BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

‘”Rayuwa ta tana cikin had’ari wai meke damuna? Ko kuma ni irin tawa jarabawar Kenan,Allah be rage ni da komai ba na ni’imar duniya komai najin dad’in rayuwa Allah ya bani bana tab’a Neman wani Abu na jin dad’in rayuwa inrasa baiwa ta kyau da diri Allah yai min ilmiy arabi da boko Allah ya ban gwargwadon iko, amma sai gashi Allah ya jarrabi zuciyana da son wani bawa nasa da bai San ma ina yi ba wanda ciwon sonsa yasa dik naji was y’an can ni’imomin sun gushe ban jin dad’in komai yanzu fa arayuwar nan kawai k’arfin hali nake don kar a gane halin da nake ciki wayyo ni KHAUSAR Allah ka kawo min mafita????”

Hiran baby kenan da zuciyarta data keyi tana zubda hawaye????

 Saurin goge hawayen idonta tai don jin motsin islam ta rufe idonta kamar tana bacci,

“Sweety ki tashi ki shirya mu tafi kar yamma tayi kinga anyi azahar”

Tashi tai tana mitstsika ido wai ita bata yarda ba bacci take,

Wanka tai ta d’auro alwala bayan tai sallah tai d’an light make up ta sa atamfa doguwar rida wadda ake kira da(A shape) ja ce atamfar ta mata kyau tasa d’an k’aramin mayafi ja a wuyanta, sannan ta zira takalminta ta fito parlour inda islam ke jiranta, sallama sukaiwa mami suka fito,

Sun hau titi sosai islam ke Jan motan zuwa sabon gari don yin kitso hira suke sama sama baby ta maida kujeran baya ta kwantar da bayanta ajiki tare da lumshe ido, islam tana ta mata magana amma bata sani ba ta fad’a tunanin mutumin, rage gudu tai ta kai hannunta ta ruko na babyn ahankali tace

"sweet sis wai meke damunki ne kwana biyun nan  dik sai nake  ganinki wata iri dubi fa dik kin rame,baki San magana sosai ki fad'amin damuwarki"?

 Lumshe ido tai tace"ba komai dear na kawai yanayin jikina ne ban jin dad'insa"

Mirmishi tai dan tasan ba gaskiya baby ta fad’a mata ba amma saita basar tace”ayya sannu sis han in munje gida sai kisami magani kisha ko “

Gyad’a kai kawai tai

Kitso aka musu mai Kyan gaske ka’ananu sosai fuskansu ya fito fes gwanin sha’awa yamma lis suka dawo gidan,
Up stairs sukai a parlour suka zube sunawa mami sannu da gida ta amsa fuskanta d’auke da mirmishi tace”jibi yanda fuskokinku suka fito sukai kyau dan Allah amma baku son kitso kullum kai a tsefe kamar India wa, shi kitso da kuke gani ado ne matuka ga y’a mace dik munin mace in tai kitso sai kaga fuskanta tai kyau”
Y’ar dariya Kawai sukeyi don dik sanda sukai kitso sai mami ta ta fad’in su dage su rink’a yi yana k’ara musu kyau,su kuma kwata kwata basa son shi don sai suyi wata uku basuyi kitsoba sai dai kullum fa cikin gyara yake da mayika kala kala,

Jin an fara kiran sallah yasa su mik’ewa zuwa d’aki don sauke farali,

Mami harta kai bakin k’ofan d’akinta ta juyo tana cewa “bayan fitarku ko Abdullahi waheed da Nabeel sun zo hard a Abdussalam ma dik suna gaidaku”

Had’a baki sukai suna fad’in”to muna amsawa”

Bayan sunyi salllar suka fito yin dinner shima sina gamawa ta koma d’aki ta zauna jira kawai take akira sallan isha tayi ta kwanta.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:24 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????

           7⃣1⃣

Tana nan zaune bakin gado har aka kira sallah ta mik’e tayo alwala tazo ta tada sallah, bayan ta idar hadda shafa’i da wutri tai adduo’inta data saba ta shafa,tana ninke prayer mat d’in ta fad’a gado don bacci ne sosai a idonta I kuwa tana kwanciya ya d’auketa.

