BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

17/9/2017
????????????????????????
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEM

WANNAN SHAFIN NAKINE EMMATA NA AYSHA SAHLA
(Allah ya rayaki yajikan mahaifiyarki )

        0⃣8⃣

Yana fitowa daga masallaci sallar magriba ya sameta a falow da mirmishinsa ya zauna kusa da ita
Amina dauko mayafinki ki kira Bilal muje mugaida yaya ko
Fuskarta fal murna tamike tai daki tana fadin to Alh yau kuma ziyara zamu fita Kenan

Cikin shiri sosai ta fito tana kiran Bilal dake dakinsa yana home work
Da gudu yafito mom gani fa home work nakeyi

Je maza ka dauko takalmanka zamuje gidansu Ameera kagansu ko .tsalle yayi yashige dakinsa don dauko takalmanshi

Alh da kansa yake driving motan suna tafe suna hira abinsu. Har suka shiga gate din gdn dake kuntau .

Bayan angaggaisa sunsha lemo da cake din da aka kawomisu
Bilal yafice wajan yaran gidan
Hjy halima ta dubi kanwarta Hjy Amina tace
Ameena tsawon shekarunku da aure kin taba k awo karar mijinki. Akan wani Abu da yaimiki Mara dadi
Ko kintaba kamashi da wani lefi

A a yaya tsawon zamanmu da Alh bai taba batamin ba da sani ko .amma wani Abune ya faru ?
Um um ba abinda yafaru daman inason kiyi amfani da wannan damar kiyiwa mijinki biyayya bisa uzurin da zai zo miki dashi ayanzu

Ameena ta kira muryanta cikin murya me taushi tace mijinki zai kara aure nanda sati me zuwa badon kingaza ba sai don haka kaddararsa tazo kiyi hakuri ki kwantar. Da hankalinki ku zauna lfy

Cikin tsananin. Firgici tace aure kuma yaya Alh da gaske kishiya zakamin .

Sabida bana haihuwa. Shine zakayi. Aure shin dama ba gaske kakeba da kace Bilal ya ishemu rayuwa har karshen rayuwarmu
Ta karashe. Maganar. Cikin matsanancin kuka.

Ba Wanda ya tanka mata saida tai mai isarta. Sannan. Ta dago kanta. Tace wa zaka aura a ina take

Kafin yai magana hjy halima. Tace hadiza. Zai aura yarinyar dake. Miki. Aiki

Wata razananniyar. Kara. Ta. Saki tana. Wayyo. Allah na shiga uku. Ni aminatu. Wannan wace irin masifa CE take. Tun karo rayuwata. Hadiza yarinyar. Dana dauka. Tamkar kanwa. Na gyara. Rayuwarta ta. Dawo mutum. Shine ta yaudareni ta gaye taje zata. Aure min miji
Dik wannan maganar. Tanayi ne ckn kuka da ihu

Tsawa. Hjy ta sakar mata .ke baki da hankali. Ne wanne hauka ne wannan. Daga. Maganar. Aure zaki. Tashi. Hankalinki. Saikace Mara tinani

Wayyo Allah. Yaya yanzu bazaki. Tausayaminba. Bayansa. Zaki bi kina. Ganin yaci amanata. Zaiyi. Auran cin amana dame aikina. Wayyo ni Amina nayi bakin ciki da danasanin daukar. Hadiza a mai aikina

Da ido hjy halima taiwa Alh magana daya fita

Mikewa yai yafice. Zuciyarsa fal kunci yanajin bakin cikin kukan da matarsa take sabida shi
Yana shirin fita yahadu da Amira ta sunkoto Bilal wai yayi. Bacci karbarsa yai yasashi akafada yaje ya bude mota ya kwantar dashi .shima yashiga yazauna kusan 30min yana zaune hjy Amina ta fito fiskar nan ba faraa ido yai jajir sabida kuka

Gaba ya budemata amma saita. Shige. Baya kusa da Bilal

Baice mata komaiba. Yaja motar suka. Tafi har. Sikaje. Gida ba Wanda. Ya ce uffan suna Shiga. Ta shige dakinta shikuma yakai Bilal ya kwantar

Dakinsa ya shige yai sallah ya Dade yana addua Allah yasa aurannan yazama Alkairi agareshi. Daga bisani yashafa .yakwanta
Don baison zuwa wajanta yanzu yaga ta dau zafi sai zuwa gobe tukun

Itakuwa hjy Amina tana gado sai juyi take a gado tana kuka hakika nasihar da yayarta tai. Mata. Ta ratsata. Amma shikenan. Haka tana gani mijinta. Zai auri me aikinta. Haka taita saka da warwara har bacci ya kwasheta

 Abangaran masu aiki suna da tarin yawa. Sabida abincin  sadaka da akeyi.  Kullum Yasa masu aikin yawa tsofaffi da yaran mata dik  cikinsu hazida ce  kadai budurwa don hakama hajiya ta ware mata dakinta ita kadai acikinsu . wanda sauran suke mutum biyar biyar adakinsu 

