me nauyi ya d’auke ta.
Takuce
layuza kabir Adam ????????
[11/13, 2:16 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
NA
LAYUZA KABIR ADAM
INA YABA MUKU INA KARA YABA MUKU
???? ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
SANNUNKU DA KOKARI NA YABA DA KARARKU ????
ALLAH YA KARA BASIRA DA HADIN KAI
4⃣9⃣
Da safe da misalin karfe goma na safe ya tara iyalan gidan a parlourn sa bayan dan tsokana da barkwanci daya saba yiwa yaran sa ya koma seriously yai gyaran murya da fara magana
“To muna godiya ga Allah subhanahu wata’ala daya dawo mana da Bilal gida lfy bayan tafiyarshi na tsawon shekaru ‘ inda yacika karatunsa Na secondary shekara uku sannan ya Dora da degree dinsa shekara hudu yai aiki dasu na shekara biyu dika inmun hada bilal yayi tsawon shekara Tara baya tare damu yana can yana yakar jahilci ,kuma Alhamdulillah. Kwalliya ta biya kudin sabulul tunda gashi ya fito a cikakken engineer a harkar hada dikan wani Abu daya shafi electronic “
Yaja numfashi sannan yaci gaba
“Bilal lokacin daka bar gida kabar baby tana Yar shekara bakwai yanzu ga ta da shekaru sha shida kuma tana s,s , two tana shirin shiga 3 nanda wata biyu insha Allah ,
Sai kuma islam wadda ka tafi baka santaba don bayan tafiyarka dayan kwanaki na daukota ta dawo gidan wadda yace ga ita sadiya ,ina fatan zaku hade kanku Ku zama abin alfahari dikda bawai dogon zama zaka karayi damuba zaka koma donyin masters dinka , amma dik da haka inason ka dauki islam tamkar yanda ka dau Baby , ina fatan ka fahimceni “
Jinjina kai yai yana fadin yes Dad insha Allah zamu kasance 'tsintsiya madaurinta daya '
Kallonsu islam yai yana fadin "Ku kuma ga Dan uwanku nan yayanku ina fatan Ku zama masu biyayya gareshi kuma hade kanku kunji yaran albarka .
Ya kara juyo da kallonsa gasu momy da mami yace "to Ku cikinku akwai me magana ?"
Mami tace a a Alh. Nikam ba magana aguna
To kefa yafada yana kallon momyn Bilal
“Nidai gaskiya maganata Alh, bansan kara tafiyannan da Bilal zaiyi inma master’s dinne kara yayi anan Nigeria ,don ina bukatar zamansa kusa dani wannan zaman kadaicin ya isheni haka”
Da zafi Dad ya. Dubeta zai fara mata fada amma ganin yanayin da fuskanta ya nuna matuka tana cikin damuwa kawai saiyaji tadan bashi tausayi don haka ya kauda kai yana fadin kibar wannan maganar tukum zamu tattauna baby Bilal kuje dik na sallameku amma ke Baby zauna zanyi magana dake ,
Sai da kowa ya fice sannan Dad ya kalli baby yace dawo nan baby zoki zauna kusa dani
Mikewa tai tsam ta zauna ku sa dashi , ruko hannunta yai yace “baby ke yarinyace me hankali da biyayya nasani sarai sadiya tayi kokari wajan baku tarbiyya ,kinsan addini gwargwadon iko kisan da yawa daga littattfan addini babu duhun jahilci atare dake kinsan illar riko agun musulmi to meyasa kika rike Dan uwanki a zuciyarki har tsawon wannan shekarun,na kula da ke tun jiya danace kumai murnan dawowa gida ko kallonsa bikiba ,meyasa baby ?kiyi hakuri kizama Yarinya me yafiya ga dik Wanda ya cuceki sai Allah ya miki sakayya mafi alkairi kinji baby na “
Hawaye ne sosai ke zuba a idonta yasa hannu yashiga share mata tare da kara mata nasiha me kashe jiki,
Ta Dade gun dad saida yaga zuciyarta tai sanyi sannan ya ce taje,
Tana shigowa parlournsu taga mami nashirin fita zataje gidansu ana suna ,cikin miryan shagwabanta tace mami wai harkin fito tun yanzu zaki tafi sunan don Allah ?
Mirnishi mami tai tace “wai baby ke a duniya bakyason ki kyalla kiga zani unguwa saikace inna zauna nono zanbaki ,
Bibbiga kafa tashigayi Mami ni wlh inba gun aikiba banson ganin ba kya gida sai inji gidan fayau
To shikenan it’s OK bazan dadeba yanzu zanje indawo
To mami Allah ya dawo dake lfy .
Takuce
Layuza kabir Adam
[11/13, 2:17 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
NA
LAYUZA KABIR ADAM
MASOYA LITTAFIN BABY KHAUSAR SAKONKU YAZO GARENI NA CEWA IN RINKA MUKU TYPING DA YAWA ,KUYI HAKURI ABUBUWANNE DA YAWA AMMA INSHA ALLAH ZAN KARA ????
NA GODE DA ADDUARKU GARENI ALLAH YABAR KAUNA ❤
5⃣0⃣
Tun fitar mami baby ta haye kan three seater na parlour ta kwanta don jin jikinta take ba karfi ga cikinta yana mata Dan ciwo ciwo can saita ja tsaki ta runtse ido.
Islam dake gefanta a zaune tana research a laptop dinta ce ta juyo tana kallonta jin tanata Jan tsaki ,
"Meke faruwa ne sis "
Dan runtse ido tayi tare da cije lebe tace "wlh islam banjin dadi ne cikina kemin ciwo tun dazu amma da kadan kadan kemin, saidai kuma yanzu yadan matsamin ,
Sosai islam ta dawo da hankalinta kan baby tana fadin
“amma kinsan bakida lfy kika bari mami ta fita baki fada mata ba sis “?
Tadan numfasa tace "to yanzu ya zamuyi sis "
Itadai baby bata kara magana ba tacigaba da juyi tana runtse ido ,
Can tace
“Ban ruwa me sanyi insha “
Tunda tasha ruwan bacci me nauyi ya dauketa
Har misalin karfe uku tana bacci ,cikin baccin taji ciwo ya murdeta ta farka da tsananinsa ,tun tana salati harta fara kuka tana kiran islam
Daga cikin daki yajiyo muryan babyn aikuwa ta gito da gudu tana zuwa ta isketa kwance kan cafet ta fado daga kujeran ,
” Innalillahi wa inna ilaihi rajiun “
Shine abinda Islam tace lokacin dataga idon baby ya kakkafe da gudu tai waje tana kiran ataimaka mata
Harta kai babban gate bataga kowa kara takuma sawa tana fadin “baba me gadi Ku taimakamin baby zata mutu “,
Atare suka fito da direba suna tanbayarta meya faru nan ta fada musu baby tana suma
Ai kuwa da sauri direba yayi farking space don dauko mota
Itakuma ta juyo da gudu zuwa cikin gida ,kaf sukai karo da Bilal ganin tana kuka a rikice yafara tanbayarta meya faru