BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

"ohh broth me kake kallo haka kamar yawu zai zuba abakin ka"
Hara ranta yai cikin matsanan ciyar kunya amma dake namijin duniya ne sai ya wayance da fad'in
"ke wasu larabawa aka hasko a tashar nan kawai sai naga wata me kama da friend d'ina shukrah,shine na fad'a tunanita"
Dammnnnn k’irjin baby ya buga da jin yace tunanin wata friend d’inshi yake wai ita shukrah,
Ita kuwa islam dariya tai tare da k'ara tafa hannu tana fad'in
“ah yaya kace kana tunani sahibarka ne kawai, ummm ta dafa hannunsa tana cewa amma fa sunanta da dad’i shukrah matar Nabeel um nice” ta k’arashe da lek’a fuskanshi cikin tsokana,
Hannunta ya matse da k’arfi har saida tai k’ara yace”waya fad’a miki budurwa tace daga ce miki k’awata ce shine harda cewa mata ta, baby kina jin wannan sistern naki zata min sharri ko”
Ya k’arashe da kallon baby, ita kuwa a sa’in dik bata cikin hankalinta don dik ta shiga wani yana yin b’acin rai da k’unci don haka ne ma ta kafa idonta akan screen d’in wayanta kamar bata San me suke cewa ba, sai da ya k’ara mai maita maganarshi ga baby sannan ta d’an d’ago kanta tace”ban San me tama ka ba hankalina bai kanku ina d’an duba wani Abu a phone nawa ne”
Tana fad’in haka ta maida hankalinta ga wayanta don bata son yana shigar da ita cikin wannan Hiran nasu me bak’anta mata rai,
Jawo laptop d'inta tai islam ta shiga yin abinda ke gabanta,hakan ya bawa Nabeel dam dawowa kusa da baby yakai hannun ya jarb'i wayanta da take shafawa a cikin gallery take tana rage wasu hotinan da suka dad'e, ci gaba yai da kallan pic's d'in fuskanshi d'auke da mirmishit sai aransa yake fad'in ya Allah ka azirtani da wannan kyakykyawar Yarinya,
D’ago Kansa yai yana kallonta da lumsheshshen ida nuwansa kallon kallo sukewa junansu ita kallon tuhuma take mai na irin kallon da yake mata, shi kuma kallon tsabar kauna yake mata ,ganin kallon yai yawa tace murya can k’asa” haba yaya ya da wannan kallon”?
Kashe ido yai can k’asa da murya shima yace “pics nake gani na big girl sun fita,
Kauda kanta tai tana kallon inda islam take don ta gane ko hankalinta na Kansu amma saita ga ita sabgarta kawai take da system d’inta,
Cikin miryan shagwaba ta k’ara fad’in “nifa yaya kallo takurani yake ka barni haka d’an ban wayan tawa”
Mak’e kafad’a yai yace”rowan waya za’amin y’ar baby”
“Wayyo Allah wannan bawan Allah zai kashe ni da wannan ida nuwan nasa”
Ta fad’a a ranta.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:22 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????
6⃣9⃣
Haka ya kasance a wannan lokacin kullum sai Nabeel yazo gidan wani lokacin ma anan yake cin abincin dare sabida hutun da ya d’an samu ba inda yake zuwa sai gidan, yayi amfani da damarsa dosai wajan hargitsa kwakwalwar baby koda yaushe da irin salon da yake amfani dashi wajan samata wani feeling nashi dik wanda ya zauna atsakaninsu awannan lokacin sai ya fuskanci akwai wata munafikar soyayya da ake b’oyewa a tsakaninsu, ko islam ta fahimci wani Abu amma sai ta basar ta zuba musu ido taga iya gudun ruwansu, don hakama in yazo gidan sai tsiri wasu Abu buwan taki zama gunsu don su sake dik da bata tab’a nunawa Baby komai ba,
Yauma da yamma baby na zaune a parlourn k'asa tana chart awayarta Riga da wando ne jikinta wandon 3 quarter Rigan kuma body hug ce ta kamata matuk'a hannun iya kafad'arta ne,kanta bud'e ba ko hula bare d'an kwali, cikin nishad'i take chart d'in don hira suke tafkawa a group d'insu,
K'irrrrr akai knocking bata ko motsa ba aka k'ara yi ta mik'e don bud'e k'ofan bata ajiye wayan ba tana tafe tana danna wayan harta kai ga bakin k'ofan ta bud'e kusan 30 seconds suna a tsaye shi yana kallonta ita tana kallon waya, a hankali k'amshin turaren sa yaje ga hancinta a tsorace ta d'ago kanta karaf suka had'a ido, " ohhhcccccc God" ta fad'i tare da runtse idonta da k'arfin gaske tace"ya Nabeel don Allah ka koma ka koma"take fad'i tana tafiya da baya da baya still idonta a runtse,
Wani irin shock ne ya kamashi jikinsa lokaci d’aya ya mutu kallonta yake cikin shauki da burgeshi a yanayin da take, ganin ta kusa zuwa jikin glass d’in dake bayan ta yasa cikin zafin nama ya k’arasa gunta ya janyo ta ai kuwa cikin rashin sa’a ta fad’o jikinsa ???? atare wani gigitaccen shocking ya kamasu, da sauri ya cikata ta haye stairs da gudunta na bara????,
Jan k’afarsa yai ya zauna a kan kujera ya lumshe ido yana maida numfashi,can brain d’insa ta dawo aiki ahankaki ya furta
"ya salam,astagfirullah Allah kasani bada niya na tab'a ta ba"
Miryan islam yaji tana sakkowa down stairs d'in "yaya Kai ne daman ka shigo ka tsorata min sister d'ina"?
