BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Harara ta wulla mata ta maida kanta ga pillow anan barci ya d’auketa.

Washe gari suna zuwa skul Islam ta zayya nawa Aisha zan can,ai kuwa tayi murna tace

 "wai sis nah zata zama amarya anma nai murna Allah ya kaimu lokacin mu rak'ashe  Musha bidiri,

Dik abinda suke Baby dai bata tanka musu ba don ita dik jikinta ya mutu gashi wani haushin Nabeel take ji don haka tak’i d’aga wayansa yai mata TeX yafi nawa Anma ba replay,

Bayan sun dawo gida wajan k’arfe 5:00 ta shige d’aki tana kunna wayanta taga wasu tex d’in nashi suna ta k’ara shigowa kamar an kunna fanfo dik na ban hak’uri ne ta taimaka ta d’aga wayanshi, ji tai tausayinshi ya kamata, amma kawai sai ta tashi ta shige wanka abinta data fito d’aure da towel ta zauna bakin gado taji wani kiran nashi ya kuma shigowa kallon wayan tai na d’an second ni, can ta d’aga bats bari taji dame zai fara ba ita ta fara

“Me yasa zakamin haka? meyasa zaka karya min tsarin rayuwata? da nasan haka zakamin da ban amince da soyayyanka ba tunda fari, kawai daga fara soyayya sai asamin ranar aure kamar an gaji ne dani kuma ba kowa yajamin hakan ba sai kai, To na fasa soyayyan na kaje ka fad’awa su Dad na jany . . . . .

Da sauri ya katse ta “haba mana BABY na haba kiyi shiru haka don Allah, me yasa zaki min haka kin San dai bayan so ba abinda zai kawo maganar aure khausar wai shin kin San iri son da nake miki kin San yanda zuciyata take min bugu adik sanda ban kusa dake?ya dace ki tausayawa soyayya ta da zuciyana baby . . . kinsan bazanyi abinda zai cutar dake ba ina sonki Ina sonki baby na so me tsanani “.

Ya k’arasa zancan da sauke ajiyan zuciya Me nauyin gaske,

Jitai dik jikinta ya mutu zuciyanta tai sanyi ahankali tace” yayana to ba Kaine kasa za’amin aure yanzu ba kuma bayan dik gasu sis Aisha da isy ba ai musu ba”

“Karki damu suma in lokacinsu yayi zaa musu”

“Um hmmm”

“Sweetheart! 2 days dai rigima kike “

“Ni bana rigima ka kashe wayan zanje wajen mami na”

“To sai da dare zamuyi waya bye”

D'akin mami ta shiga,bata ciki don haka ta haye gadon ta kwanta bayan kusan 5 minutes mami ta shigo ganinta a kwance yasa tace"a a Baby ya na ganki kwance ana kiran sallah ko kina up?"

“Um mami gashi ma cikina ya fara kimin alluran yanzu”

“Ok bari muyi sallah sai in miki wannan ciwon maran naki Baby sai yayi kamar ya tafi sai kuma ya dawo, sannu kinji”

 Tunda aka mata alluran bacci ya dauketa bata farka ba sai wajan goma na dare, tana tashi taji ciwon ya mata sauk'i wayanta Tajawo taga miss Call d'in Nabeel daman tasan za'ai hakan danna kiransa tai ringing d'aya ya d'aga yana cewa"ina kika shiga ne my precious ?"

“Yayana ban jin dad’i ne wlh mami tamin allura shine bacci ya d’auke ni”

“Subhanallah, meke damunki precious?”

