BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
.
8⃣0⃣
Bayan an saukesu da fura da abinci me rai da lfy sukaci sukai k’at sannan sukai sallah,
Suna zaune aka fara shirin tafiya dinne Nas-yuza make over ita ce ango ya d’auko domin yiwa amar yarshi kwalliya har a gama bikin,
Tunda ta shigo kit d’in Kayan kwalkiyanta kawai Nabeela ta kalla tace” Baby ko dai mu sasanta da me kwalkiyan nan ta mana naji ance daga kano aka d’aukota Donni daman hankali na bai kwanta da kwalliyan da zamu je amana ba ina ganin kamar basu da kwararrun masu kwalliya”
Wata budurwa dake gefansu zaune ce ta dubi Nabeela da mamaki tace” a ina ne ba kwarrarun masu kwalliyan to wlh ke wani wajan make up d’inma in kikaje zaki d’auka a Dubai aka miki, ai ko ina da k’wararru kawai iya kud’inka iya sha’aninka,ko yanzu ma gun kwalliyan zan wuce kuma zaki ga wadda zaamin”
Dariya y’an d’akin suka sa suna fad’in oh khadija dubi yanda kike tada jijiyan wuya kina Kare martabar garunku,
Baby ce tace”sis to ko zamu ragu mutum biyu su je gun make up d’in mutum biyu su zauna Nasyuza tai musu don mufi sauri”
Islam ce ta mik’e tace ai kuwa bari ni da Nabeela muje can d’in ke kuma da sis Aisha sai a muku anan d’in, amma bari mu wuce da kayanmu don ana mana mu saka in mun dawo kwai sai mu tafi”
Kwalliyya akai wa amaryan na d'aukam batu,sannan dik wanda yace tamau in ta fad'a mai farashin kwalliyan shmmm, amma muta nan nawa kanawa ansaba irin wannan sabgar indai aksn ayi ado ne za'a iya b'atar da ko nawa ne don haka baji baby tace ai musu ita da Aisha, nan fa me kwalliya ta k'ara gyara zama ta gwangwaje su dake kuma tana da sauri nan da nan aka gama musu, amma zuwa lokacin dik an tafi gurin dinner sai k'ali lan ne a gidan, Aisha ce tasa waya ta kira Islam tana fad'a musu suyi sauri su dawo su suke jira,
Ankon dinner d’in suka saka wani material ne milk color sai he’d copy color, don haka dik sukai anfani da sauran abu buwan copy danginsu d’an kunne sark’a, takalmiy,post,da d’an nate d’in da suka yafa jiikinsu.
Gayu yayi gayu sai suka zama wasu taurari dik su hud'un babu wadda zaka kalla ka kauda ido, dan ba dama fa,baby ce ta d'aga wayanta ta kira ya Nabeel kan cewa sun shirya,yace su fito.
Tun daga nesa ya zuba mata ido cikin kallon kinyi azababban kyau, asannu suka k'araso da sauri ya bud'e mata gaba ta shiga su kuma sukai bayay,itama zuba mai ido tayi sai taga ya mata kyau matuk'a cikin shigan da yayi sai taga kamalanshi ta k'ara fitowa ga k'asumbar nan ta k'ara fitowa ta cika fiskar cikin gyara, ji tai ya Matso da fiskanshi ya hura mata iska a ido da sauri ta sauke idonta k'asa cikin jin kunya, mirmishi yai yaja motan suka bi motan amarya da ango dake gabansu,
Tunda suka shiga gun dinner din ido yayo Kansu kasancewar sune y’an bayan amarya day sauran k’awayenta da abokan ango,
Bayan amarya ta tsaya afili ita da ango aka sa wak’an bikin nan da nan y’an mata aka shiga cashewa, ana lik’a kud’ad’e, wani abokin ango ya tsaya kan Baby yana ta mata ruwan kud’i ai kuwa tafi yaita tashi jin tafin yai yawa yasa Nabeel d’ago kansa ai kuwa dimmmmm gabansa ya fad’i inba gizo idonsa ke masa ba Baby fa namiji kewa lik’i kama an hankad’oshi haka ya shiga filin ya fizgota suka fita daga cikin hole d’in bakin motansu ya tsaya da ita, idonshi jajur cike da kishi ya kalleta yace
“Me yasa zaki min Haka me yasa zaki tsaya Gabon k’ato yana miki lik’i ?”
