BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:22 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????
6⃣6⃣
Cikin wani San yanyan yanayi ya juyo da kallonshi ga baby yace “baby nayi tunanin kinyi kewana Ashe ba haka ba ne “
Girgiza kanta tashiga yi tana fad’in” um um ya Nabeel kaima kasan baza mu kasa kewanka ba ko ba kaiba ma kana tare da mutum in baya nan kana kewansa”
Kallonta ya k'ara yi da yanayi daban don ba haka yaso tace ba yaso jin wani Abu daga bakinta , basarwa yai yana canja salon Hiran da cewa " baby ya skul I hope dai kuna maida hankali sosai"?
“Um yaya muna yin iya kacin iya warmu”
“To Allah ya bada sa’a Ku k’ara dagewa “
Islam ce ta shigo da dan gudunta tana zuwa ta zube a gefen baby tace "sis kinga ta kawo mana tsamiyar biri da kurna da magaryar"
Bud’e ledar hannunta tayi ta fito da kulli uku aciki ko wanne yakai kwano d’aya ,baby tace “kai amma ta birgeni musamman ma akan wannan tsamiyar birin, kawo mana Abu mu zuba mu b’are shi duka in an cire b’awan an Tara yafi dad’in sha”
Nabeel dake ta kallon yanda suke zumud'in shan abar yai d'an mirmishi yace
“Kai kunada kwad’ayi yanzu kan tsamiyar birin kuke wannan rawar k’afar ?nifa lokacin da Mike yakasai kullum saina siya in zamuje islamiyya gata nan k’ofar islamiyar mu kamar banza ,amma tunda muka bar yakasai ni banma k’ara ganinta ba sai yanzun “
Islam tai dariya tana cewa "ai muma a yakasan da mukaje rannan gidan inna muka ga tana sha muka sha shinefa mukaji dad'inta shiyasa yanzu da naji saddika zasu garinsu tace akwai a can nace ta kawo mana"
Kiran sallar magriba akai hakan yasa Nabeel mk’ewa ya hau sama yaiwa mami sallama yana saukowa suna hawa baby ta matsa gefe ta bashi hanya don ya wuce yana zuwa saitinta yace
"emmata gobe ki tanadi zuwa na akwai maganar da zamuyi me mahimmanci"
Kad’a kai tai batare datace komai ba sai k’irjinta dataji ya bada rassss,
Ya kalli islam yace " ke fa ya dai kika tsare ni da ido"
Mirmishi tai tace “a a ba komai ka gaida ummy da nabeela da kowa da Kowa”
NIGHT****
(DARE MAHUTAR BAWA INJI BAHAUSHE)
Dikkan wanda baida damuwa baccinsa yanzu yayi nisa kasancewar yanzu 1:00 garin yayi tsit musamman dake garin na sanyi ne, zuciyoyin guda biyu dik acikin tunanin junansu suke kewa tare da shauki juna dik ya dabai baye su,
Ab'an garen Nabeel ba bakon Abu bane agunsa tun dad'ewa zuciyarsa kemai dakon son baby yaso fallasa asiri n Ransa tun a saa'in amma jin dayai mami na yawan mai maita bazata bari yaranta Susa soyayya aransu ba balle su kasa maida hankali a karatu har sai sun gama karatunsu na medicine domin tana son su gajeta ko bayan ranta,kuma taxi gaba da ja musu kunne akan tsare gida ga dikkan namijin dake shigo musu da zancan soyayya balle kuma aure, wannan dalilin ne yasa shi sawa ransa salama akan ya b'oye soyayyar dayakewa baby har zuwa sanda yake ganin mami zata basu damar soyayya, amma akoda yaushe da iya yake kwana aransa kuma kullum Sonta k'ara girma yake aransa musamman ma yau dayaga ta k'ara girma da wani kyau na daban,
To hakan shine ma yakasance ga baby amma ita ada bata yarjewa ranta cewa son Nabeel take ba tafi dai alak’anta abin ga birgeta d’abiunsa da tsarinsa yake ,amma yau kam ta tabbatar son nabeel take yi don yanzu inta runtse ido sai ta rink’a hangoshi da irin kallon da yai ta mata ayau don ta tabbatar da wannan kallon na soyayya ne a zahiri da kuma irin yanda yarink’a mata magana cukin sanyin murya,dammm gabanta yak’ara fad’uwa data tino da yace gobe zai zo zasuyi magana me mahimmanci ,to Kodai zaizo ya bayyana mata sirrin ransa ne kai amma dataci SAA a rayuwarta in har namiji kamar Nabeel ya zama mijinta ga tsantsar kyan fuska ga uwa uba kyan hali ga cikar zati da kamala, mirmishi tai ta juya agadon cikin nishad’i data tuna yanda siffar Nabeel take dogo ne me faffad’an k’irji abinda tafi so Kenan ga minjin da zata aura, dammmm taji k’irjinta ya kuma bugawa data tuna da sharad’in mami akansu na hana soyayya yanzu ,to amma kuma ai ya Nabeel d’an gida ne bashi da Matsala ko yanzu yace ayi auran ba wata dauwa,don gaskiya itafa indai ya Nabeel ne zai aure ta ko yanzu ayi ta shirya.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:22 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????
