BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“To kunji tsaka Nina da shukrah kuma yanzuma an mata aure tun tuni,
Don haka kar ma Ku k’ara had’ani da matar wani”
Ajiyan zuciya baby ta sauke jin k’arashen zancan nasa nacewa anwa shukrah aure,amma da kam
cikin ta dik ya d’uri ruwa,
Dariya islam tai tace “ayya kace an kasa ka, to Allah ya kawo wata mafi alkairi”
Da Sauri ya amsa da”AMEEN”.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:25 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION
????????????????????????????????????????

        7⃣3⃣

2 weeks letter
Su baby an tsunduma karatu lecture ta fara nisa a 300 level komai ya k’ara tsauri yau suna skul gobe suna hospital practical,

Zuwan ya Nabeel ya ragu sai dai kullum saiya kira waya ko ta baby kota islam suyi hira, dik da hiranshi da islam bata nisa zata tsokaneshi ko shi ya tsokaneta amma sai suyi Minti 30 suna hira baza ka tab’a gane ko jin me baby ke fad’a ba in suna wannan wayan,ga wanda yasan soyayya yana gani yasan k’auna ake kwasa amma su sunk’i amincewa Kansu ita suke dik da kowanne a zuciyarsa yasan cike yake da k’aunar d’an uwansa,

Ita dai islam tana gefe tana kallon ikon Allah amma ita da Aisha sun kafa misu ido dik motsin da zasuyi suna an kare in tayi tsami kowa zaiji,

Wani Abu ma da yake k’ara bawa Islam dariya yanda baby ta dage da kitso tunda Nabeel yace yana so dik 2 weeks kaji tace zataje sabon gari kitso, hhmmmm soyayya Kenan.

Ahaka suka cinye  semester suka koma second semester kuma a m kacinne hak'urin Nabeel ya k'are don haka ya shirya bayyanawa baby asirin zuciyarsa

Ranar wata lahadi yazo gidan yasamesu a gardin da Aisha sunata hiransu yazo yaja kujera ya zauna bayan sun gaishe shi, suka shiga hiran dashi musu  sukeyi akan sunan  wata powder da aka turowa islam a wathApp ta manta sunan powdern gashi ta goge photon kwalin, baby tace (classic)ne fa islam tace ba haka ba ai kuwa take islam ta kira number d'in wadda ta turo mata ta tanbayeta ta Tina mata sunan powder d'in tace (Tara) ne atare suka sa dariya harda Nabeel yace

"Baby sarkin musu gashi islam ta Fiki gaskiya sai kiyi shiru"

Sosai ta k'ule da dariyan da sukai mata gashi shi kuma harda k'arin bayani,

Shiru tai bata k'ara magana ba anata hira Aisha tace"sis ya dai kikai shiru"?

Hara ra ta watsa mata ta kauda kai

Nabeel sarkin tsokana yace “au biki huce ba daga y’ar dariyan da mukayi”?

Bata tanka shi ba shima ta mik’e tai hangar cikin gida dik binta sukai da kallo ganin da gaske haushi taji yasa ya mik’e ya bita yana fad’in bari inje in bata hak’uri karta had’ani da mami,

Taje dai dai korido d’in dake kusa da parlournsu ya cimmata d’an d’aga mirya yai yace “babynah” taji shi sarai amma sai tai kamar bataji ba don ya kuma mai maita sunan daya fad’a, “babynah don Allah tsaya” cak ta tsaya amma bata juyo ba har yazo kusa da ita yace” baby pls kiyi hakuri ban San ranki zai b’aci ba kinji”

Kallon sa tai da shagwab'a idonta harda y'ar k'walla tace'sabida suna tsokana ta shine kaima ka biye musu ko"

“Ya salam ya furta ahankali domin wani Abu dayaji ya tsirgamai har tsakar kai,

Matsowa yai kusa da ita ya marairaice murya tare da kashe ido yace” plssss my hubby Kiyi hakuri bazan k’ara Bari su isy suyi miki dariya ba kuma nima bazan k’ara miki ba kinji”

Yana maganar ne ida nuwansa a lumshe cikin yanayin soyayya, d'ago da Kanta tai ta d'an kalleshi suka had'a ido da sauri tai k'asa da idonta, 