Ahankali ta d’ago da idonta ta kalleshi na some seconds sannan tace
“Yayana me zai had’ani da wani namiji a halin yanzu ko ada da banda kai bazan kula wannan ba bare yanzu da Allah ya had’ani da gwarzon namiji irin wannan wanda samun irin sa a duniya dace ne babba ne y’a mace, ni kam yanzu banda wani sauran buri akan wani namiji na sami irin wanda nake fatan samu, one in town”
Ajiyan zuciya zuciya ya sauke,jin kalamanta suka zubawa juna ido cikin so da k'auna k'wayar idonta take sarrafawa cikin tashi tana wani janyesu kamar tana jin bacci dik sai da ta saukar mai da kasala jikinsa ya mutu murus, to ganin yanda dik yana yinsa ya fara canjawa yasa ta kauda idonta daga nashi,
Hannunta dake cikin nasa ta zare a hankali.
“Yaya na gaji da tsaiwar nan mu koma ciki ko mu sami gu mu zauna”
Rik'o hannunta zai k'arayi da sauri ta janye tace muje, kallonta kawai yai ya wuce gaba ta bishi a baya suka show daga baya ya Samar musu waje suka zauna suka ci gaba da shanawa da soyayyansu , ahaka har lokacin tashi yayi suka taho gida.
To haka sukayi kwanakinsu uku a katsina cikin jin dad’i da sha’anin biki wanda b’an garan su Nabeel da Baby sukam gara wasai don soyayya sukaci suka k’oshi abinsu.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
8⃣1⃣
Tun bayan dawo warsu daga katsina ba abinda suka sa agaba kuma sai shirin bikin Baby.
Yaya Nazeef yayan Aisha ya dad'e yana damun Aisha akan yana son Islam amma tak'i bashi had'in Kai sabi da tasan dokar gidansu kullum ya mata magana sai tace"yaya bafa sa kula kowa maminsu ta hana su inma na fad'a mata baza ta yarda ba"
Kullum haka take fad’a mai ai kuwa yana jin labarin ansa bikin Baby yace bai San zance ba kawai Aisha ta bashi number Islam shima ya fara gwada tashi sa’ar, ai kuwa Aisha ta bashi tun daga ranar yashi ga filin yak’in Neman gurbi ga Islam ba dad’ewa Islam ta amince dashi suka k’ulla soyayya suke k’one wa abin su.
Rayuwa taci gaba da tafiya cikin yanayi kala kala Karatunsu yana k'ara zurfi lokacin biki yana k'aratowa ,an fara d'iban mahajjata a k'asarmu a k'asan duniya domin yin aikin hajji, anan gidansu baby Dad,mami, hjyn Bilal dik dasu za'a tashi, yayin da gidansu sis Aisha baza'a bar kowa sai Aisha da k'aramar k'anwarsu 'fadwah' wadda ita ma don bata kai she Karun balaga bane Abban su yace sai wata sheka rar zata je,Ita kuwa Aisha sabida skul ne,
Yanda suka tsara Aisha zata dawo gidansu Baby ne harsu mama su dawo don tafi nutsuwa da karatu, ita kuma fadwah uncle d’insu ya d’auketa zuwa gidanshi dake tishama,
Rana d’aya jirginsu Ya tashi zuwa k’asa me tsarki daga airport sukayo gidansu Baby inda aka kawo musu inna k’anwar baban su mami wato kaka ce wajan su Nabeel da Islam don ta zauna dasu, inna mace ce me hakuri da barkwanci don haka suke son zama da ita ta taho da d’an jikanta na’eem hakan ya k’ara yiwa su Baby dad’i don na’eem yaro ne me wayo da shiga rai yana sasu nishad’i akwai surutu da tanbaya.