  Da safe da wuri ta tashi don tun 8:00 ta farka kasancewar ta kwanta da wuri, juyi kawai take tana tunani duniya da wasu Abu buwan da yazo kwakwalwarta, ganin tunanin yak'i k'arewa yasa ta tashi ta shiga wanka tai brush data fito bata wani tsaya kwalli ya ba kawai mai ta shafa da tura ruka  ta zira Riga da siket na English wear's tasa y'ar hula akanta kallon islam tai taga baccinta take fi sabilillah kawai fitowa tai parlour shiru gidan kamar ba muta ne,

Kitchen ta sakko data shiga taga dik masu aiki sunata aikace ai kacensu taja kujeran roba ta zauna tana gaishesu da b'arin jiki suka amsa suna  rankofowa,

Mirmishi tai tace
” karku damu iya Ku ci gaba da aikunku yau nazo tayaku hira ne sannan in koyi abinda ban iyaba”

Dariya sukai dika sukaci gaba da aikinsu

Tana zaune tana ganin dik yanda sike gudanar da girkin cikin kwarewa da tsafta sai abin yake birgeta,

Kusan awa guda suka gama had’a komai na abincin funkaso da miyar agushi sannan farfesun Kayan ciki sai kunun gyad’a,

Masu alhakin jerawa a dining sukaje suka shirya dining d’in, fitowa tai daga kitchen d’in ta koma d’akinsu anan ta Tatar da islam ta tashi hartai wanka,

 Wajen goma  suka fito zuwa dining d'in kowa yaci abinda yake shawa'a san nan suka dawo parlourn k'asa suka zauna suna d'an hira, kasancewar mami tana gun Dad sai wajan 12:00 suke break dik ran week end indai ita ke da girki k'aunarsu suke kwasa.

Misalin k'arfe biyar na yamma Nabeel yazo gidan   mami ce kad'ai a  k'asa su suna d'akinsu tare da Aisha data zo tun wajan biyu   zama yai suka gaisa yace "yauma y'an matan gidan basa nan?"

” a a suna d’akinsu Aisha ce ta zo”

 "Ok gobe zasu koma skul ko"

  Nuno wani shiri akai a tashar da take kallo shi yaja hankalinsu dik suka maida ida nuwansu ga t.v d'in,

  Kusan 30 minutes da zuwansa suka sakko Aisha a gaba sai islam hannunta rik'e da d'an kwalinta sai da suka sakko ta ganshi da sauri ta d'ora d'an kwalin a kanta Aisha ce ta fara fad'in "Ah ya Nabeel daman kazo" yai mirmishi kana yace" Aisha kuna d'aki kun k'ule ana suburbud'a zanje yaushe za'asan nazo, musamman wannan akun tana kusa ai ba magana"

Zumburo baki islam tai tace” eh da mutum me shiru shiru ai k’ara wanda zai magantu bai fiye gulma ba, itama wadda kake tinanin bata surutun suda ce inta ganka ne take Shiru”

Dariya sukai dika Aisha ta kuma cewa”wai ya Nabeel sai yaushe zaku dai na wannan dabin da isy”

  Mirmishi yai yace"sai randa ta girma"

 Dika dariya suka k'arayi mami tace"Aisha tafiya zakiyi "

“Eh mami zan wuce”

“To kigaida maman naku kice tayi hak’uri har yanzu Kayan basu k’araso bane shiyasa taji shiru”

“Tom mami zan fad’a mata”

  fita sukai  suka raka Aisha gate inda driven ta ke jira,
Bayan sun dawo suka Tatar saishi kad'ai mami ta hau sama kallon labaran k'arfe shida.

[11/13, 11:25 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????

