BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Watan Halima goma daidai agidan ta haifo yarta ta fari ansha murna. Ran suna taci sunan kakarta Hafsatu suna kiranta Ameera
Bayan shekara daya da rabi ta kara haifo yarta mace akasa mata suna juwairiyya
Izuwa wannan lokacin arzikin Alh Abubakar ya kara bunkasa don yasami karin matsayi gun aiki kuma yanada gidan gonarsa daya zuba maaikata suke kula dashi
Lokacin ne kuma. Aliyu ya gama degree dinsa akan sanin maa’danan kasa
don haka yana gamawa Alh Abubakar yai cuku cuku yasamarmishi aiki kuma ya hadashi aure da. Kanwar matarsa.sunanta Amina
Agidanshi daya gina a unguwar. Tarauni yabawa dan uwannashi kyauta. Ya. Zauna. Da matarshi
.
Zama ake naso da kauna tsakanin Amina Da. Aliyu. Yana. Bawa. Matarshi. Kulawa sosai da. Sosai. Kamar ba. Auran. Hadi ba. To. Dayake. Itama. Aminan. Tana dahankali. Sai Abinnasu. Yai. Dai.
Tsawan. Shekara. Daya da. Auransu. Amma. Allah. Bai. Nufesu. Da. Haihuwaba. .awannan. Lokacinne. Kuma Kawu Bala. Ya rasu. Sunshiga. Tashin. Hankali. Domin. Kuwa. Basu. Da. Kowq sai shi ne kadai wanda. Ya. Ragemusu. Cikin. Danginsu. Kwanansa. Biyar. Da. Rasuwa. Halima. Ta. Kara haihuwa. Da. Na. Uku. Akasa masa. Sunan. Kawu. Wato. Bashir
Yau da. Gobe yakai tsawan shekararsu biyar da Aure ko batan wata Amina bata taba. Yiba
Tunbasa fito da. Damuwarsu. Har ya kai kowa. Ya. Gane halin. Kuncin da. Suke ciki. Kullum. Cikin. Ganin. Likita. Suke amma shiru.
Ganin irin damuwar dasuka shiga yasa Alh Abubakar yakira su. Yai musu nasiha kuma yace ga kyautar Bilal yabasu dan da halima. Ta kara Haifa yanzu
Da zummar. Ana yayeshi. Su. Dauka.
Murna. Sosai sukai tare da godiya …
????????????????????????
8/9/2017
[10/2, 11:34 PM] Spouse 2: *_????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
(ja’oji)
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah tsira da Aminci su kara tabbata ga annabirrahma Muhammad rasulillah
0⃣5⃣
Bayan sunyi wannan maganar da kwana. Biyu Alh Abubakar. Yai tafiya duba abokinsa a Kaduna ahanyarsu ta dawowa suka tafka mummunan. Hadari ko shurawa basuyiba shida direbansa
Innalillahi wa inna ilaihirajiun
Mutuwa me yankan kauna hakika anwa wayannan mutane gagarumin rashi wanda bazaa maida gurbinsaba
Sunyi kuka sunyi salatin karma Alh Aliyu ji yaje kamar kwakwalwarshi bata aiki haka yake zama kamar karamin. Yaro yaita kuka ana rarrashinsa
Haka sukaita karbar gaisuwa har kwana bakwai. Kowa ya. Watse .
Adaran ranar ne halima ta kira. Alh Aliyu da kanwarta Amina .tace musu ga Bilal nan su tafi da abinsu ta yayeshi tunda yana cin. Abicinsa kuma. Yana wayonsa ko ina shekararsa guda
Alh Aliyu ya rungume Bilal yana kuka. Yace Allah yajikan dan uwana amma inason dikkanku. Ku. Dawo gidana mu zauna kinga zama ba namiji agida hadari ne
Girgizakai tayi. Tace ba. Komai Aliyu. Karka damu zamu. Zauna anan nida sauran. Yaran. Insha. Allah ba wata matsala .
Ba asan ranshiba ya hakura .