6⃣7⃣
Da tsananin sanyi aka tashi yau don haka sun dad’e a d’aki busu fitoba tun bayan sallar asuba da sukai suka koma bacci don sun mami zata aiki tana shirya inta lek’o ta dubasu zata wuce bata tashinsu,
Islam ce ta farka misalin k’arfe goma tai wanka tare da ta fito tsayawa tai bakin gadon tana fad’in sis nah ki tashi haka, juyi tai idonta cike da bacci tace
“sis barni wlh da bacci a idona” ta k’arashe maganan da rufe idonta,
Islam shiryawa tai cikin Kayan sanyi Riga da wando y’ar k’asar jamani blue ta fito k’asa tai break,nan taci gaba da zamanta tana wasa da wayanta,
Baby bata farka ba sai wajan sha biyu ta shiga wanka kusan 30 minutes sannan ta fito ta zauna abakin gado dik jin jikinta take yamata nauyi ,ahankali take komai ta shafa mai tare da tura rukanta ta taje gashinta tasa mai reborn dik abinda take daga zaune takeyi y’ar pouder tasha fa a fuskanta tare dasa wa lebenta lips tik ta zizara kwalli wanda yake k’ara fito mata da zahirin kyan idonta ,
Tana sa unders d’inta islam ta shigo d’akin tace
"sis yau kuma bacci ne yai dad'i"
D’an mirmishi tai tace”wlh kinga nai baccinma kuma me makon Dana tashi inji k’arfin jikina amma kinga dik jin jikin nawa nake yamin nauyi kamar anmin duka”
“Ayya sannu sis ,Kodai dannau ne ya danneki cikin baccin har yanzu kuma bai sakekiba”
Da Yar dariya ta k’arasa zancen,
Hara ranta tai kawai ta Mike zuwa bakin woodrop ta bud’e Riga da dogon wandon jeans ta d’auko black ta saka sannan ta d’auko katon rigar sanyi ta d’ora akai tasa hulan sanyi fara tasa,bayan ta idar da sallah ne ta sa safa sannan ta dauko bakin takalmi soot tasa don baby akwai masifan jin sanyi ,
Tana sakkowa down stairs tana duba wayanta hankalinta kwance saida tazo k’arshe ta kai kanta ga kujerun parlourn rasssd taji gabanta us fad’i ganin ya Nabeel zaune ,
Tsayawa tai tak’i k’arasa wa bata San dalili ba ,saida yagama kallonta tsaf sannan ya ce “emmata Yakima tsaya k’araso mana,ko k’afance ta makale aza a d’auko ki”?
