BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Itadai islam saidai taita bashi baki akan ya kwantar da hankalinsa zuwa Dan lokaci baby zata hakura tadaina mai abinda takeyi na shariya da kauda kai.
Itakuwa baby inma taga islam suna waya da bilal tsaki takeyi ta kauda kai.
Yauma suna zaune a cikin guarding suna lido wayan Islam yai ringing da murmishi ta daga tana fadin
“babban yaya shiru kuma kace yau zaka dawo”
Daga daya bangaran yai dariya yace
“Kanwata ganima nakusa gida tundazu jirginmu ya sauka dirbane baizo da wuriba amma gamu munkusa zuwa gida”
“OK to sannu da zuwa saikun karaso”
Baby ta dubeta tai tsaki Islam kuwa mirmishi kawai tai bata tankaba karan bude gate sukaji azatonsu dika motan su Bilal ne Amma sisukaga Nabeel ne dammm kirjin baby ya buga tarasa gane meke damunta akan Nabeel run zuwansu na farko gidansu shida yayansa take yawan tunaninshi ko kuma daga taji sunansa abakin ko Islam saitaji gabanta ya fadi ta rasa gane dalili.
Jin ana mata tafi a fuskanta ne yasa tai saurin dawowa daga tunanin data shiga, kur ya tsaya kallonta sannan yace “Y’ar baby tunanin me kike inata magana kin Lula”
Kauda kanta tai gefe tace “sannu da zuwa” ta hanyar kauda tanbayar da yai mata,
“Yawwa sannunki da tunani amma biki fadamin tunanin me kikeyiba”
"Nifa ba tunani nakeba to tunanin wama ni zanyi"
“A a mu bamu saniba saikin fada munji”
Islam ce tace "tofa kai kam ya nabeel ba zuwanka ba kaita damun mutane da tambayoyi"
Yana shirin yin magana wayanshi tai k’ara da sallama ya d’aga da muryanshi me dadin amo,
Atare suka d’ago suna kallanshi jin yanda yake magana cikin harshen larabci tamkar wani rikakken malamin bala rabe,
Yakai minti biyar yana wayan sannan yai sallama ya kashe,
Ganin irin kallon da sukemaine yasa yace yadai y’an mata, da Sauri baby ta kauda kanta gefe islam kuwa tace
"hhhhmmmm su ya Nabeel irin wannan larabci kamar malamin balarabe"
Dariya yai yace "ba wani balarabe kawai daburawa Mike"
“Wannan ya wuce daburawa”
Itace maganar data fito daga bakin baby batare data San ta fito ba don a zuciya tai maganar,
Shigowar motar su bilal gidanne yasa suka juya dikansu da sauri islam ta mike tana fadin oyoyo big broth
Juyo da kanshi yai yana kallon baby
“yace waye ya shigo?”
Batare da damuwa ba tace “ya Bilal ne”
Yace “yayanku?”
Um kawai tace
” meyasa danace dabura larabci nake Naji kince yafi karfin daburawa?”
Dan mirmishi tai me fito da asalin kyanta tace “ai naji abinne ba dama,inason na Iya larabci wlh”
Sosai ya kalleta yace “da gaske, inkuwa kinaso to zan rinka koya miki”
Da fara’arta tace “wlh da gaske inaso yaushe zaka rinka koyamin?”
“Dik sanda kike da time”
“to dik ran jumaa da yamma”
“Tom karki damu daga gobe zamu fara tunda gobe Friday ne”
Sosai yaga fara’a a fuskanta da jin dadi
Yace “kinga na tsaya agunku ko ciki banshiga mungaisa da mami ba,bari inje mu gaisa in wuce gida naga waccan ta tafi gun yayanta ta manta da bakonku”
Yafada yana shigewa cikin gidan
Nan yabar baby da fadawa dogon tunani akansa.
Takuce
Layuza kabir Adam ????
[11/13, 2:18 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
????????????????????????????????????
5⃣4⃣
NABEEL BELLO YAKASAI shine cikakken sunanshi dane ga Alh,bello yakasai Aminin Dad kuma abokin kasuwancinsa ,dane ga yayan mami
Nabeel shine d’a na uku agidansu kuma su bakwai iyayensu suka haifa yanada yayyye biyu y’an biyu mace Dana miji wato WAHEEDA DA ABDUL-WAHID saishi sannan y’an uku salma ,saleema,Abdussalam sannan auta wato Nabeela
Mahaifiyarsu hajiya hassana mutuniyar Sudan ce bangaran shuwa Arab itama y’an biyu iyayensu suka haifesu itada Hussain dinta, kyakykyawar gaske ce ga fari ga uban tarin gashi har gadon baya kallo daya zaka mata ka gano irin baiwar kyau da Allah yaiwa Hjy hassana gata mace me yawon faraa da kirki batada k’yamar talaka ko kadan dik da kasancewar ta taso cikin tarin dukiya kuma ta auri me dukiya,y’an uwan mijinta sunada dinbin yawa kasancewarsa mutumin cikin gari amma dikkansu ta Iya zama dadu yanda suke da kirki sai sike zamansu da dangin mijinta lfy, kuma dake suma y’an boko ne yasa da ajinsu suke tafe.