” cikin shagwab’anta tace” cikina ke ciwo fa”

‘Kai wai wannan ciwon cikin bazai hakura ya barmin ke ba,ko da ai very soon zan raba ki dashi insha Allah”

Sarai tasan me yake nufi sai tace”kana da maganin sane? Amma ka barni da ciwo haka yayana”

“Hhhmmmm Niko nake da maganinsa Baby sai dai yai nisa”

” a ina yake da yai Nisan”

“Yana gareni amma dik da haka baza ki tab’a samun sa ba yanzu”

“To me yasa bazan samu ba bayan Kuma yanzu nafi buk’atarsa”

” hhmmmm tunda biki gane ba bari in miki gwari gwari”

Jin ya fara k’ok’arin sakin layi yasa tace “a a bar baya ninka na gane zan kwanta sai da safe”

“Ok sannu Allah ya k’ara miki lafiya me d’orewa”

“Ameen na gode my hubby good night and sweet dreams”.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:28 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

WANNAN SHAFIN TUKUCI NE GAREKU MASOYAN BABY KHAUSAR
AISHA A.TAHIR (MAMMY AA.T)
UMMY KATSINA (MMN MUHD)
MAMAN YASMEEN
AMINA NASIR
HAFSAT
MMN NAWAF
HAfSANAN????????.A
KADY
RAMLERT

 DA DIKKAN WAY'ANDA MA BAN FAD'I BA INA GAISHEKU???? MUNA HAD'E IRIN MATUK'AR GAISUWAR NAN????????.





       7⃣9⃣

Cikin satin suka je kasuwa suyo Ankon bikin hafsa y’ar yayan Baban Islam wanda za’ayi a katsina sun d’ora buri kan zuwa bikin nan don haka har zuwa sukai suka sami maman Aisha akan ta barta su tafi bikin tare in lokacin yayi ai kuwa ba gardama ta amince musu,

Agidan su Nabeel ma harda Nabeela da z’a tafi don haka Nabeel yace shi zai kaisu kar ahad’asu da driver,

Ranar Alhamis za’ayi dinner ran jummaa daurin Aure sai asabar ayi yini don haka tun laraba sukaje Sabon gari aka musu gyaran kai da kunshi, ran alhamis sun so tafiya tun safe amma sabida kar suyi missing lecture da yawa yasa suka shiga skul sai biyu suka fito kai tsaye gidansu Aisha suka wuce taiwa y’an gidansu sallama sannan suka yo gida, anan ma a gurguje suka watsa ruwa Suna shirin cin abinci motan Nabeel ta iso shida Nabeela don haka sama sama suka ci sika fito mami tai musu rakiya bakin gate, baby ce a gaba sai Islam Aisha da Nabeela a baya kayansu dik a boot,

  Sun fara tafiya a hankali yake tuk'in suna d'an hira Islam tace 
    "yaya Nabeel ka k'ara gudun motan nan miyi mije,ka ga fa k'arfe 7:00 zaayi dinner d'innan ya dace ace in munje mu huta kafin mu wuce kaga kuma fa sai munje wajan kwalliya ko anan zamuyi kusan 2 hours kafin agama mana kuma yanzun uku fa",

Ta cikin glass ya kalleta yace “to sarkin azarb’ab’i ni bana gudu a mota ina tattala rayuwata gani ga mata ta inje in kashe mu in cuci y’ay’an mu”

Dariya sukai gaba d’aya banda Baby ita mirmishi kawai tayi,

Aisha tace” oh su ya Nabeel wato harma kunyi auran kun haifi y’ay’an “

Dariya ya d'anyi hankalinsa naga titi yace

“To Aminiyarmu me yai saura wata hud’u da sati biyu kamar yaune zaki ga munyi auran, kuma munayi wata Tara insha Allah ta haifo mana y’an biyu ko uku kinga ai dika a wata goma sha uku zaayi hakan kamar yaune na zama Dady Baby ta zama mommy”

 Shewa suka saki suka tafa Nabeela tace "um su yaya iyayen k'auna"

Baby wadda tunda ya fara maganar ta kauda kanta zuwa titi tasa hannunta kan bakinta tana mirmishi,

 Kallon ta yai da dariyansa yace "wai me kike kalla a titi kinbar mijinki a gefe?"