          7⃣2⃣

Kujeran dake gefansa baby ta zauna yayin da islam ta zauna a wadda take facing dashi, a hankali baby tace “yaya barka da yamma”

“Yawwa barka dai baby ya shirin komawa skul”

“Um gashi munayi gobe kam zamu koma”

Kallon islam yai yace "wa yaga isy a 200 level,baby kuma 300 za'a wuce ko"

 Mirmishi baby tai tace"um  ai dik kamar yaune in Allah ya nufa ma zamu kammala"

Itadai islam wayanta ta zubawa ido da alama wani abin ya tafi da hankalinta ne,

 Kallon baby yai yai k'asa da muryanshi cikin zakinta da dadi yace"baby kitson nan yamiki kyau sosaisosai biki ga yanda fuskanki ta k'ara kyauba"

Cikin lumshe idon da bata San tayi ba tace

" na gode yayana"

Ayanda tai maganar da yanayin yasa shi jin wani yammmm ajikinsa ya kuma k’asa da murya ” baby ki rink’ayin kitso don Allah ina so inga mace tayi musamman ke da kike da gashi da yawa”

Kallonsa tai da tuhuma tace”to kasa budurwarka ta rink’a yi mana tunda kana so in mu k’annanka munyi”

Y’ar dariya yai “yace to ai bani da budurwa kinga ai sai insa k’anne na suyi in gani”

Mirmishi tai”hhhhmmm to kacewa islam ma ta rink’a yi tunda tare Mike zuwa”

Kallon islam yai yace “isy me kike ne naga kin nutsu haka”?

“Um ina d’anyi hira da friend d’ina ne”

“Ok jiya dana zo mami tace kunje kitso, muga kitson ko yayi kyau”?

Hara ransa tai cikin wasa tace a nawa zaka ganmun kitso”

“A dik yanda kikai mai kud’i”

“Tab d’in bazaka ganmin gashi ba kaje shukrah tayi ta nuna maka”

D'an zare ido yai yace shukrah a ina zan ganta ita da bata k'asar nan, kuma ma on tana nan saita bud'e min gashinta in gani ba k'anwata ba ba mata ta ba"

“To in ba matarka bace ai budurwarka ce”

Juyo da kallansa yai ya baby wadda tinda aka anbaci sunan shukrah farin cikin da take ciki ya gushe amma dake mace ce me zurfin ciki baza ka gane halin da take ciki ba,

Yace” baby kina jin islam”

D’an mirmishin yak’e tai tace”to ai gaskiya ta fad’i”

"Ok had'emin kai zakuyi Kenan to yau dai bari in fad'a muku wace ce shukrah a wajena ko zaku barni in huta da batun ta"

‘Shukrah Abdulshakur shine cikakken sunanta mun had’u ne a makaranta a sanadiyar ganin sunanta da nai kusa da nawa ajikin bord a matsayin way’anda sukafi kowa k’ok’arin exam a shekarar, da fari sunanta ne ya fara birgeni sannan na jinjina mata matsayinta na mace take da k’ok’ari haka, hakan yasa nasa araina sai na ne meta mun k’ulla friend ship da ita, dik da department d’inmu ba d’aya ba, lokacin dana ganta nasha mamaki ganinta Yarinya k’arama kuma cikin shigarta ta kamala hijab harda nik’ab,mun k’ulla k’awance da shukrah wanda hakan yasa muka shak’u da juna sosai don dik sanda bamu da lecturer mukan had’u muyi ta tattauna abinda zai k’are mu shukrah languages take karanta don haka ta iya yaruka kala kala amma tana son yaranta na larabci don haka dik hiranta rabi da larabci takeyi ana na koyi larabci nima ta ita Hausa sosai don zakuyi zaton ta zauna a k’asar Hausa amma ba abinda ya had’ata da hausawa sai makaranta, shukra ita kad’aice gun mahaifinta don haka yake masifar sonta kuma d’an raayin boko ne don haka yasa aranshi sai shukrah tai karatu harta ce ta gaji, shukrah tana da k’ok’ari na buga musali don haka cikin skul d’inmu dik an San sunanta amma da wuya kaga mutum d’ari da zasu ce ma sun san kamanninta don koda yaushe cikin nik’ab take ko nima min kai kusan wata 5 tare sannan ta yarda naga fuskanta ba wata kyakykyawa bace amma fara ce doguwa me dad’in murya, ga rik’o da addini matuk’a ba dad’ewa da fara kawancen mu muka k’ulla soyayya,lokaciny da ta sanar da mahaifinta ni take so ta aura kai tsaye ya ce bai amince ba don bazai amince ta auri wanda ba k’abilarta ba hasali ma yace yai mata miji a dangi sa, kasancewar a him rah Yarinya me biyayya ta shaida min kawai mu hak’ura muci gaba da friend ship tunda Abbanta bai amince ba’

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button