BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan tashiga cikin skull d’in tai parking a gun da aka tanada dominshi d’an k’aramin past me gadin ababan abin hawan d’aliban yabata Wanda yake d’auke da number 37 ajiki tana tsaye ya manna wata number 37 d’in ajikin motan nata (sabida tsaro ) sannan yace zaki bada naira 50 kud’in gadi tace “ba damuwa inna fito zan baka “

Tana shiga lecture theater d’in ba mutane sosai mutum biyar ne tai musu sallama tasami gu ta zauna.

dikkansu binta sukai da kallo dan ko wa yaga wankan saiya k’ara kallonta ba k’arya , kus kus suka fara na gulma

Batafi 5 minit da zama ba Aisha tasako kai itama kamar baby sallama taiwa y’an class d’in tazauna kusa da baby suka kashe cikin mirmishi Aisha tace

“sis ya a motan kika zo kuma”?

   Da d'an mirmishi tace eh tana waje bari  mu gama lecture mu fita kiganta ai Dad ya hutar damu wannan zirga zirgan.

To k’arfe goma suka fito a lecture d’in suka nufi parking space d’in ta nunawa Aiaha motan suka tai mirmishi tace
“Kai sis Dad ya kyauta Allah yak’ara bud’i’

 Daga nan suka wuce  library don su d'anyi karatu tunda sunada interval na 1 hour.

Lokacin da suka fito a library sun d’an ja lokaci don saura 5min su shiga class da sauri sauri suka k’arasa parking space d’in amma da sukazo me gadin baya kusa wani ne a wajan baby ta k’arasa race

” don Allah ina me gadin”?

Yace “yazagaya band’aki kud’an jirashi kad’an”

Waje suka samu suka tsaya dik a k’age suke don wannan lecturer d’in da zai musu ba ishashshen kirki gareshiba zai iya hanasu shiga ,

Suna tsaye harkusan 10mint sannan ya dawo y’ar butarsa ahannu a hankali Aisha tace ” kashi yayi da ganin wannan dad’ewar” dariya sukasa a tare yana zuwa yace “hajiya kuyi hakuri don Allah nad’an zagayane”

Suka bashi past d’in ya duba numbern jiki sannan sukaje zasu d’au motan har ta bata wuta ya k’araso window da babyn take yace
“Hajiya kinmanta biki bada hamsin d’inba itace sana’ar ayi hakuri hajiya’

D’an dafe kai tai tace ” yi hakuri wlh na mantane inata sauri “

 Bud'e jakanta tai ta d'auko sabuwar 500 ta mik'amai yana shirin had'a mata canji tace "a kabarshi kawai ba wani abu"

Kamar zai kifa don godiya yaita musu addu’a yana fad’in Allah yabasu sa’ar jarabawa ya karesu sharrin me sharri.

Sanda suka k’arasa bakin hole d’in wani wawan birki taja tai parking Wanda yaja hankalin y’an ajin harda lecturer d’in ,

Suka shigo ajin cikin mutuwar jiki donba tabbas zai barsu shiga, wani kallo yai musu ya nuna musu k’ofa alamar su fita, cikin muryan shagwab’a da marairaita baby tace” sir kamana afuwa pls muna karatu a library bamusan lokaci yajaba”

Har cikin ransa yaji zakin muryan baice komaiba ya nuna musu gu alamar su zauna,

Ai kuwa mazan sukasa dariya da ihu ????
Don sungane abinda yaja hankalin sir .

Takuce
Layuza kabir Adam
[11/13, 2:21 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
????????????????????????????

Na
LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

Allah _ina rokonka da sunayenka tsarkaka kafitar dani sharrin masharranta ka kareni daga bin way’anda basa ganin girmanka ????

         6⃣1⃣

Sannu-sannu rayuwa ta rink’a zuwa tana wucewa ta kowace fuska. Bilal yanacan Kasar India yana karatun sa cikin nasara da kwanciyar hankali sai dai a gefe guda na zuciyarsa yana cike taf da wani k’udiri Wanda yabarwa kan sa ya zama sirri tsakanin shi da zuciyar sa.