“Baby na kinyi hak’uri ko”

Gyad’a kai tai don bakinta ya mata nauyi bring d’inta ta tsaya da aiki to wai me ya Nabeel yake nufi da kiranta da way’an nan suna yen me yasa yake son k’ara tsun duma zuciyanta cikin sonsa- – – katse mata tunani yai ta hanyar fad’in

“Baby nah ina son magana da ke yanzu ki d’an ban aran hankalinki kinji, baby zuciyana ta dad’e da kamuwa da k’aunarki matuk’a, baby ziciyana tana sonki tana son rayuwa dake har abada, ina son ki tai makeni ki amshi soyayyata ki amince in zamo abokin rayuwarki mu zauna a inuwa d’aya matsayin miji da mata! Ina sonki baby na!ki amince da soyayyata kinji hubby nah”,

Wata irin aza babbiyar kunya ce ta kamata ji take inama k’asa ta bud’e ta shige, wai yau ga ranar da take fatan tazo mata amma kuma tazo ta rasa ya zatayi don kunya da kid’imewa,

“Kinyi shiru baby ko biki amince in zamo miki abokin rayuwa ba? Kice wani Abu mana sweetheart”

“Don Allah ya Nabeel ka barni ka ban hanya in wuce kaji”
Dik abinda take fad’i hannayenta na rufe akan idonta ,mirmishi yai yace to in kin shiga ciki zaki kirani ki ban amsa?
Da Sauri tace eh na yarda don fatanta dai kawai ya bata hanya ta gudu, matsowa yai kusa da kunnenta yace to jeki amma ina jiranki da yanzu har dare,bata hanya yai ta wuce ta gudu tai parlour,
Mirmishi yai cikin jin wani dad’i ya koma gunsu islam fuskarsa d’auke da fara’a,

” yaya yadai kaketa fara’a haka”

“Hhhmmmm bari isy wannan sistern taki akwai rikici nadai lallab’ata na gudo, bari In wuce gida Aisha ki gaida y’an gidan “

Yasa kai yai babban gate don Jan motansa,

Had’a ido sukai suka tafa Aisha tace “wato sis har yanzu fa muta nan nan basu yarda da Kansu ba suna son juna sun zaunay nuku nuku”

” A to mudai in tai wari zamu ji”

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:25 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????

Ya uban giji ka kare mu sharrin me sharri dikkan wanda yake nufinmu da mugun Abu Allah ka maida masa kansa , mu kam bamu nufin kowa da mugun Abu Allah Kaine shaida .????????????

        7⃣4⃣

Tunda ta shiga d’aki ta haye bed cikin tsananin farin ciki juyi take tana fad’in Allah na gode maka daka nuna min wannan ranar yau wai ya Nabeel ne yake furta min yana so in zama abokiyar rayuwarsa ta har abada, lalle ni Baby me nasara ce a rayuwata tunda har gwarzon namiji irin Nabeel ya furta min Kalmar so da k’auna babu abinda zance sai Alhamdulillah.

Tana jiyo motsin su Islam tai maza ta rufe ido, Jan k’afarta Aisha ta fara tana fad’in “ke daga shigowa sai ki fara bacci da yamman nan kinsan kuma babu kyau ki tashi”

Farin cikin da take ciki shi ya mantar da ita fishi take dasu,ta mik’e zaune tana cewa”bafa bacci nake ba kawai dai hutawa nake”

Islam tace “sis Aisha fa tafiya zatai”

“Ok habibty zaki wuce? Bari akira drivern mu ya kaiki tunda naki yak’i zuwa.

