BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Eh tun cikin dare take fama wlh”

“Ina zuwa ganin”

“Amma yaya ya za’ayi mu sami alluran bacci,ko zaka biya asibitin mami ka karb’a mana ayi mata ta samu bacci me tsayi”

“Ok ok Islam bari inje yanzu don Allah ku kula da ita gani nan insha Allah”

30 minutes sune suka kawoshi gidan lokacinma shida da rabi tayi, da sauri ya kira Islam yace”zoki bud’emin k’ofan Nazi”

“Ok gani nan”
Da sassarfa ya hau benan yai sallama ya shiga d’akin har zuwa lokacin kukan take tana juyi a gadon hannunta dank’e cikin na Aisha, bakin gadon ya k’arasa yace”my precious sannu kinji” ahankali ta bud’e idonta ta kalleshi tare da mik’a mai hannunta, rik’o hannun yai ya zauna bakin gadon yana k’ara mata sannu, lumshe idonta kawai tai k’walla na zuba, cikin rauni da rausayin masoyi ya matse hannunta sannan ya kalli Aisha yace “ga alluran barcin kuyi mata”
Kar b’an ledan Aisha tai ta had’a alluran cikin sirinji ,ganinta had’a yasa ya mik’e ya fita falo,
Yana fita Islam ta tai maka mata sukai mata alluran,
Kiranshi Aisha ta lek’a tayi ya shigo yazo ya zauna gefan gadon k’ara ruk’o hannunshi tai tana lumshe ido cikin tsananin azaba, ahankali baccin ya fara d’aukanta kafin me harta yi,

Ganin ta sami baccin yasa ya zame hannunshi cikin nata, sai alokacin yasami damar gaida inna , haka yaita zama har kusan awa guda sannan yace bari yaje gida ya dawo,yai musu sallama ya fice.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION ????????????????????????????????????✍

             8⃣3⃣

Bayan sallar la’asar su
ummy suka zo tare da Nabeela ,salma da saleema sai Abdussalam daya tuk’osu a motar, har cikin d’akin Islam tai musu iso, a kunyace Baby ta gaida ummy ita kuwa ummy kasancewarta wayayyiyar mace yasa ta zauna kusa da Baby ta ruk’o hannunta tana mata sannu,
Abdussalam ne yazo bakin gadon yana cewa”Aunty na ina yini ya jikin?”

Hara ranshi tai cikin wasa tace “bana amsawa in baza ka fad’i suna na ba”

Dariya yai yana m jijga kai yake yace”wlj ban isa ba yanzu in fad’i sunanki, indai zance ya Nabeel dole kema ince miki Aunty”
Dakuwa ummy tai mai tace” uban surutu tana fama da kanta zaka zo ka dameta da magana”

Ficewa yai da sauri yana dariya ya koma parlour ya zauna wajan inna suka fara hira

Dik su salma suka mata ya jiki ta amsa,

Ummy ce tace ” Baby kinci abinci kuwa?”

Caraf Islam tace” wlh ummy bataci komai tun d’an kunun da ya Nabeel ya kawo mata tasha kad’an har yanzu bata k’ara komai ba”

“Ke saleema bud’e cooler d’in nan ki zubo mata wai nan shinkafan ai zaki ci ko?nasan kina sonta sosai”

Don kawai bata son yiwa ummy musu yasa tace” zata ci”

Da aka zubo mata wai nan a dole ta fara ci amma data ji miyan ansa (ya’kuwa) tayi d’an tsami tsami sai taji dad’inta sosai don haka daga cin guda d’aya taci har uku , ummy taji dad’i ganin taci da yawa, sai wajan magriba sukai musu sallama suka tafi inna tana Taiwa su salma tsiya,

Ana idar da sallar magriba ya Nabeel ya shigo hannunshi d’auke da ledoji guda uku manya ,daya shigo ba kowa a palourn dik sun shiga sallah yai knocking d’akin nasu Aisha ta taso ta bud’e hannunta rik’e da casbaha da alama azkar take batace komaiba ta koma kan prayer mate d’in ta zauna ita kuwa Islam bata ma idar da sallanba,

Bakin gadon yazo ya tsugunna tana zaune ta zubo k’afa funta k’asa tana danna wayanta, hannayensa ya had’e guri guda alamar ban hak’uri , mirmishi tai tace”sannu da zuwa ya aiki”

“Yawwa sannu ya jikin naki ,kin ganni sai yanzu ko wlh bak’in namu ne basu tafi da wuri ba muna ta biga lissafi don Kayan da yawa ,kuma lokacin da suka tafi na taho traffic ya tare ni sai yanzu”
. ” ah yayana ba wani Abu fa ai na watstsake sai dai kuma na gaba”