Haka. Aka. Hada musu. Dikkan. Kayan. Bilal suka. Tafi. Dashi
Wannan. Shine farkon zaman. Bilal. Hanun kanin. Mahaifinshi. Da. Kanwar mahaifiyarshi cikin so da kauna. Bilal yake zaune agunsu yana kiran Alh Aliyu Dad Amina kuma. Da mom .
Tunda ga lokacin suka cire damuwar. Haihuwa aransu
Bayan shekara da rasuwar Alh Abubakar hjy Halima ta daura aure wanda Babban Aminin Mijinta ya aureta kuma ya rike yayanta cikin aminci .suke zaune da matarshi Allah ya hada kawunansu
Bilal yarone kyakykyawan gaske. Ga koshin lfy dayake dashi. Dan gata sosai agun iyayennasa. Ko. Kusa. Bass son. Yataba. Bilal. Wani irin so. Sukemishi tamkar. Daga jikinsu. Ya. Fito. Haka shima. Bai San. Kowaba saisu . ahak Bilal. Yakai shekara. Hudu. Aka kaishi. Mkrnta
Wanda. Zuwa. Wannan. Lokacin Arzikin. Alh Aliyu. Baa magana. Ya Gina tamfatsetsan gidansa. Anan Sakkoto road .wancan tsohon Nasa kuma yasaka mlm Khalil wani malaminsa dayake mishi taimako. Kuma yake taimaka mishi wajan harkar addini ko irinsu fitar da zakka dik shine akan harkar
Haka rayuwa take gudu yanzu bilal shekararsa bakwai . yana zuwa makarantar boko inya dawo yatafi islamiyya . yaro ne wayo da basira ga kokari a mkrnta hakan yasa yake dashiga ran mutane
Yau kwanansu uku da dawowa daga aikin hajji Alh Aliyu yai wani mafarki dayasashi ckn tunani sosai mafarkin yatsaya mai arai
Don haka bayan yai wanka yashirya. Yatafi gidan mlm Khalil ya bashi labarin mafarkin da yayi .tsawon lokaci. Mlm bai magana ba daga. Baya. Yatashi yai alwala yai sallah rakaa biyu. Yadau tsawan lokaci yana wuridi sannan yagano abinda yake son ganowa nan yai adduoinsa yashafa Jiyowa yai ga Alh Aliyu yace Lalle Alh akwai wani alheri dayake tunkaro rayuwarka kuma alherin yananan cikin gidanka acikin alherin kuma harda
Samun karuwa na haihuwa
Sosai Alh yamaida hankalinsa ga mlm
Sannan ya nisa yaci gaba Acikin gidanka Akwai maiyiwa matarka hidima .to wannan
Itace Alherinka kwan haihuwarka yana jikinta don haka kaje ka nemi auranta In Allah. Yanufa ita zata fiddomaka da kwanka dunyi …
????????????????????????????
8/9/2017
[10/2, 11:34 PM] Spouse 2: _????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
Kina raina komai tsawon lokacimy sweet
Friend Fatima
y.Abdullahi _ummy
0⃣6⃣
Don haka bayan yai wanka yashirya yatafi gidan Mlm Khalil ya bashi labarin mafarkin da yayi . tsawon lokacin Mlm bai maganaba daga baya yatashi yai alwala yai sallah rakaa biyu yadau tsawon lokaci yana wuridi sannan ya gano abinda yakeson ganowa .
Dubansa yai yace Alh. Hakika haske ya bayyana cikin rayuwarka kuma yana nan yana tun karoka tsawon lokaci yana cikin gidanka sai yanzu Allah yakeson bayyanashi
Alh Acikin gidanka akwai. Meyiwa. Matarka hidima. Lokaci me. Tsaho. Wannan. Mata itace mahadar. Arzikinka ta hanyar haihuwa
Kaje ka nemi. Auranta. Insha Allah Alkairin na gareta
Cikin wani yanayi ya dubi Mlm kamar be gane bayaninba .
Ganin hakan yasa
Yagyara Zama tare damai bayanin dalla dallah .
*tofa dare ya tsala yayin da gari yayi shiru. Alh.na kwance saman makeken. Gadonsa. Yanata juyi dik abin. Duniya ya isheahi yarasa. Meke me dadi ga koshi ga kwanan yunwa.