Alh,Bello ya auro ta ne a harkar kasuwancinsa da yakeyi a Sudan yazama tamkar da agun mahaifinta don agunsa yake sauka inyaje can sari to anan Allah ya hada zuciyoyinsu mahaifinta kuwa ya aura mai ita dikda ansha rigima kafin danginsu su yarda da auran don dagewa sukai bazasu bawa bahaushe usul auran y’arsuba shikuma mahaifinta yace matukar yana num fashi ba abinda zai hana auren hassana da bello,to dake Allah yayi da rabo haka akati bikin bada son ran dangintaba mahaifinta da kansa da abokinsa suka kawota kasar Nigeria gidan mijinta,dake tanaso tai zamanta ba tare da damuwa ba balle dataga mijinta dan dangine sai hankalinta yak’ara kwantawa.
Ikon Allah watanta goma daidai ta haifo y’ay’anta biyu
Macen kamarta daya da ita namijn kuma farar fatarta kawai ya dauko amma kamarsa daya da Abbansa,
To haihuwar datai yasa tarin danginta tahowa suna daga sudan ,yanda sukaga dangin mijinta na kaunarta da kula da ita yasa hankalinsu ya kwanta da auran suka manta da komai,
Bayan haihuwar y’an biyu da shekara biyu ta haifi Nabeel shi saida ya shekara biyar sannan ta haifi y’an uku suma shekararsu uku ta haifi Nabeela wato auta,
Waheeda,Nabeel,da Nabeela suke kama da ummunsu matukar kama yan uku da Abdulwahid kuwa kana ganinsu kaga mahaifinsu don shima badaga namba wajan kyau irin na Hausa Fulani saidai farar fatar ummunsu da irin gashinta suka dauko, shiyasa inkaga y’an gidansu Nabeel kamar ka sacesu ka gudu don kyau Kansu ahade yake yake inkaga yanda suke muamala a tsakaninsu bazakace ga babba ga karami ba amma hakan baisa sun raina junansu ba, anyiwa Waheeda aure bayan tagama karatunta a b.u.k yanzu da yayanta biyu,saikuma Abdulwahid yana aiki a Aminu kano a cikakken likitan fata,saikuma Nabeel daya gama degree dinsa na biyu a kasar chana Inda yakaranci business donshi yanason yagaji mahaifinsa a fannin kasuwanci,
Wannan shine tarihin Nabeel Bello yakasai
Washe gari ———-
Baby tunda suka dawo daga skul tana dawowa tai wanka tashiga tsara kwalliya dikda kasancewarta bamai yawon yin ado a fuskaba amma aranar fenti kala kala tashiga yiwa fuskarta ta tsaida giran nan tata das haka tazo tazauna a gaban walldrower doguwa ce sosai ga fadinta ya kusa cinye bangon dakin ta bude kayane side by side tari guda kai saika dauka Kayan mutum gomane amma natane da islam mafi yawan Kayan bibbiyune maana dik Wanda ka dauko irinshi biyu ne saidai wani kala daya wani kuma kalanshi ya babbanta tundaga kan English wear Indian Wear, har zuwa kaya irinnamu na hausawa,
Wani material ta dauko bakine anmai ago da fulawa ja a milk ya hadu matuka anmai dinkin Riga da skeet dinkine irin na zamani sanda tasa Kayan zaka dauka ajikinta aka dinkashi yanda ya zauna das dashi ,
Ta saka dan kunne da sarka fation jajaye sannan tasa bangles masu Jan duwatsu tasaka da zobensu da tauko plart shoe ja ta ajiye agefe, tana daura dankwali islam tashigi dakin rike baki tai tana fadin
“wow big girl wannan wankanfa sai ina”?
“Bangane sai inaba wato bana kwalliya sai da dalili”
Dariya islam tai tace “ah ni ba haka nake nufiba ganinai nasan Indai ba fita zakiyiba bakya irin wannan shigar saidai English Wear to yanzu naganki harda tsaida dan kwali ba doleba inyi magana”
Baby rasa abin fada tai don ita kanta batasan dalilin wannan kwalliyarba dik da wani sashin na zuciyarta yana fadamata don Ya Nabeel zaizo ne amma sai tai saurin canja tunaninta,
Dabara ce ta fadomata tace