Sukuwa y'an mata su Baby abubuwa suna ta tafiya sun yi exam har sunje hutu sun dawo.

 Karatun su suke yi me cike da daɗi da wahala kasancewar yanayin karatun medicine daban yake da sauran karatu shi abune da yake buk'atar nutsuwa da ja'jircewa sosai da sosai.

           Shekara guda tim yanzu suka cinye cikin karatunsu  Abu buwa da yawa sun faru na daɗi da rashin sa.

A gida da makaranta, kuma a wannan lokacin ne Islam ma tasami gurbin karatu a skul ɗin nasu, kuma itama a medicine ɗIn.

Shigowar islam b.u.k ya k’ara fito da ainihin Baby ma’ana ita Islam bata d’aukar wargi ko kaɗan saɓanin Aisha da baby da sai mutum yayi abu goma basu tanka musuba.

Yanzu kawancan Aisha dasu ya K’ara girma sosai don Dad yanada number ɗin Dad ɗin ma

Kuma Mami tana zuwa har gidan su gun maman ta itama maman tana Zuwa sun k’ulla zumunci me k’arfi tsakanin a su.

Yanzu Aisha kawo ta Deriver ya ke yi, in sun tashi sai su tafi tareda baby ta sauke su gida in lokacin tashin su ɗaya da Islam su taho gida tare

In kuma sun riga ta tashi sai su taho driver yaje ya ɗaukota.

Dad yai tafiya ta sati ɗaya ranar da ya dawo yazo musu da tarabar wata kyakykyawar mota kalanta ja dai dai mata.

Washe gari suka shirya tsaf cikin shigan su islam doguwan riga yellowce a jikin ta, Baby kuma wani material baki me yarfin ja don yau practical gare su yai kyau sosai ɗinkin riga da skate tai rolling da jan mayafi na kashka mai adon stones agaban sannan ta ɗora farar lab coat tare da Jan takalmi da Jan jaka ta d’auko key ɗin suka fito.

K'arfe goma za su shiga practical don haka sunada lecture 8-10 kamar koda yaushe yauma da sallama tashiga class ɗib kallo aka bita dashi

bata damu ba don tasaba da wannan Kallan da ake mata.

Bata samu kanta ba sai wajan karfe biyu suna fitowa ta kira Islam a waya Dan jin tana ina  tace " ina lecture amma yanzu zamu tashi ku jirani mu wuce".

  Suna k'arasowa gaban motan na su suka ga mutane zaune saman ta,  ga mata biyu tsaye suna hira.

 Da kallo ɗaya zaka gane rikakkun y'an duniya ne.

Sallama suka yi musu Aisha tace "don Allah zamu ɗauki  Motan ne".

Basu tanka ba suka bita da wani banzan kallo, sannan suka cigaba da hiran su.

Ganin abin rain in wayone yasa cikin kuluwa Baby tace

“Malamai bakwa jine zamu ɗauki motar mu mukace”.

Cikin muryan rashin mutunci wani ɗai daga cikin su yace 

 "Ke wai ina motan naku take zaku dami mutane da iyayi?".

Caraf wani ya cafke da cewa “Inaga akan wannan gwangwanin da muke kai suke magan, yanzu akan wannan abin za’a damemu da feleken banza?, wlh sai mu far fasa ta muga uban data tsaya muku”.

“Don Allah in kuncika ɓatattun y’an iska to fasa, kai koda kartan motan nan ma kuyi kuga haukan daya fi naku yawa wlh banzaye kananun y’an bariki”.

 Cewar Islam data k'araso wajan taji me suke faɗa

Takuce
Layuza kabir Adam ????
[11/13, 2:22 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
????????????????????????????????????

Allah ka k’ara d’aukaka musulunci da musulmi_Allah _ka ruguza kafirci da kafirai ????

