BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Wayanta ta fitar cikin jaka takira islam tace in busu fara lecture ba tazo kusa parking lot tasa mesu,
Sannan takira driver yazo ya d’aukesu motansu ta sami Matsala,
Daga k’arshe takira dad d’insu cikin muryan shagwaba data saba mai tace
“Dad muna cikin matsala a skul munyi accident motanmu dik ya b’aci”
Cikin tashin hankali yace” agarin yaya amma ba abinda yasa meku ?ina islam d’in”

“Dad dik bamu sami matsala ba bama cikin motan ai,masu aikine a vaf sun shigo da yashi nai parking kan hanya suka bi da motan dikta b’aci, Dad inba damuwa ka k’ara siya mana irinta pls My Dad”

“Ok ok karki damu bari sai kunje gida zamuyi maganan”
“Ok Dad bye “

Takuce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 2:23 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
????????????????????????????????????

Allah ina rok’on ka daka k’arawa mahaifina lafiya me d’orewa alfarmar girman zatinka????????????

       6⃣3⃣

Suna nan zaune Islam ta k’araso da fara’arta tace

“y’an uwa ya buku tafi ba ko zaku jirani ne”

 Mirmishi  sukai suka nuna mata waje donta zauna baby tace" sis kinsan meya faru ? Dik abinda kika gani karki nuna  kin damu ko kad'an",

 nan dai ta fad'a mata abinda akaiwa motansu, mik'ewa tai tsaye tace"haba wai nufinki mu barsu suci bilis? Ai wlh sai sun gane bama tsorons- - - -  bata k'arasa ba sukaji hayaniyya acan parking lot d'in tashi sukai suka k'arasa gun,

Wani sukaji yanawa wata mata bayanin abinda ke faruwa wai sunzo d'aukan abin hawansu ne guard man d'in baya nan sunata jiransa sai can suka hangoshi k'asan wata mota kwance kamar baida rai da suka d'agashi shine suka ga da ransa yanata maganganu irin na maye alamar a bige yake don haka aka taru ana kallonsu kowa na fad'in albarkacin bakinsa kan yazama tsohon banza tsoho dashi yake shaye shaye,

Kallon juna sukai Aisha tace wato yana can yana maye aka mana b’arna a mortar,

Tafi sukaji agefansu  da muryan j.z yana cewa

” wato shi mutum in yakasance d’an k’arya sai kai maganinsa gobe saika ga dame zaima k’aryar”
Kafin yamaida numfashi Islam tai wata y’ar dariya tace

"Kai Allah ya shiryi d'an matsiyata Wanda bai San arziki ba ai shi me arziki akoda yaushe zuciyansa a sake take da walwala baya sa damuwar wani aransa balle ya dameshi, matalauci matsiyaci  shine me hali irin naku na dabbobi, wa kake da suna kai kayi kad'an ka takamu wlh  kaida way'anna karnukan da suke binka abaya"

Wata k"ara j.z yai yace "ke k'aramar Mara kunya ni kike fad'awa way'annan  ban zayen magan ganun "?

Caraf Aisha tace”your brain is not working, I think you are out of senses I – – – – – “
Zata k’ara magana taji ankaiwa wuyanta dank’a
Billy ce me wannan aikin amma me itada zata shak’i Aisha kawai itama taji an dank’i kanta da tsananin k’arfi tare da jijjigashi fit baby tacire mata d’an kwali me za’a gani kwakwis gashi ne Wanda da k’yar aka tattarashi aka d’aure da ribbon sai kuma tarin wasu manyan ribbons na acuci maza data cikasu acikin d’an kwalinta,????????