Shin da wane ido zai. Kalli hajiya yace mata zai auri. Me aikinta kai. Abin da nauyi
To kuma hakurarsa akan lamarin. Fa yana nuna cewa dik sonshi da. Haihuwa fa. Kenan sai dai yaga anayi matukar bai auri wannan me aikinba
To ya Kenan
Haka ya kwana yana saka da. Warwara har asuba. Bayan idar da sallarshine ya zauna cikin masallacin yaita kaiwa Allah kukansa tare da Neman zabinsa .
????????????????????????
14/9/2017
[10/2, 11:38 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
kullum muna tare tundaga o level har high institutions _Allah yabar kauna
Najaatu_SaeedYusuf _Zainab muhd umar
0⃣7⃣
Tofa abu ya damu Alh gashi bashi da abokin shawara. Awannan maganar. Don haka ya maida lamarinsa. Ga Allah. Koda. Yaushe cikin. Addua yake akan Allah yamai zabi na. Alkairi.
Ai kuwa cikin kwana biyu. Sai yakejin. Abin. Aransa don haka. Yakoma gun Mlm da maganar
Kai tsaye yacemishi. Yajewa hjy da batun. Kar yasa shakku aransa. .
Da dare bayan yagama dikkan shirinsa na kwanciya. Hjy na gefansa. Ya. Dubeta da kulawa yace.
Hjy tanbayarki. Nakesonyi. Sosai ta gyara. Zama da maida hankalinta kansa
Inajinka Alh tafada
Hjy cikin masu aikin gidannan wace hadiza
Mirmishi tai tana cewa ayya hadiza. Ai me tayani girkice. Alh akwaita da hankali da gudun zuciya uwa uba tsafta
Ai mutuniyar Adamawa ce bafulatana ce usul
Yan gudun hijira ce da yan hari suka kai musu farmaki cikin rigarsu suka tarwatsa. Su toshine fa kowa yai ta kansa ita tayo nan kano ta fada hannun matar dake kawo mana yan aiki to shine ta kawomin ita
Don lokacin da takawota gidannan ko Hausa bataji sosai
Yanzu aitakai shekara uku agiddan .lokacin datazo dai tacemin shekararta ashirin da biyu .don har anfara mata shirin biki .wannan tashin hankali ya samesu .
Saida takai nan sannan tai shiru don hjy irin matannan wanda magana bata musu wahala ga yawan faraa.
Kallonta yai tsaf sannan yace Allah sarki .kice batada ma iyaye Kenan tace eh dik sun rasu . amma Alh ince dai lfy kake wannan tanbayar yace. Eh lfy .kawai daman inason sanin ko wace ne dazu naganta shine nake tunani don bansantaba agidannan
Dariya tai batare data kawo komai arantaba tace to dama Alh kai sanin yan aikin gidannan kayi kullum suna bangaransu .
Bai kara cewa komaiba ya juya ya kwanta itamata ta kwanta .
Sosai yake tinanin akan hadiza da tarihinta da hjy ta bashi .don haka yaji ta kara Shiga zuciyarsa
Dik iya wani shiri dazaiyi yayi cikin sati biyu .ya hada Kayan lefe yakai gidan Mlm Wanda shi yakeson yazama waliyyin hadiza a auran
Sassafe yau yaiwa gidan hjy halima momyn bilal tsinke
Bayan sin gaisa .ya gyara zama .hjy dama wata ce nazo da ita me mahimmanci kuma ina rokon hadin hadin kanki akai
Jinjina kai tai tace fadi ko mene ne Aliyu kwarin gwiwarsa yace dama aure nakeson karawa shine nakeso ki kira Amina ki mata nasiha akan karta tashi tashi hankalinta . haba Aliyu mene don zakayi aure kuma shine wani abun damuwa ai karuwarmu ne gaba daya
A a hjy ai inda matsalar take shine me aikinta hadiza zan aura .
Dik da maganar ta bugeta amma saita dake .tace karka damu da dare in Allah yakaimu ka daukota kuzo tare .
Godiya yai sosai sannan yabaro gidan.