Ahankali ta jayo k 'afa funta ta k'araso parlourn ,1 seater ta zauna kamar bak'uwa tace"yaya barka da rana"
Saida yagama k'are mata kallo sannan yace "barka y'ar Hutu ai na kira islam a waya tace kina bacci har lokacin,me ya faru ko bakijin dad'i ne"
Girgiza kai tai tace”um um lfy na qlau kawai jiya ne ban samu cikakkken bacci ba sai yanzu na rama shi”
“Munyi anko Kenan kinga nima jiya ban samu bacci sai wajan k’arfe uku fa ,amma kinga ni dake nasaba ban rama shi ba”
"Hhhhhhmmmm ta ai kai kasaba da k'in baccin wuri ni kuwa kaga dik dad'ewa na ban wace 11: ban kwantaba sai dai in ina exams ne"
Islam ce ta sakko tana "fad'in yaya ka k'ara so Ashe naje nayi sallah"
“Um na k’araso amma fa yunwa nakeji me zaku bani inci”?
“To sai dai a duba kitchen d’in muga abinda sukayi ,ko dake ga baby nan itama ko break bataiba taje ta had’o muku abincin Donni kama ba yanzu ba”
Kallon baby yai yace"to y'ar babyn mami kawo mana abinci muci tunda kema ko break biki ba"
Mik’ewa baby tai zuwa kitchen tacewa me girkin ta had’o abinci na mutum biyu tare da flet biyu da spoons ya juyo zuwa parlourn,
Komai a kintse me aikin ta kawo ta jera a dining ta juya, baby ce ta tashi zuwa dining d’in ta zuba musu kowa a nashi flate d’in tasa spoon ciki ,d’an d’aga muryanta tai tace “ya Nabeel ga abincin na zuba maka”
Tasowa yai yazo yaja kujera ya zauna wadda ke opposite tata ,ahaka suke cin abincin bame cewa uffan ita dik kunyarshi ce ta cikata shi kuma aikin kallonta ne yasa shi yin shiru sau uku tana d'agowa suna had'a ido don haka bata k'ara d'agowa ba, har ya cinye nashi ya mik'e yazo dai dai kanta tare da rank'afo da kansa yace" baby wai meke damunki yau d'innan? Gashi abin cin ma bikici na kirki ba"
D'ago da kanta tai ta kalleshi a kai kaice sannan tace",ba komai kawai jikina ne ban jin dad'insa"
"Ayya sannu to amma kici abincin sosai mana"
Gyad’a Kai tai sannan ta bud’e flask d’in tea ta had’a, dawo wa parlourn sukai sika zauna tana d’an kur bar tea d’in suna ta’b’a hira, lokaci lokaci suna had’a ido saiyai mata mirmishi tare da kashe ido’ dik ya takurata ji take kamar ba a gidansu take ba.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:22 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????
Dikkan yabo da godiya sin tabbata ga babban sarki gwanin iya kyauta (ALLAHU GADIRUN ALA MAN YASHA’U)
6⃣8⃣
Acikin zuciyan baby ta matsu taji me Nabeel zai fad’a mata tunda yace mata in yazo zasuyi magana me mahimmanci amma gashi sai Jan aji yake mata yak’i fad’in abinda ya kawoshi dik da dai tasan bazai wuce zan can yace yana sonta ba tunda gashi ai yauma dik abinda yake mata irin kalan soyayya ne,
Shikuwa dik zaman da yake ya rasa ta ina zai fara aikinshi gareta don yana tunanin kamar bazai samu had’in kai daga gareta da kuma maminta ba don haka kawai yasa aransa zai k’ara lokaci zuwa nan da watanni ya gama sabar mata da muamala dashi yanda kai tsaye in ya fito da sirrin zuciyarsa zai karb’u,
Bayan anyi sallar la'asar yaje mosque ya dawo yana shigowa mami na shigowa nan suka gaisa tai up stairs don tai wanka da sallah tad'an huta,
Zama yai tare da kunna t.v don lokacin su baby dik suna sama yin salla basu sakko ba,
Yai zaman kusan 10 minutes sannan suka sakko a lokacin baby ta canja shiga zuwa wata doguwar Riga brown me had’e da d’an hijab ajiki irin k’irar Arabian d’innan,kasan cewar sanyin da ake ya ragu,
Sosai rigar ta amshi jikinta sai dai ta d’an kamata kasancewar roba ce jikinta amma dake da dogon wandon Jean’s ajikinta yasa bai bada matsala ba,
K’ur ya kafe ta da ido harya manta ko meyake aikatawa saida islam ta tafa hannunta tana cewa