BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Muna amsawa ya su khadija”
“dik lafiya na baro su”
Baby dai hankalinta bai gama kwanciya ba saida taga sun dawo d’aki mami bata nuna komai ba sannan ta kwantar da hankalinta sosai.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:26 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????✍????????????
7⃣7⃣
Nabeel bayan ya koma gida ana sallar isha’I yabi Abbansu sashinsa bayan sun zauna ya dube shi yace”Nabeel ya akai ne naga alamar akwai magana a bakinka”
D’an mirmishi yai gami da Sosa k’eya yace “Abba dama maganar KHAUSAR nake son maka”
“Wace KHAUSAR d’in”?
Ya tanbayeshi
“KHAUSAR dai ta gidan mami”
“Ok meya faru da ita”?
“Daman Abba min dai daita kanmu ne a tun tini nace zan Sanar dakai kayiwa Dadyn ta magana asan da zan can shine ta k’i yarda wai sabida mami tasa musu dokan kula wani sai sun gama karatunsu dika, to ahaka dai Mike ta b’oye zan can kar mamin taji to yau kuma mamin ta sani shine nake gudun karta hana ta ci gab da kulani”,
Abba wanda tun fara maganar Nabeel bakinsa yaki rufuwa da fara’a yace”ah karka damu zanwa sadiyan magana manya su shiga zancan, ai tunda dik gida ne me za’a jira ai tunda kun fiskanci juna kawai zanwa AA Abdallahn magana sai ayi komai a huta maganar makaranta saita k’arasa a gidanka”.
Wata irin fara’ace ta kamashi ya k’ara k’asa da Kansa”Godiya nake Abba Allah ya k’ara girma yaja da rai”
“Karka damu Nabeel ai ni naji dad’in wannan lamari Allah yai muku albarka ya k’ara had’a kanku, tashi kaje abinka”
Da kwarin gwiyarsa ya tashi ya koma b’an garansa,
To a gida dai mami ta shiga tinani yaushe Baby tayi wayon da zata fara soyayya haka bata Sanar da ita ba ita da yaranta basa b’oye mata komai nasu dik abinda ya dame su ita ce ta farko da suke fara sanarwa amna gashi yanzu sun had’e kai sun b’oye mata, can kuma wani tinanin ya zo zuciyarta to ko tana gudun Karta sanar da ita ne ta hanata,? Mirmishi kawai tai taci gaba harkar gabanta.
Washe gari da safe Abban Nabeel kuma yayan mami ya kira ta a waya inta samu lokaci tazo gida yana son magana da ita,
Tana kashe wayan take fad’awa Dad daman tana kusa dashi,
Yace”to in kin tashi daga aiki sai ki biya”
Haka kuwa akayi da wuri ta bar asibitinta zuwa gidan yayan nata dake na’ibawa by past, bayan sun gaisa da ummy (maman su Nabeel) suka shiga hira aka kawo mata abinci taci sannan ta k’arasa ga sashin Abban,
Bayan sun gaisa suka d’an tab’a hira irin ta wan daya shak’u da k’anwarsa, daga bisani ya gyara zama yace
“Sadiya jiya Nabeel yazo min da batun khausar akan suna soyayya sun fahimci juna tun tuni yaso ya Sanar da manya ashiga lamarin amma ita Baby ta hanashi sabida bata so ki sani don kin haramta musu soyayya har sai sun kammala karatu, shin me yasa Sadiya zaki kafawa yaranki mata wannan dokar, dik da nima ina da wannan ra’ayin amma ai kinga in har mutum ya amince Yarinya taci gaba da karatun ta agidanshi ai ina ganin ba wata Matsala ko?”
Mirmishi tai kana tace”yaya wannan dokar na kafa musu ita ne sabida na fiskanci yanda samari sukai Cha akan su tun suna secondary to kaga inna kyalesu zasu iya kawo min shirme, amma kaga ai ko yanzu daman suka sami manemi zan basu dama koda kuwa a waje ne to balle kuma Nabeel wanda koshi yana da damar kawo wani amatsayin ma nemi auransu balle shi da kansa, don haka yaya na amince d’ari bisa d’ari kuma naji d’ad’i nai murna da Allah ya had’a baby da miji kamar Nabeel, don haka yaya kayiwa Dadyn nata magana sai asa lokaci kawai ayi bikin”.
"To masha Allah Allah ya k'ara had'a kan zuriyar mu"
Mami ta amsa da “Ameen”
Night
Mami tana zaune a d’akinta ta d’aga wayanta ta kira Baby tace Ku shigo d’aki keda Islam ina jiranku”
Dam baby taji gabanta ya fa’di don tasan kiran nata ne.