Ihun da sukaji ne yasa suka San jama'a sun cika wajan anata kallonsu, d'aya cikin y'an tawagar j.z ne ya taso a kufile dan billy budurwarsa ce yaji ciwon abinda baby taimata agaban mutane hannu ya d'aga ya kaiwa fuskan baby mari amma kafin yasauke yaji andank'i hannun nasa an d'auke tashi fuskar da kyakykyawan mari a kid'ime ya juya don ganin waye da wannan gangancin Mlm idi drivern su baby ne daya k'araso gun yanzu yaga rikicin,
    D'alibai sun cika gun suna kwasar kallon rikin inda wasu keta murna akan wulakancin da su baby sukaiwa kungiyar su j.z don sun gallabi d'alibai da wulakancinsu  in ke mace ce suyita binki wai da sunan soyayya dik su dami rayuwarki in namiji ne sai sun ganka da wata mace suzo gabanku suyi ta watsa ka suna ma rashin mutunci,

K'arasawa islam tai gaban j.z ta kafe shi da wani wula kantaccen kallo sannan ta nuna shi da yatsa tana fad'in 

“We are not going to listen to you guys,we will definitely going to report all of you to the school,so that they’ll be able to punish you according to what you did – – – –

    K 'arar motan security's na skul d'inne ta tsaida islam subida ankai musu report d'in baba me gadin motoci yana maye kuma suna zuwa suka Tatar da wani cest d'in, tanbaya suka shiga yi akan way'anda suke rigima aka nuna su baby da su j.z nan aka kwashesu dikkansu zuwa security office don jin baa si sannan suka d'auki me gadi suka kaishi asibitin skul don abinciki lafiyarsa.

Takuce
layuza kabir Adam????
[11/13, 2:23 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

  NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
????????????????????????????????????

Me girman kai shine wanda rayuwar sa bata ci gaba yana kunyar yai tambaya kar ace bai iya ba yana kunyar ya nemi gyara kar ai mai dariya ????
Allah karka samu cikin bayi masu girman kai????

        6⃣4⃣

Bayan ankai su office d’in cheap security ya fara tanbayar su Baby meya had’asu da su j.z har sukayi fad’a cikin makaranta kuma bayan sun San doka ne dik d’alibin da yai fad’a cikin makaranta kora ce sakamakonsa,

   Tiryan tiryan baby ta fad'a musu dik abinda ya faru daga m ya zuwa yau da irin b'ar nan da sukaiwa motansu,

Kallonsu sosai ogan yai yace ” dik abinda ta fad’a haka ne ko kuna da abin fad’a”

J.z ne ya fara inda inda nason k’arya ta zancan baby wani security dake gefe yace ” karkuyi gan gancin b’ata mana lokaci kuyi k’ok’in fad’a mana gaskiya k’ila gaskiyarku ta ceceku amma matyk’ar Ku kai mana k’arya mukai bincike muka gano to kunsan zamu mik’aku ga students affianced daga nan kuma za’a rubuta muku takar dar kora”

Iya kid'ima y'an kungiyar j.z sun shiga dik cikinsu ya d'uri ruwa sai gumi sukeyi,

Karo na biyu aka k'ara tambayarsu akan su fad'i ta bakinsu, sunusi yafi kowa  kid'ima cikinsu shine yafara magana kamar haka

" wlh na rantse da Allah dik abinda baby ta fad'a gaskiya ne mu muka fara tsokanarsu kuma Billy ce tasamu sabida tace mana ta tsanesu Dik  dik sanda ta gansu da had'ad'd'iyar shiga take ganinsu  wai suna mata wani gani gani muyi mata maganinsu,   don Allah officer kuyi hak'uri wlh in kuka koremu ni ban San wane hali zan shiga ba sabida da buga buga nake karatunnan gashi muna shekarar kusa da k'arshe ne"

Cikin tsawa ya tare shi da cewa " lokacin da zaka aikata Lefin bakai tunanin daya kake karatunba baka tuna dokar makaranta ba sai yanzu zakai mana zancan banza dikkanku hukuncin korane gareku kaida tsagerun y'an uwan naka, kuma saikun had'a kud'i. Kun gyara musu motansu y'an iskan yara kawai"

Dik wani report sun gama rubutawa zuwa students affianced  domin atarkata su j.z 

suna nan zaune har wajan karfe uku zuwa lokacin muta nan dik sun gama jirkita matan dik sunsha kuka sun k'oshi don sun fiskanci da gaske koransu ta tabbata,

