BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

     Tofa zaman gida yasamu manya tun ba'aje ko inaba  dayin candy baby ta  fara gajiya da zaman don haka tafad'awa mami zata rinka binta asibiti don bazata Iya zama ita kadai agida ba kowa yafice yabarta.

Zuwanta asibiti yasa ta k'ara kaunar karatun fannin lafiya arayuwarta don haka Tak'ara 

Azama wajan kallon dik motsinsu.

Lokacin da aka fara saida form a makarantu sai kuma shawararsu ta canja ita da Aisha don da school of nursing sukace zasuyi amma yanzu sai suka canja suje b.u.k suyi medicine,
To dake abinda sukeso shi iyayensu ke so nan da nan sai yayan Aisha yaje yasuyo musu form din dake dama sunyi jamb suka cike da dik dai abin da ya dace,

Basu shan wata wahala taneman admition komai da yayan Aisha sukeyi don yana da kafa a skul din sosai nanda nan suka gama komai sukayi registration sai kuma zuwan lokacin fara lecture.

Takuce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 2:19 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR ????????????????????????????

ZAMANI WRITERS ASSOCIATED

Na
LAYUZA KABIR ADAM

FOLLOW US ON THIS DETAILS:

LIKE OUR FACEBOOK PAGE:
↓↓

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

CHECK OUR BLOG’S
↓↓

Zamaniwriters.blogspot.com

DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:
↓↓
Zamaniwritersassociation@gmail.com

          5⃣8⃣

Parking driver yayi ta fito cikin takun ta na kasaita ta juya ga drivern tace “1:pm zamu tashi sai ka dawo kamar 2:45 haka”

Ta juya zuwa hole d’in da zasu yi lecture d’in a gefen k’ofan shiga ta tsaya tana sa wayan ta a kunne tace

 "Hello Aisha Kina ta ina"

“Sis gani zan shiga hole d’in ta k’ofan baya anan yaya ya ajiye ni”

“Ok nikuma ina ta gaba mu hadu a ciki”
Kusan a tare suka shiga Seat na biyu suka zauna kasancewar ba mutane sosai a ciki daliban basu zazzo ba

 Sun kai kusan  20minit sannan hole d,in ya d'an cika amma ba wani da yawa ba don dama an fad'a musu department d'in nasu dika basu kai 50 ba don haka cikin sauki da nutsuwa suke 

lecturer ya shigo da murmyshin shi bayan kallon su yai d’aya bayan d’aya daga bisani yace

“Good morning class”

“Morning sir”

Dik hole din suka amsa murmushi ya k’ara yi da ganin alamar sa mutum ne mai fara’a da sauki nan dai yai musu y’an bayane-bayane dan gane da kansa da kuma course d’in da zai rinka d’aukan su,

  Cikin k'warewa da Iya teaching lecturer d'in yai musu lecture ta  awa biyu wato 2 credit ce, kaso hud'u.  cikin biyar na d'aliban sun fahimci darasin 

(to abinka da k’wari kunsan k’aramin kai baya shiga ajin medicine ????)

K’arfe 10: suka fito da tarin d’oki kunsan sabon student da rawar kai duk girman sa
Waje suka samu suka zauna k’asan wata bishiya ta kalli Aisha tace

 "Sis kinsan ban yi tunanin abin haka yake ba sai naji duk abin ba wuya, nai zaton in ya fara lecture d'in zanji abinda kunne na bai taba ji ba".

Dariya Aisha tai tace “hhhmmm daina fad’in haka sis maybe wannan din ce muka ji saukin ta yanzu ba zamu gane komai ba sai tafiya ta mik’a”.

Kasancewar sai 11:00 zasu k’ara shiga wani lecture d’in yasa suka zauna nan sukai ta discussion a tsakanin su ta lecture d’insu

 Lecture d'in da suka  k'ara shiga ma 2 credit ne don haka 1:00 dai-dai suka fito kuma daga wannan sun gama sai gida.

Sosai suke jin dad’in karatun su a b.u.k don komai yana tafiyar musu yanda suke so suna fahimtar duk abinda ake musu wanda ma basu gane ba basa barin lecturer yabar aji sai suyi ta tanbayar shi yai musu bayani harsu fahimta

Sati biyu da fara zuwan su skul sun zama y’an gari sun fara gane bambancin dake tsakanin 0 level da university abin a bayyane yake kowa karan sa yake ci ba babbaka ba ruwan wani da wani Wanda yasan meya kawo shi yayi karatu Wanda kuwa kansa yake hayak’i yayi wauta.

Tunda suka fara zuwa baby da Aisha da dogayen riguna suke shiga kamar yanda suka tsara don koda Dad ya bata kud’i tayi siyayyan makaranta gowns kawai ta kara jibgowa kala kala kusan kala sha biyar bayan na gida da take dasu sama da guda talatin, don haka kullum da shigar take zuwa sai dai ranar da za suyi practices tunda sunasa lab coat to sai suyi shigarmu ta hausawa ko Riga da siket Riga da zani sai su d’ora lab coat d’in akai.

Da yawa idon y’an class d’in su sun sa shi akan baby da Aisha don gani suke girman Kai ne da su sabida basa shiga sabgar Kowa

tsakanin su da mutum gaisuwa ce mace ko namiji, don su daman basu da shiga sabgar k’awaye tun a primary har secondary sune k’awayen junan su sai islam dik Wanda ya san su su uku yasan su to yanzu da ba islam su biyu suke harkokin su,

to hakan da suke sai wasu suke ganin girman kai garesu, sunaji a gaban su za’ai ta gulman su amma ko kallo mutum bai ishe su ba balle su tanka masa.