Sakkowa sukai taiwa mami sallama sukaje gate suka kira driver ya d’auketa,

 Tunda akai sallar magriba tana kallo kiransa yanata shigowa amma tai biris har akai sallan isha bata d'aga wayanba, ko hira bata tsaya yiba gun Dad sama sama tamai sallama ta dawo d'aki ta barshi da Islam, bayan tai wanka tai brush tare da d'auro Alwalan bacci ta fito tasa sleeping dress d'inta yalwataccu ta haye gado tare  addu'a ta kwanta,

Wani kiranne ya k’ara shigowa sai da yakusa tsinkewa sannan ta d’aga, shuru tai tana jin sauke ajiyan zuciyanshi, sannan yace” baby nah kina jina? Don Allah kiyi magana inji dad’i kinji”

"Um yayana ina jinka fa"

Ajiyan zuciya ya sauke tare da cewa” yawwa hubbyna kinsa zuciyana cikin wani hali ina sonki Baby kice kema kina sona kinji hubby ta”

  Ji tayi wani shauk'i ya baibayeta kamar tana yawo a duniyar sama, cikin miryan shagwab'a tace"Toni me zance maka yaya na'

 "Kice kina sona"
"To ai kaima kasan ina sonka"

 "Um um so na soyayya nake so kimin bana y'an uwan taka ba"

“Hhhhhmmmm”

“Me ne ne hhhhmmmn kodai baki sona”

"Ni dai bacci nakeji zan maka tex"

Tana fad’in haka ta katse wayan.

Bin wayan yai da kallo cikin fadu'uwar gaba don yana jin kamar bazai nasara ba, dafe goshinsa yai yana fad'in" _ya_ _ila'hi_ _Allah_ _kasa_ _Baby_ _ta_ _karb'i_ _soyayyata_ ".

  Anata bangaran ma zubawa tata wayan ido tai tana sakin wani irin mirmishi me cike da tsan tsan farin ciki,

Gyara kwanciyanta tai tafara rubuta mai tex d’in d’an short ta tura mai

    _"Bazan_ _butul_ _cewa_ _soyayyanka_ _ba_ _sabida_ _ka_ _cancanci_ a _soka_ "

     Yana zaune ya zubawa wayan ido yana jiran shigowar sak'on nata, ai kuwa yana jin

‘d’in d’in’ yai saurin bud’ewa, dik da ba ta haka yaso ta amsa mai ba amma ya godewa Allah, yasan yanzu hankalinsa zai kwanta.

********
     Bayan sati guda wata irin soyayya suke me cike da tsantsan k'auna waya kullum cikinta suke amma a b'oye don bata San kowa ya gane, inya kirata sai tayi wayo tacanja waje ko kuma in ba yanda zatai ta tashi saitai rejected d'in kiran.

Wannan shi ake kira da (kifi na ganinka me jar koma) don k’ir idon Islam akansu sai dai kawai tayi dariya in taga Ankirata taje ta b’uya,

Yau suna kwance har bacci Fara d’ibansu kiranshi ya shigo ta lek’a idon Islam taga ko tayi bacci “sis sis” ta kira sunanta don k’ara tabbatarwa,jin shiru yasa ta d’aga wayan cikin wata mirya me tada tsikan jiki tace
“Yayana”
Mirmishi yai Yace “um Baby nah zuciyana Tanata bigawa da biki d’aga ba nai zaton ko lefi nayi”.
“Ya za’ai inyi fishi da zuciya na,kawai dai ina d’an uziri ne hubby na”
“KHAUSAR ina sonki”

“Nima ina sonka my Nabeel” ta fad’i mirya k’asa k’asa,

  "Baby bazan jure zama bakya  kusa dani ba gaskiya zanwa Abbana magana yazo yasami Dad asa mana ranar aure sai kici gaba da karatunki a gidana"

“Shagwaba mirya tai”um um yayana nidai baza’amin aure yanzu ba nifa yarinyace”

“Hhhmmm kin taba ganin Yarinya ta iya soyayya?”

“To ai Nima d’in ban iya ba”
“Lalle ma ai kikafi haka iya soyayya to ban San yanda zanyi ba ahaka ma in akamin wani lafazin ina jina a duniyan sama, inyafi haka kuma ai sai in shid’e”.

“Kai yayana nidai ba ruwana”

“Baby kinsan wani abu ?”
“Um um saika fad’a zuciya na”

  "Baby . . . .  . . 

K'it ta katse wayan jin girman maganan daya fad'a" Kai wlh namiji bashi da kunya ji ya Nabeel Kamar ustaz anma yai ta yanko manyan zantuka acikin kunnena".

[11/13, 11:26 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button