Ahaka report yak'ara zuwa daga hospital  na skul cewa bincike ya nuna baba me gadin motoci lemo yasha wanda aka zuba Kayan maye kuma daya dawo normal suka tanbayeshi meya had'ashi da lemon da akasa Kayan maye aciki ya shaida musu su j.z ne sukazo gunsa suka zauna wai zasu tayashi zama shine suka fito da lemo zasu sha suka bashi roba d'aya to tunda yasha be k'ara sanin ina Kansa yake ba, 

Kuma agun wani d’an department d’insu ya bada shaidar cewa har shaye shaye suke acikin makarantar kawai d’alibai na tsoronsu ne shiyasa busu iya fad’awa security ba,
Tofa ana wata ga wata Kenan nan fa aka k’ara can Kansu j.z kowa na fad’in albarkacin bakinsa cikin office d’in wani me d’an dama dama ya dubesu yace

“it is good for you guys to be have well more especially in the school”
Na gefansa yace”
Just leave them,they don’t have sense”

Sudai k’uru k’uru kawai sukeyi da idanuwa don tusa ta k’urewa bodari,

Bayan an duba motan su baby akaimata kiyasin kud’in gyarata kimanin dubu d’ari da hamsin don dik glass d’in dake jikinta ya tashi daga aik ga fenti da suka karkarce,
Sunajin kud’in da akace zasu biya suka zube ak’asa suna bawa su baby hak’uri akan su taimakesu su yafe musu ,baby ce wadda dik tausayinsu yacikata tace”ba komai mun yafe musu officer abar maganar motanmu”

To anan ne suka sami d’an rangwami,
Haka suna gani aka bawa kowannansu takardar kora ,

Kuma aka rubuta sunayensu ajikin dikkan wani announcement bord dake skul d’in na cewar ankoresu tare da rattabo lefin da sukai sabida yazama izna ga sauran d’aliban da suka maida iskanci sana arsu .

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:21 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATED
????????????????????????????????????

       6⃣5⃣

Sai magriba su islam suka dawo gida don suma an tsaidasu anja musu kunne kan dik abinda ya had’asu da wani d’alibi kada su d’au doka a hannunsu suyi maza sukai report,

Sai bayan sunyi wanka sunyi sallah suka fito parlour cin abinci anan sike bawa mami labarin dik abinda ya faru ta jajanta sannan suma taja kunnansu akan karsu k’ara biyewa wani suyi ko cacar baki a skul in ba haka ba mutuncinsu zai zube amatsayinsu na y’ay’a mata mota kuma tace su kwantar da hankalinsu z’a suyo musu wata sabuwa amma kafin akawo musu sai su rinka’a amfani da sauran na gida,

To koda Dad ya dawo shima haka suka kora mai bayanin abinda ya faru ya jajanta sannan yace amma da kukace accident kukai,mirmishi sukai babya tace
“Dad Aida ni banso muka kula suba Auntyn fad’a ce tace baza abarsu suci bilis ba” ta k’arashe da tsokanar islam dariya sukai Dad yace

 "to ba wani Abu cikin satinnan zaa kawo muku wata irinta, waccan kuma zanwa driver magana yaje su janyo ta ya kaiwa baka nikai baza'a rasa wanda za'a bawa itaba, su kuma sunjawa Kansu ai gashi sunyi shekarun banza abaya ,Allah ya kyauta dai"

Haka su baby sukaci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali cikin satin aka kawo musu wata mortar amma ita maroon calor ce ,


 ***********   shekara biyu cif da fara karatunsu a b.u.k wata ranar litinin  suna gida kasancewar suna hutun semester ,lokacin  yakai wata shida Nabeel baizo gidansu ba sai dai yana kiransu a waya lokaci lokaci , amma dik da haka baby tanajin abinda takeji aranta game dashi har yau in taji an fad'i sunansa sai taji gabanta ya fad'i ko kuma inta kwanta taita tunaninshi, aranta tana so ta gano ko menene dalili amma ta kasa sabida bata tab'a soyayyaba balle ta gano ko sanshi take dik da tarin samarin dake bibiyarsu akoda yaushe amma mami ta hana sabida tace had'a karatunsu da soyayya matsale ne don haka ko shawaar amsa tayin wani basu tab'a yiba.