Abinda ke gaban su shi suke yi don ko interval suka samu da yawa tsakanin lecture da lecture maimakon su zauna su yita hira a'a library suke zuwa su yita karatu  don su ba wani shiga cafeteria suke cin abinciba,

In suka yi break a gida to zasu tawo da d’an lemukan su da snack in sunji yunwa su ci abin su komai na su da tsari suke yin sa.

Takuce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 2:20 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????????

      *NA*

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

          5⃣9⃣

Lectures sun fara d’aukan zafi, gasu baby yanzu suna yawan practical gashi tsakanin hole d’in da suke lecture da lab d’in nasu da nisa don haka duk tafiyan ke damun baby.

wata rana suna hira da Dad a parlourn shi ya dube ta yace “baby duk kin rame karatun da wahala ko?”.

D’an murmushi tai tace “Dad ni bama karatun ba wannan zirga zirgan zuwa lab ke damuna, duk mutum yabi ya gaji. wlh Dad da k’yar nake d’aga k’afa na duk ciwo suke kemin”

Ta k’arasa maganan cikin muryan shagwab’a kamar zatai kuka.

Sosai Dad ya zuba mata ido yace

“Baby ina ganin zan baki duk inda zaki je a skul sai kirink’a motayawo da ita, saboda wannan zuru zuru d’in naki yana damuna”

  Murmushi tai mishi na nuna tsananin farin cikinta a fili ta d'ora kanta kan kafad'arsa tace

“Dad na gode Allah yak’ara tsawon rai da arzim’i me amfani”

Cikin jin dad'in addu'ar ta yace 
  "karki damu baby kullum burina inga farin cikin ki y'an matan Mami"

Da gudu ta shige part d’insu tana fad’in
“sis sis Kina ina fito kiji”

Islam dake d’aki ta fito da gudu tana cewa
“Me muka samu ne y’ar uwa ki kemin irin wannan kiran haka?”.

Mik’a mata hannu tai suka kashe sannan tace

” ke Yau Dad ya yarda da deriving d’inmu yace sabida zirga-zirgan skul zai ban motor”

tsalle islam tai tare da rungume juna.

Mami dake sakkowa a stairs ce tace
“Tom banda dai tuk’in ganganci baby kinga dalilin da yasa ya hanaku deriving tun tuni sabida tsoron karku yi ganganci da lafiyarku a titi don haka ki kula kinji”

Tace “tom Mami insha Allah za’a kiyaye”

* sati d’aya da maganan Dad ya bawa baby key d’in dalleliyar mota k’iran zamani ya’ yai blue black ce sai shining take, aikuwa itada islam kamar suhau sama don dad’i don dama sun dad’e suna son yabasu wannan damar su bama sabuwar motan ke sasu murna ba sai y’ancin da suka samu na deriving.

sun san yanzu duk inda zasu je kawai ba wani Deriver da zai rink’a kaisu, zarar mota kawai zasuyi su hau kwalta sun k’ara zama manyan yara yanda gidan masu kud’i wayanda gidan su yake cike da motoci na d’aukar magana da tsorata gayu.

Ganin irin murnar da islam ke yi sai kace ita ce ke zuwa skul d’in yasa Mami tokanarta suna zaune a parlour suna hira tace

“To islam Dad d’inku yace karfa ki d’auka harda ke yabawa daman deriving, baby kad’ai ya bawa kema sai kinje b.u.k zaki fara”.

Turo baki tai tana buga k’afa “haba haba mana Mami wai meye cikin tuk’in? Yaran ma fa da busu kaimu ba yi suke, amma mu sai maida mu k’ank’ana kukeyi Mami. gashi yanzu kuma an bawa Baby dama bandani kwana nawa ta bani?”.

Ta k’arasa da dungure wa Baby kai

Dariya Mami da baby suka sa don Mami daman sai da ta kiftawa baby ido kafin ta fara fad’awa islam d’in
To ganin dariyan da sukai yasa tasan tsokanarta kawai akeyi.

Tofa ran Monday Baby aka d’au babban wanka cikin wata bakar doguwar Riga ( black very) inji kanawa tayi light make up d’inta tai rolling da pink d’in k’aramin mayafin kashka sannan ta d’au pink jaka tasa plat shoe irin me tuta akansa d’innan shims pink ta d’aura agogo a hannun ta fatarshi pink sannan tasa Bangle’s pink a d’ayan hannun,

 Kai madalla da wannan wanka , harta fito Islam tace  "kin fito fa hajiya ta amma wayan ki ta b'ata wankan kalli cover d'in jikinta Jane kawo maza aje acanja mata Riga" 

karb’an wayan tai tai up stairs da gudu,

 B'angaran da suke ajiye tarkacan Kayan adon wayoyinsu tai ta d'auko wata pink d'in cover me Khan gaske tacire na wayan tasa wannan.

Da gudu ta k'ara sakkowa tamik'awa Baby wayan "tnx my lovely sis" tace tasa kai ta fice.

Takuce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 2:20 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
????????????????????????????????????

         6⃣0⃣

Daganin yanda take tukin akan kwalta kasan gayu da k’warewa sun zauna agun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button