Bud'e idonsa yai yace" sarkin surutu daman kina gidan"
"Um ina sama yanzun dai na sakko"
Zama tai kusa dashi suka gaisa yana tanbayarta mami bata dawo ba tace”ta dawo tana d’akinta tana hutawa”
Haka sukaci gaba da hira har kusan 20 minutes baby bata sakko ba dik hankalinsa yana kan hanya so yake kawai yaganta,
Islam ta kula da yanayin shi ta mik'e"bari in dubo sis d'ina najita shiru tana fad'a ta haye stairs d'in
Ahankali ta tura k’ofan d’akinnasu ta shiga akan gado ta hangota kwance ta duk’un k’une kanta cikin bargo kamar me bacci,_ k’ara sawa tai kan gadon tana biga k’afar babyn tace”sis me haka da yamman nan kika kwanta kinsan dai babu kyau ko?”
Juyowa tai tace”isy ba bacci nake ba fa”
“To meyasa kika kwanta ko bakida lfy ne”
“Um um lafiya na qlau kawai ina d’an san hutawa ne”
“Haba mana sis kinga fa ya Nabeel yazo,zaiga rashin kyautawarmu mun barshi shi kad’ai,kinga ni mami tace min inje kitchen in tsaya kan masu girki zaayiwa Dad bira bisko,in kika sakko sai ki tayashi hira”
Mik’ewa tai ta zauna tana kallon islam tace”sis nifa kunyar yaya nake wlh kinga fa da Kayan daya ganni”
“To mene abin kunya tunda ya Riga da ya ganki ai sai dai a kiyayi gaba, in kika nuna mai kina jin kunya kinsan halinsa da tsokana zai hanaki sakat amma kawai ki basar”
Jim tayi sannan ra mik’e ta d’auko dogon Riga (after dress) ta d’ora akan Kayan ta balle mab’allayen Rigan har k’asa ta d’auko d’an mayafin rigan ta d’aura akanta sannan ta biyo islam suka sakko, kwata kwata kin yarda tai ida nuwansu su had’u don haka ma ta bud’e wayanta ta cigaba da chart d’inta,
Islam ta mik’e tai kitchen ta barsu su biyun kusan 5 minutes ba wanda ya tankawa d’an uwansa, shi yafara kauda shirun ta hanyar fad’in
"baby kiyi hakuri d'azu ba niyyata rik'e ki ba naga kina tafiya da baya ne gashi kinzo jikin glass kar ya yankeki shiyasa na jawo ki"
“Um hmmm” kawai tace, ya kuma fad’in “ai lefinki ne daga anyi knocking biki san waye ba kije bud’e kofa a dik yana yin da kike,kinga inma ba ni bane kila ko maaikatan gidanne maza”
Turo d’an bakin tai gaba tace”to nifa na manta ma ba hijab jikina kuma kaima inata cewa ka koma inje insa hijab ka tsaya kallona”
D’an mirmishi yai yace”ni bake nake kallo ba ba fa ina tunanin wani Abu ne kawai, banma kula ke kika bud’e k’ofanba”
“Au nai tunann kana sane kak’i komawa”
Dariya ce task kubce mai ya basar kawai yashiga bata labarin ban dariya donta sake don yaga dika takure take har lokacin kunya fal idonta.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:23 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????
7⃣1⃣
Tana nan zaune bakin gado har aka kira sallah ta mik’e tayo alwala tazo ta tada sallah, bayan ta idar hadda shafa’i da wutri tai adduo’inta data saba ta shafa,tana ninke prayer mat d’in ta fad’a gado don bacci ne sosai a idonta I kuwa tana kwanciya ya d’auketa.