Bayan sun zauna ta dubesu da y’ar dariya tace”oh yara na sun girma har sun San su b’oye min wata magana data shafesu”
D’agowa sukai a tare suka kalleta sannan suka maida Kansu k’asa don sun San inda zancen ya nufa.
“Ya kukai shiru um y’an Matan mami?”
Islam ce tace “mami indai muna tare da ke ai baza mu tab’a girma ba kuma bazamu b’oye miki komai namu ba”
Dariya mami tai tace”to ba gashi kun b’oye min zan can Nabeel ba”
“Mami sister ce bata so ki sani don karkiyi fad’an ta karya miki doka”
“To ai yanzu kun Kai lokacin da nake so kuje kafin Ku sa kanku cikin rikicin soyayya, don yanzu kara tunku yayi nisa kuma kunyi hankali nasan dik inda kukaje yanzu baza Ku ban kunya ba,don haka baby karki damu d’azu naje gida munyi magana da yaya na manya zasu shiga maga na, kuje Allah yai muku albarka zanje wajen Dad d’inku”.
Suna shiga d’akinsu Islam tai tsalle ta run gume Baby tana fad’in”yeeee sis nah magana dai ta fito kowa yasani yanzu sai ayi Soyayya me y’anci abar b’oye b’oye”,
ita dai Baby mirmishi kawai take tana jin wani farin ciki yana ratsa zuciyarta.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:28 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
7⃣8⃣
Kamar yanda Abban Nabeel ya fad’a yazo ya sami Dad ya sanar dashi abinda ake ciki dik da kafin zuwanshi daman mami ta mai baya nin komai, yayi farin ciki yayi murna dik da akwai wani k’udiri aransa amma hakan bai hana shi farin ciki ba don yasan Nabeel yaro ne na gari me cikar kamala wanda yasan bazai bar baby cikin wani hali ba kuma ko ba komai Nabeel d’an Ami ninsa ne kuma d’an wan matarsa don haka had’in yayi dad’i.
To an tsaida loka cin biki inta kammala 300 level kafin ta wuce 400 nanda wata biyar Kenan, lokacin da zan can yazo kunnan baby ta rasa a wane hali take farin ciki ko akasin haka shin ana nufin nan da 5 months zata bar gidansu tabar Dadyn ta da maminta ta bar y’ar uwarta Islam tana wannan tinanin ta fashe da kuka tun Islam na tsokanarta har itama jikinta yai sanyi ta shiga rarrashin ta amma tak’iyin shiru don haka taje ta fad’awa mami,
Mami data shigo taga irin kukan da take sai abinma ya bata mamaki ta sami waje ta zauna bakin gadon ta d’ago fuskarta dake cikin pillow tace” Baby meke faruwa me yasa ki kuka haka um?”
Mai makon ta tsagaita kukan a a saita kuma tsanantawa tare da rungume mami k’am ta cusa kanta a jikinta,
Shafa kanta mami ta shiga yi tana d’an biga bayanta kamar wata k’aramar Yarinya,
Saida taji tayi shiru tana ta sauke ajiyan zuciya sannan ta kuma cewa" me yasaki kuka haka BABY?"
Cikin shagwab’anta tace”mami me yasa zaku min aure yanzu ko kun gaji da nine?”
D’an mirmishi mami tai kana tace”to mene ne Baby don ansa miki ranar aure kawai sai ki fara kuka haka, inma ba aimiki aure yanzu ba dole in ana raye wata rana za’a miki, to yanzu tunda kina sonsa yana sonki ai sai amuku ko? Karki damu kinji Baby dikkan matar da kika ganta cikin gidan mijinta ta shiga irin wannan rud’anin loka cin da aka fara mata maganar aure, don haka karki damu ki kwantar da hankalinki kinji, bashi da wani anfani aita tsawaita lokacin aure in dai ba da wani dalili ba, kinga kuwa mu ai Alhamdulillah bamu da bu’ar tsayawa Tara wani Abu don za muyi miki aure komai muna dashi Alhamdulillah don haka ba wani Matsala ki share hawa yenki ki kwantar da hankalinki kinji Baby nah”.
Gyad'a kai ta shiga yi tana goge y'ar sauran kwallar tata,
Mami na fita Islam ta kalleta tace oh baby kamar bake ce kece min aure kike so ba amma kuma an fara maganar auran zaki fara ma mutane kuka,