          6⃣2⃣

Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin islam da y’an matan ita tana musu kallon matsiyata dame kuke tak’ama su kuma suna mata kallon tsagera tafi sauran iya rashin kunya ,

Wata tsawa ta sakar musu wadda har ta razana su baby cikin muryan gadara da yauk’i race

“Ku wawaye marasa tunani ku d’aga mana motanmu bakwajin me mukace ne tumaki kawai”

D’aya daga cikin y’an matan nasu ce ta d’aga hannu zata kaiwa islam mari kafin ta kai baby ta d’auketa da wani lafiyayyan mari Wanda yashiga har cikin kanta,ganin hakan yasa d’ayar kaiwa babyn dank’a da sauri baby tai baya tana fad’in no no no karki fara ma tab’ani da wannan k’azamin hannun naki me kuraje inba hakaba zan b’allashi , d’ago kai billy tai ta dubi samarin nasu tace

” dalla can wai kuna kallon wannan banzayen suna mana hauka bazaku d’au mataki ba “?

D'ayan saurayin me suna j.z ne ya duro akan motan yana fad'in
   "Haba mana guys karku badamu wannan ai fad'anku ne na y'an mata in mukasa baki cab'ewa zatai ,amma yanzu ku bar wasan nan haka zamu had'u dasu next time"

Hannu ya kad’a musu yai gaba dik suka bishi a baya.

Tunda suka shiga Motan ba Wanda ya tanka dik ransu a jagule yake,

Saida suka sauke Aisha sannan tai musu sallama suka wuce,

   Koda sukaje gida basu k'ara bi takan zancanba suka shiga yin abinda ke gabansu har lokacin kwanciyya yai suka kwanta.

Yauma sanda suka shiga skull d'in parking lot suka wuce bayan Islam dake Jan motan tai parking me gadin yazo suka gaisa yabasu past islam ta kalleshi  tace 

  " baba jiya ya akai ka bar y'an iskan nan suka zauna mana akan mota kuma naga baka barin ayi hakan" ?

Gyaran murya yai yace”hajiya kuyi hak’uri wlh way’an nan yaran y’an iska ne sun fi k’arfin kowa daka musu magana saisu ma rashin mutunci”

 Cikin takaici ta kalleshi tace " ai insunfi k'arfinka basufi k'arfin hukumar makarantaba zamu kaisu ga security"

Misalin k’arfe 12:00 Baby da Aisha suka gama lecture ita kuma islam sai k’arfe uku dan haka wucewa zasuyi gida driver yazo d’aukanta ,

Tunda suka kusa da parking lot d’in Aisha ta fara hango b’ar nar da aka musu kallon baby tai taga idonta ma bai kai gunba ta k’ara kallanta lokacin da suka je dai dai motan tace

 "Sis baki ganin abinda yasamu motan"

K’ur ta zubawa motan idon sannan tai wani mirmishin takaici tace
“Sis kinsan waye yai wannan aikin ko”

 D'aga kai tai ranta na matuk'ar bace

Dafa kafad’an ta baby tai tace” Aisha karki nuna komai ko akan fuskanki sabida a yanzu nasan suna kusa damu don ganin yanda zamuyi barsu sune matsiyata ,zasu gane kuransu”

Wato wani irin dagargaza akaiwa dikkan glass d'in Motan gaba da baya  gashi dik ansa k'arfe an karkarce fentin jikin motan an kun kunce tayoyin an fasa dik dangers gaba da baya, kai motan dai dik ba Kyan kalla ,

Fitowa sukai daga parking lot d'in suka sami wasu kujeru can gefe suka zauna, Aisha ta dubi baby 

“tace sisy kinsan meke ban mamaki yanda har sukaiwa motan nan haka ba Wanda yagansu kuma ina guard man d’in yake”

Mirmishi tai tace ” karkiyi tunanin dole wani zai gansu lokacin da zasuyi wannan aikin dalili kinga parking lot d’innan yana nesa da gun wucewar mutane kuma kinga motan nan tana tsakiyar motoci sai aimata komai wani bai kulaba ,sannan guard man da kike magana ai kinga bama mu ganshi gunba wayasan inda yake, kuma ko yana nan me zai iya tunda d’azu da kansa yafad’awa isy sunfi k’afinsa tsoronsu yakeji, so karki damu barsu kawai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button