BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

7⃣5⃣
Hhhhhmmmmm su Baby fa ba saban ba anshi ga duniyar masoya sai wani lumshe ido akeyi ana juyi akan gado,kamar ance ta bud’e ido karaf suka had’a da Islam dummm gabanta ya fad’i don tasan isy taji dik hiranta da Nabeel, kauda Kai tai ta juya baya”sister”Islam ta kirata ahankali,
“Na am”ta amsa ba tare da ta juyo bay,
“Sis nah ki jiyo magana nake so muyi me mahimmanci”
Batace komai ba ta mik’e zaune tare da jingina bayanta jikin gadon ta sa fillow a k’irjinta ta zubawa Islam ido alamar ke nake sauraro,
Itama gyara zamanta tai tana fuskantar babyn tare da rik’o hannayenta ta sark’e cikin nata,
“Sis a wane matsayi kika d’auke ni”?
“Ban gane ba sis ai kinfi kowa sanin matsayinki guna”
“Um um da dai nasani amma yanzu ina da ko kwanto akai”
“Islam ke d’in y’ar uwa tace wadda ban da kamarki dik duniya, ke ce abokiyar wasa na lokacin k’uruciya, sis ke wani sashi ce ta zuciyata, bani da wata k’awa data fiki kece y’ar uwata kuma aminiyata,ke kikafi kowa sona cikin y’an uwana, kece abokiyar shawarata kuma abokiyar sirrina ke . . . . “
Zata k’ara magana Islam ta d’aga hannunta alamar dakatar da ita tana fad’in
” baby na yarda da dik zan tukanki amma banda na k’arshe biki d’aukeni abokiyar shawara da sirrinki ba, da haka ne da biki b’oye min abin dake tsaka ninki da ya Nabeel ba, Baby tunda dad’ewa na lura da takunku da Nabeel amma kika b’oyemin bayan kin San zanfi kowa farin ciki da hakan, why sweety?”
Ruk’o hannayenta tai ta matso kusa da ita sosai tana fad’in”haba mana my sis kinsan bazan Tab’a canja ki da wani matsayi ba bayan wanda kike kai ke d’in ta dabance,you are very special to me,”.
Gyad’a kai tai tace ” is ok nd apology accepted, to amma ki fad’a min meyasa kika b’oye min”
" isy wlh ina jin kunya ne kuma ina tsoron mami ta sani sabida kin San dokanta akanmu kar tace na fara karya mata doka, don haka nace mishi yayi shiru da maga nan sai zuwa wani lokaci"
“Hhhhhhhh sis waye yace miki soyayya yana b’uya, wa yace miki ana iya b’oye so? To tun sanda kika fara son ya Nabeel na gane har shi d’inma ina kula wai sai ya faki idona ya rink’a aika miki kallon k’auna tare da manyan kalamai amma wai Ku dik baku yarda son juna kuke ba”.
Duka baby ta kaima ta tace”to sannu jasus sarkin sa ido wato kina nan kin matsa gefe kina kallonmu”
“To ai abinda biki sani ba har sis Aisha tasan da haka dik zuba muku ido kawai mukai muga iya gudun ruwanku”
Dariya Baby tai tace” oh sister isy ke ko hhhmmm . . . yanzu ya kike ganin za’ayi da mami?”
"Ki fad'a mai kawai ya b'oye soyayyanki ga mami har zuwa ki gama 300 level sai ya fasa kowa yaji kinga ko dai baiko dasa rana akai zaiyi dai dai in kin gama sai ayi auran naku k'un biya k'un biya ya k'are"ta k'arasa da tsokana,
Mirmishi tai tace”sis bana tunanin zan iya kaiwa wannan lokacin ba tare da ya Nabeel ba yanda nakejin zuciya na bazan iya kaiwa ko 1 year banyi aure ba”
Zaro ido Islam tai cikin tsananin mamaki tace”ya ila’hi! sis kin lalace wai har kina so kice min aure kike so amiki yanzu? Sabida kin d’an d’ani zakin soyayya shine kike so amiki aure kije kiji sauran soyayyan ko?”
A yanda take maga nan yasa baby tun tsirewa da dariya tana fad’in”wai mamaki na baki isy? To meye abin mamaki karfa kimanta shekaru na sunkai matsayin da zan buk’aci hakan musamman in kikai la’a kari da wanda zan aura 0ne in town, hhhmmm hausawa nacewa abari ya huce shike kawo da Rabon wani, k’ara tun kan wata ta kwace minshi in maza in aure abuna”.
Sosai Islam ke shan mamakin sauyin da Baby tayi lokaci kad’an, Baby da maga nan wani namiji be gabanta Baby data tsani tarayya da maza bata shiga sabgarsu dik yanda take da namiji ko d’an uwanta hira me tsayi bai had’asu amma shine yanzu har take fad’in wai aure take so,hhhhhh lalle soyayya sai abarta da gani an dank’i Baby da k’arfi a kotun so.
Duka Baby ta kaimata a cinya ganin ta fad’a tinani tace”ke uban me kike tinani kika bud’e baki kamar yawu zai zubo? Kawai don dik nace ina son aure kike wannan tunanin to zauna ke kar kiso abarki abaya.ta k’arasa tana wa Islam gwalo da dariya.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:26 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????