Hankalinsu dik yana ga kallon film d’in Indian Hausa da sike na munnahh , knocking akai ba wadda ta motsa cikinsu domin bud’ewa saida mami tai magana sannan baby ta tashi taje bud’ewa, wata y’ar k’ara tasa tare da rufe baki da hannu ganin wanda ke tsaye cike da murna da farin ciki tace ya “Nabeel shigo mana” ta bashi hanya ya shigo shima fuskanshi d’auke da fara’a islam ma mik’ewa tai cikin mamakin ganinsa da murna tace ‘yau agari ai na d’auka ka koma China dik da zama sai mubika muyima aure acan”
Kai mata rankwashi yai aka yana fad’in “daga dawowata ba sannu da zuwa sai surutu”

Bayan ya zauna  suka gaisa da mami itama cikin farin ciki take mai sannu da zuwa, baby taje ta kawo mai lemo da ruwa ta zuba mai a cup sannan tace"ya Nabeel sannu da zuwa ya hanya ya China"

Yai y’ar dariya sannan yace “dik Alhamdulillah baby ya nasameku us fama da islam”

Dariya sukai islam tace”hhhhmmmmmm wai ya fama dani sai kace wata Yarinya k’arama”

Hira suke sosai na yushe gamo mami ta mik’e tace”bari na koma sama in kalli labarai don in ina nan bazaku barni ba”

Bayan tashin mami ya Nabeel ya kalli islam yace” ke ya naga kin rame ko karatunne”?

"Hhhhmmmm kai dai Bari kawai yaya abin ba magana fa, bakaga ma ramar baby har tafi tawa ba "?

” ai ita dama bata kaiki k’iba ba shiyasa baza’a gane ramarta da wuri kamar keba, kefa kinga dik y’an kumatun nan sun koma”

Dariya sukasa dika baby tace “yaya baka rabo da tsokana”

 Mikewa islam tai tana fad'in "ina zuwa bari in d'ouko wayana naga shida tayi yanzu maryam Naseer zata kirani tacemin zata aikomin da sakona in driver d'insu ya d'auko k'annanta islamiyya zai biyo ya kawomin"

Tana fad'a tai up stairs da dugu 

Juyo da kallonshi yai ga baby yace” emmata wai da kika ganni tsoro kikaji ne naga kin rikice”?

Cikin sanyin miryarta da jin kunyan rikicewar da yace tayi tace” you surprise me seriously”

“Allah emmata”ya fad’a yana karya miryanshi da salon tsoka nanshi

K’asa ta k’ara yi da miryanta cikin y’ar shagwab’arta tace”ya Nabeel why is it that you don’t used to come now,you abandoned us”

Wani kallo yai mata dayasa wani Abu tsirgawa har cikin ranta da sauri ta d'auke idonta daga kallonshi,
"Baby I'm so busy, kinsan da ina k'asar kullum ina zuwa yanzu kinga banida ishashshan lokaci, amma yanzu mun gama tsara komai a China ansami wani ansa akan aikina yanzu ni zan rink'a kula da kamfaninmu na k'asar nan ,don haka in kin ganni a China sai dai inje y'an kwanaki in dawo"

Tace “to Allah ya taimaka”
Yace “amin emmata ,kinyi kewana Kenan da bana zuwa me yasa”
Rud’ata tanbayar tai ta rasa amsar bashi can Allah ya kawo mata dabara tace”a a ni kewan karatun larabcina nayi harna manta wasu abubuwan sai dai inna duba a littafi in tuna”

Kafeta yai da ido don ba amsar daya so ji daga gareta ba Kenan cikin canjawar yanayi yace

“it’s like you didn’t missed me”
Kafin ta bashi amsa islam ta sakko tana cewa”sis bari in lek’a gate in amso sakon,ya Nabeel kai kuma bari indawo kaban labarin y’an matanka na China naga har wani d’an tunbi”
” to jeki dawo kiji labari Yarinya”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button