Dik cikin masu aikin Hadiza jininsu yafi haduwa da wata dattijuwa iya Abu macece me kirki sosai don sauran masu aikin haushin hadiza sukeji yanda hjy take kula da ita sosai take fifitata akan.su

Yau tunda ta tashi takejin faduwar gaba  don hakama bata shiga cikin gidan da wuri ba sai sha daya na rana  tashiga gun hajiyar da sallamarta  shiru ba Wanda ya amsa kai tsaye kitchen ta shige  don shirya abincin rana  ta fara harhada abinda zatai amfani dashi .taji muryar Alh yana fadin  Hadiza da sauri ta juya   tare da tsugunnwa tana fadun  Alh ina kwana  

Da fara arsa ya amsa yace tashi tsaye dama magana nakeso muyi
Rawa jikinta ya dauka tace to Alh .yakai minti biyu yana kallanta sannan yace hadiza zaki iya aurena

Da sauri ta gado ta dubeshi tana ja da baya tare da rufe bakinta da hannu don kuka ya kubce mata
Bai damu da yanayin da tashigaba yace hadiza ki shirya aurena nanda Dan lokaci don hajiya ta ban tarihinki dika .don haka tausayinki Yakama ni inason auranki don in inganta rayuwarki kinji karkiji tsoro ko shakkar wani ab… …….
Bai karsaba daga bayanshi yaji ance andaiji kunya wlh girma ya fadi rakumi ya shanye ruwan yan tsaki
Ke kuma munafika zo ki ficemin daga kitchen al gumguma .inna kara ganinki a sashinnan saina karyaki maci amana .
Jiki na rawa hadiza tabi ta kofar baya ta fice .tana rusa kuka cikin tashin hankali tayi bangaransu
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEM

            ????

Bata tsayaba saida ta dangana da dakinta tana shiga ta fada kan katifarta tana gursheken kuka
Iya Abu ce tashigo ta zauna gefan katifar tana fadin haba hadiza me yafaru kike wannan gursheke sai kace wadda ake zarewa rai tashi maza ki daina haka gashi can kinsa makiyanki dariya sunata murna yau sunga kukanki

Ajiyar zuciya tai tamike zaune .
Yauwa ko kefa yata share hawayanki ki fadamin damuwarki insha Allah zan share hawayanki .

Cikin inda inda ta fadawa iya Abu komai ita ma abin ya girmameta tagumi ta rafka daga bisani tace ki kwantar da hankalinki hadiza shi aure da kike gani nufin Allah ne inya tsara ke me dakice ga Wanga me gida tofa ba makawa saiya aureki koda kuwa kina garinku ne

Don haka ki sawa zuciyarki nutsuwa .ki mika lamarinki ga Allah zai isarmiki
Ammafa hakika wanga batu batu da girma yake um um um ni zainabu shikuwa Alh. Banda Abu nashi yana zamansa lfy da matarhi zaizo da wannan batu .

To Amma aishi komai nufin Allah ne .
Kuma abinda nakeso dake kija bakinki kiyi shiru akan maganar har muga yanda Allah zaiyi.

Da yamma hjy Amina ta Tara dika maaikatan gidan mata  banda Hadiza don ita tanacan zazzabi ya rufeta .

Ta kare musu kallo can ta samo me Dan tsafta kuma bazata wuce shekaru talatinba bazawara ce barira sunanta
Tace ke daga yau nayi canjin hadiza dake .kezaki rika tayani aikin bangaran girkin Alh. Kuma kije kicemata nace ta kwashe kayanta ta mayar makwancinki ke kuma ki koma dakinta

Tofa abin nema yasamu gun Barira jiki na rawa tashiga kwarara godiya gun hjy. Ai tana cewa su tafi ta mike ita da mukarrabanta sukai dakin hadiza suna to afito yau yar lele ta tafka lefi .wayasani ma ko sata tama wash kuma na fadin
kila asiri datakewa hjyn ne ya karye .shewa suke sosai sina fitar mata kayanta daga dakin.iya Abuce ta tsaidasu cikin bakin cikin maganganunsu tace haba Ku kuwa kamar kafirai Baku da imani ko kadan kuna ganin yarinyar cikin ciwo amma kunzo kuna mata watsi da Kaya.
Tattare Kayan tai akai dakinsu .gefan kayanta ta ajiye sannan taje ta kamota ta kwantar da ita atabarmarta tana bata hakuri .
Itadai aikin kuka kawai takeyi
Da dare Mlm haruna direban cafane yazo yakira iya Abu yace .Alh.ne yace inshaida miki ki kamo hadiza kuzo in kaiku asibiti a dubata .ancemai batada lfy.
Daga asibiti kai tsaye gdn Mlm Khalil direba yayi dasu nan iya tabar hadiza ita aka dawo da ita gida .
Don Alhj yace abarta
anan har sai andaura aure sai akawota dakinta .

????????????????????????????

[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button