Da safe da wuri ta tashi don tun 8:00 ta farka kasancewar ta kwanta da wuri, juyi kawai take tana tunani duniya da wasu Abu buwan da yazo kwakwalwarta, ganin tunanin yak'i k'arewa yasa ta tashi ta shiga wanka tai brush data fito bata wani tsaya kwalli ya ba kawai mai ta shafa da tura ruka ta zira Riga da siket na English wear's tasa y'ar hula akanta kallon islam tai taga baccinta take fi sabilillah kawai fitowa tai parlour shiru gidan kamar ba muta ne,
Kitchen ta sakko data shiga taga dik masu aiki sunata aikace ai kacensu taja kujeran roba ta zauna tana gaishesu da b'arin jiki suka amsa suna rankofowa,
Mirmishi tai tace
” karku damu iya Ku ci gaba da aikunku yau nazo tayaku hira ne sannan in koyi abinda ban iyaba”
Dariya sukai dika sukaci gaba da aikinsu
Tana zaune tana ganin dik yanda sike gudanar da girkin cikin kwarewa da tsafta sai abin yake birgeta,
Kusan awa guda suka gama had’a komai na abincin funkaso da miyar agushi sannan farfesun Kayan ciki sai kunun gyad’a,
Masu alhakin jerawa a dining sukaje suka shirya dining d’in, fitowa tai daga kitchen d’in ta koma d’akinsu anan ta Tatar da islam ta tashi hartai wanka,
Wajen goma suka fito zuwa dining d'in kowa yaci abinda yake shawa'a san nan suka dawo parlourn k'asa suka zauna suna d'an hira, kasancewar mami tana gun Dad sai wajan 12:00 suke break dik ran week end indai ita ke da girki k'aunarsu suke kwasa.
Misalin k'arfe biyar na yamma Nabeel yazo gidan mami ce kad'ai a k'asa su suna d'akinsu tare da Aisha data zo tun wajan biyu zama yai suka gaisa yace "yauma y'an matan gidan basa nan?"
” a a suna d’akinsu Aisha ce ta zo”
"Ok gobe zasu koma skul ko"
Nuno wani shiri akai a tashar da take kallo shi yaja hankalinsu dik suka maida ida nuwansu ga t.v d'in,
Kusan 30 minutes da zuwansa suka sakko Aisha a gaba sai islam hannunta rik'e da d'an kwalinta sai da suka sakko ta ganshi da sauri ta d'ora d'an kwalin a kanta Aisha ce ta fara fad'in "Ah ya Nabeel daman kazo" yai mirmishi kana yace" Aisha kuna d'aki kun k'ule ana suburbud'a zanje yaushe za'asan nazo, musamman wannan akun tana kusa ai ba magana"
Zumburo baki islam tai tace” eh da mutum me shiru shiru ai k’ara wanda zai magantu bai fiye gulma ba, itama wadda kake tinanin bata surutun suda ce inta ganka ne take Shiru”
Dariya sukai dika Aisha ta kuma cewa”wai ya Nabeel sai yaushe zaku dai na wannan dabin da isy”
Mirmishi yai yace"sai randa ta girma"
Dika dariya suka k'arayi mami tace"Aisha tafiya zakiyi "
“Eh mami zan wuce”
“To kigaida maman naku kice tayi hak’uri har yanzu Kayan basu k’araso bane shiyasa taji shiru”
“Tom mami zan fad’a mata”
fita sukai suka raka Aisha gate inda driven ta ke jira,
Bayan sun dawo suka Tatar saishi kad'ai mami ta hau sama kallon labaran k'arfe shida.
[11/13, 11:23 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????
7⃣0⃣
A wannan lokacin ne hutun su ya k’are zasu koma skul to Monday yau asabar dik sun gama wani shirinsu na komawa skul, sai dai zuciyan baby cike take taf da k’aunar Nabeel ta rasa ta ina zata b’ullowa lamarin domin ita dai baza ta iya fad’awa wani tace son Nabeel take ba balle kuma shi gogan don abin kunya ne babba gareta ta cewa wani d’a namiji tana sonsa koda kuwa zata bar duniya a sanadin son nasa, amma kuma fa gaskiya tana azabtuwa da k’aunar sa yayin da shi kuma take tunanin zuciyansa tana ga wannan Yarinya da yake fad’a wato shukrah,???? lalle in kuwa haka ne rayuwarta tana cikin had’ari ya ilahi yanzu ace kawai taji za’ai bikin ya Nabeel da wata Mace ya zatayi tab d’in ba makawa tasan ranar barinta duniya yayi ke nan,