7⃣6⃣
To haka rayuwa taci gaba da gan garawa soyayyar khausar da Nabeel koda yaushe k’ara girma take, amma a b’oye don baby taja masa kunne da babbar mirya akan karya sake ya sanar da wani don lokacin Sanar da duniya baiyi ba,
Su dai Islam da Aisha tinda sun Riga da sun San komai ba'a b'oye musu agabansu ake rak'a shewa asha k'auna ba'a ko kunyar su ,
Ahaka ranar da sirrin zai tonu rikicin soyayya ya b'alle tsaka nin su yazo gidan da yamma mami taje unguwa suna cikin hira wata course mate d'insa ta kirashi a waya sukaita hira wajan 5 minutes sannan sukai sallama yana kallon Baby yaga ta had'e rai tasha mur kawai sai dariya ta kamashi ai kuwa tana ganin ya fara dariyan ta kunce da kuka hawaye Biyu biyu a fuskanta, ganin hawayen yasa ya koma serious yana fuskantar ta yace
“Baby nah me yai zafi haka mene abin hawaye daga na d’aga waya wlh ba abinda ke tsaka nina da ita sai mutinci y’ar gana ce tare mukai karatu da ita a London, ki yarda dani baby pls”
Ko kallo be isheta ba saima tsanantawa datai cikin kukanta ta d’ora kanta bisa cinyarta,
“To fa k’aramin Abu ya zama babba”
ya fad’i cikin kid’ima
D’aga muryanshi yai ya kira Islam dake d’akinsu na k’asa da sauri ta fito jin kiran da yake mata tace
” gani meya faru yaya?”
“Islam tai maka min dubi Baby daga na d’aga wayan wata friend d’ina data kirani shine take kuka”
Mai makon yaga islam ta baiwa Baby hak’uri kawai saita k’yal k’yale da dariya tana fad’in “ah wannan fad’anku ne irin na masoya dik wanda ya shiga shi zaisha kunya rarrashi abarkay,nima in fad’anmu ya had’o mu ni nake rarrashin kayata ba wanda ke taya ni, don haka nayi nan”
Ta juya ta koma d’akin,
A k’ufule yace”amma wlh isy baki da kirki amma ba wani Abu”
Tashi yai ya dawo gabanta ya tsugunna tare da rik’o hanna yenta cikin kasa lalliyar mirya me kashe jikin masoyi yace
“Baby nah ki yarda dani wlh Baby ahalin yanzu ba wata y’a mace dake gaba na sai ke ke kad’aice burina kece cikin mafarki na ke nake fatan ki zamo uwar y’ay’a na, baby sirrin zuciyata kece ruhina kece miradin zuciyata,in kikai fishi dani Baby zuciyata zata azabtu bazan yafewa kaina ba wannan hawayen dake zuba a idonki ko wani ne yai sana diyar zubar hawa yenki bazan yafe mishi ba balle kuma ni da kaina, kin sani kema ke d’in bugawar numfashi nace Allah bai tab’a jarabtata da son wani Abu ba sama da sonki Baby ki yafe min kinji my . . . . .
Bai rufe baki ba yaji takun hawa bene yana d'aga kai yaga mami ce ke hawa Ashe ta dad'e tsaye Kansu tun shigowarta take sallama busu jiba harta gaji ta wuce ta barsu, ya d'anji fad'uwar gaba amma dake daman so yake ta sani sai yai mirmishi ya dawo da dubansa ga babyn yace
“Kinga kin k’i hak’ura gashi har mami ta dawo ta same mu a haka kinga yanzu sirrinmu ya fallasa”,
Da sauri ta d’ago kanta idonta cike da hawaya tace”don Allah da gaske”?
“Wlh da gaske nake yanzun tai stairs ni takun takalminta ne ma ya ankarar dani ina d’aga kai naga itace”
“Inna lillahi was inna ilaihi ra’jiun, ya zanyi yanzu mami ta San na karya mata doka na fara soyayya a lokacin da bata bamu dama ba, yanzu ya zanyi yayana”?
“Ki kwantar da hankalinki nasan dabararr da zanyi ba zata gane meke tsaka ninmu ba.
“Allah da gaske?”
“Eh da gaske mana”
Turo baki gaba tai cikin shawagab’a tace”to ka tashi mana karta kuma sakkowa ta ganka haka”
“Um um ni bazan tashi ba sai kince kin hak’ura kin daina fishin”
“Um na hak’ura ka tashi don Allah”
Mik’ewa yai ya zauna kan kujera ya zuba mata ido cikin kallon so da k’auna yace
” bari in wuce gida baby nah”
Mik’ewa tai da niyar yimai rakiya suka jera zuwa bakin gate suna d’an Hiransu kamar basu ba,
Sai da ya tada motan sannan ta juyo gida,
Gun Islam tai kai tsaye cikin fargaba Islam ta kalleta tace
“masoya ya akai na ganki kamar a firgice?”
"Sis bari kawai mami fa ta dawo, kuma ina kyautata zaton yau sirinmu ya tonu don ta sami yaya tsugunne a gabana"
“Ke baza ta gane komai ba kawai donta ganshi tsugunne gabanki sai ta d’auka wani abunne? Kawai zata d’auka tsokanarki yake tinda tasan tsoka nan yaya”.
Ajiyan zuciya tai sai yanzun hankalinta ya d’an k’ara kwanciya tace”to zo muje mata sannu da zuwa”
Mami kasan cewarta wayayyiyar mace yasa da suka zo mata sannu da zuwa bata nuna komaiba da fara anta ta amsa tana ce musu “hajiya tana gaishe ku”