Tun tafiyar su Dad kullum Nabeel sai yazo da dare tunda da rana suna skul inyazo sai goma yake tafiya haka zai zauna cikinsu suyi ta hira sai inna ta fara jin bacci zata koma d’akin da aka sauketa ai kuwa yana ganin ta koma zai kori su Islam yace su basu waje to anan kuma zaa shiga Hiran soyayya.
Zaman Aisha a gidansu ba k’aramin shak’uwa ya k’ara musu ba don dik duniya Bayan Dad,mami, Islam. Baby ba mutumin da take so sama da Aisha domin k’awa ce tun ta k’uruciya don haka daban take jinta aranta, shi kuwa Nabeel Kowa yasan gurbin sa don shi soyayyarsa ba iri d’aya ce data kowa ba. Domin dik sanda numfashinta zai buga yana bugawane da tinaninsa aranta tare da shauk’insa,
Tafiyan su mami da sati guda cikin dare cuwon baby ya tashi tun tana daurewa har taji numfashinta na fizga don haka ta shiga anbaton Allah tana juyi, cikin bacci Islam taji salatin ta da sauri ta farka ta kunna fitilan d’akin ai kuwa ganin Baby tai har ta fara kakkafewa , salati taja da matuk’ar k’arfiy tace”Baby cikinne ko me?”
Firgit Aisha ma ta tashi nan suka shiga jijjigata suna kiran sunanta amm ina ba baki sa juya ido kawai take cikin tsananin ciwo, Aisha tace"Islam ki d'auko alluran da ake mata muyi mata karta k'arasa sumewa"
Islam cikin kuka tace “mami tace baza”a mata ba wannan watan alluran ya fara mata yawa “
“To ki kawo tablets abata”
“Shima an hana bata sabida shan da take yi yai yawa zai bata matsala “
“Haba mana Islam to za’a barta da ciwo ne haka jifa yanda jikinta ke rawa”
“Wai sister ya kike magana kamar ke ba likita ba kin San fa matsalar baby sarai”
Dafe kai Aisha tai cikin tausayin halin da Baby ke ciki tace”samo Lipton sis yi sauri”
Da sauri Islam taje kitchen ta debo ruwan zafi a cup sannan tasa Lipton guda biyu cikin ruwan ta kad’a tashigo d’akin da sauri ,sama sama ta d’aga Lipton d’in ya rage zafiy suka d’agata ahankali Aisha ke bata tana d’an kurb’a cikin yanayin ciwo, tasha kamar Rabin kofin ta kife kan gadon tana kuka rik’e da mararta, ahankali ahankali kuma ya fara lafa mata tai lamo, adai dai lokacin aka fara kiran sallar farko suna nan zaune sun rafka tagumi aka kira asiba Sukaje sukai alwala suka tada sallah, tun kan suyi sallama sukaji juyinta tana salati cikin mawu yacin hali kafin suyi sallama ji kake kiff ta fad’o a gadon nan sauri sauri sukai sallama ba batin tsayawa addu’a sukai kanta da gudu harta suma, kukansu ne ya shigo da inna da sauri tana “lafiya y’ay’an nan?”
Ganinsu durk’ushe bakin gadon sun d’ago Baby suna kuka yasa ta fad’in “inna lillahi wa inna ilaihi ra’jiun, me yasa mi khausar d’in ko ciwon nata ne yazo?”
Gyad’a mata kai kawai sukai
Da sauri ta shiga toilet d’in ta taro ruwa a roba tana zuwa ta shiga shafa mata tana tofa mata addua ahankali ta sauke numfashi tare da kiran sunan Allah zuwa can kuma ta fashe da kuka tana kiran “mami na Dady na kuzo karna mutu bayan idonku,wayyo Allah yaya na kana ina kazo gareni in mutm kusa dakai”
Islam ce d’auki wayanta ta kira number d’in ya Nabeel ringing biyu ya d’auka don yana zaune yana Jan casbaha,
” hello Baby nah ya akayi yau soyayyan asuba ce ta motsa”
“Yaya ba ita bace bata da lfy tana ta kiranka”
Da sauri ya mik’e daga zau nan da yake yana fad’in “innalillahi wa inna ilaihi ra’jiun, Islam me yasa meta, ko ciwon cikinne?”