Juyo da kan tayi ta kalleshi kallo me tattare da tarin soyayya da k'auna tai k'asa da mirya tace

” haba yaya na baka jin kunyar Nabeela in ka saba yi gaban su Islam ita fa”

Gangarawa yai gefen titi  ya zuba mata ido sannan ya sako da kanshi kusa da fuskanta sosai yace cikin miryan da bamai ji sai ita

“Precious mene abin jin kunya a maganar nan kawai don na fad’i abinda ke raina,ina sonki Baby na dikan lokacin da naji an anbaci sunanki sai bugun zuciya ta ya k’aru kece burina fatana kullum mu kasance cikin inuwa d”aya ki zama mallaki na!”
Lumshe ido tai cikin jin dad’in kalamansa tace ” yaya na nima kai d’aya ne mafarkina a koda yaushe fata na na bud’e ido na ganni kusa da kai . . . “

“Ohh gocchhh yau fa mun biyo iyayen soyayya wai ko kun manta a titi Mike ne kuka had’e kai kuke kus kus kuna soyewa ,abin haushin ma bama jin me kuke fad’a da mun tofa namu gaskiya mu dai a kunna mota muyi gaba”
Um Islam Kenan

Sudai su Nabeela da Aisha dariya kawai suke,

Shiko gogan ko juyowa baiyi ba sunata aikawa junansu tsimamman kallo sai da babyn taga bashi da niyan tashin motan sannan tace

“Yayana mu tafi lokaci fa”

Da sauri ya kunna motan yaja sukaci gaba da tafiya Islam nata musu k’orafi,

Tafiya suke sosai a cikin daji suna wuce k'auyika da dajika suka k'ara so wata kasuwa nan yai farking domin siyan gujjiya donshi masoyinta ne kiran wata Yarinya yai me saida gujjiyan  da gudu ta k'ara so ya zuge glass yace nawa dika farantin? Jim tayi sannan ta tace 

"ban San ko ta nawa bace amma dai gwangwani d'aya sha biyar ce"

Kallon su Islam yai abaya yace “zaku ci ne? In siya daku”

“Dik zamu ci”
Suka ce

Kallon yarinyar yai yacey “yanzu kina ganin kamar zata kai gwangwani nawa dika ta farantin?”

Shiru tai tana k'iyasta yawon ta sannan tace "zata kai gwangwani ashirin"

“Ok to samo babbar Leda guda hud’u kizo”
Da gudu ta juya zuwa wajan wani me tireda ta siyo ledar, tana zuwa yace to “rabata biyu ki zuba aleda biyu biyun kuma bamu mu zuba b’awon”

Yanda ya umarceta haka tayi ta mik’a mai ya karb’a ya mik’wa su isy Leda d’aya baya d’aya ledan kuma ya mik’awa baby yace

” Rik’e mana tamu”

Sannan ya kalli yarinyar yace “yanzu nawa kike so in baki kud’in gujjiyarki da ledar da kika siyo?”

“To ka bada Dari uku da ar’ba’in har ledar”

Mirmishi yai ya zaro 500 ya mik’a mata yace”to gashi canjin kisai irin wannan Jan bakin da kika sa abakinki”

Dariya sukai dikansu ita kuwa yarinyar rufe fuskanta tai tace “an gode” sannan ta d’iba da GU dugu tai gaba, sudai banda dariya ba abinda suke mata.

Suna tafiya baby tana b’are mai tans zuba mai Ahannunshi yana ci, yayi yayi taci tace mai ita bata cin gujjiya kuma bawai bata ci bane kawai taga rashin aji ne taci d’in sai dai ta b’are mai shi yaci,
Suko su Islam suna baya suna watsa tasu.

Tun suna tafiya suna hira cikin kuzari har suka gaji sukai shiru,

Cikin ikon Allah da ni'imarsa suka je garin katsina, kai tsaye gidan su hafsa sukai farking dagudunta ta fito jin Diran motansu don tun suna hanya take ta yo musu waya har suka zo suna kusa da gidan Baby ta kirata tace gamu mun shigo layinku don haka tana jin  diran motan tayo waje rungu mesu tayi tana ta musu barka da zuwa ahaka suka k'arasa cikin gidan , kowa fitowa yai yana musu barka da zuwa aka kaisu masauki shi kuma Nabeel yayan hafsa yaja shi d'akinsa.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
[11/13, 11:28 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button