Kallonta yai da sauri yace “wane irin kuma na gaba ana fatan Allah ya yaye miki dika”
Ajiyan zuciya tai ganin bai fahimci abinda take nufi ba don ita nufinta sai wani month d’in kuma,

Nunu tai mai da bedside d’in dake gefansa don ya zauna tashi yai ya hau ya zauna sosai,_Aisha data shafa adduar ta tace” sannu da zuwa ya aiki”

“Yawwa sannu Aminiyar mu ya jinya? Ina fatan kun kula min da ita sosai”

Mirmishi tai tace”yaya tan bayeta kaji har wanka na mata”
Zaro ido Baby tai tana kallon Aisha tace”sis wanka kuma Allah ya kiyaye ni yanzu ai na girmi amin wanka”

Dariya Aisha tai ta fice zuwa parlour shi kuma ya dawo da kansa ga Baby yace “ya zaki ce kin girmi amiki wanka?”

“Ehh mana na girma mana, ni yanzu wa zai min wanka”

Kansa ya nuna da hannunsa yana kashe ido d’aya ,
K’asa tai da kanta bata ce komai ba,ganin tayi shiru yai k’asa da murya don kar Islam dake sallah taji yace” Baby biki girmi wanka ba in dai ina raye don in dai mukai aure ni zan rink’ai miki wanka in nad’eki a towel in kawoki d’aki in shiryaki in miki kwalliya sannan in goyoki abaya na in kawoki dining in baki abinci abaki har sai kin k’oshi sannan in ci nawa ,in mun gama in d’aukoki in dawo dake kan kujera Misha soyayyanmu”

Lumshe ido tai tana d’an mirmishi tace” hhhmmm”
“Ban gane hhhm ba ko bakya so?”
Girgiza kai tai tace” ummy tazo harda su Abdussalsm dasu Nabeela”
Dariya kawai yai don ya gane so take ta baga rar da zancan yace”tom sun kyauta”

Jawo ledan dake gabansa yai ya Ciro roban fresh milk Yar asali yace “Bari aziba miki milk d’in kisha ko”
Juya idonta tai tace”um um ummy na ta kawo min wainan shinkafa da miyar yakuwa naci da yawa yanzu kam ban shaawar komai”

“Ok ummy ta kyauta mun gode mata,bari asa wannan d’in a fridge anjima sai ki sha ko?”

Gyad’a mishi kai kawai tai, wata ledan ya jawo it kuma cike take da fruits ya kalleta yana d’an mirmishin tsokana yace
“ga wannan su kisha su yanzu don kina buk’atarsu a wannan lokocin”

Da ido ta tanbayeshi me Nene bud’e ledan yai ya tura mata ta d’an lek’a ganin fruits ne yasa ta d’ago tai mai kallon Kai ko hhhmmm,
“A a ni bana buk’atarsu sabida inada dik abinda zasu bayar ajiki”

" a a akwai abinda yai miki k'aranci yanzu sai kin had'a dash"

Maganar da Islam ke mishi ne yasa ya juyo da ganinshi kanta” malama Hafsa wato yau dai addini akeji tunda na shigo ake sallah”

Dariya tai tace”ah daman ni kullum cikin addini nake “
“Ok to naji jeki parlour ina ganawa da madam d’ina”

“Hhhmmm sannu me madam ko bakya fad’a ba can na nufa”

Dariya yai ” ki kawomin abinci ina jin yunwa, kuma kicewa inna gani nan fitowa gareta Dana shigo bata parlourn”

Gyad’a mai kai kawai tai ta fice,

Juyowa yai yaja d’aya ledan ya d’ora mata kan cinyarta’ kallonsa ta kuma yi a karo na barkatai tana Neman k’arin bayani kan ledan dake kan cinyar tata,
“Um ki bud’e mana ki gani”
Hannu tasa ta bud’e, da sauri tai saurin rufe ledan ta shiga biga k’afanta tana d’an kukan shagwab’a tace

“Wai meke damunka yayana koda yaushe burinka kasa ni cikin jin kunya haba don Allah ka barni haka”

Y’ar daiya yai yana lek’a fuskanta yace” To meye abin rufe ido ki bud’e mana ki kalleni”

“Ni dai Allah ka fita ka fita ni bazan bud’e ido na ba sai ka fita”
Sosai yake dariya ya d’auke ledan akan cinyarta yasa kan gadon yana cewa”To wai in ban fara miki irin wannan siyayyan yanzu ba sai yaushe, ni ki daina kunya ta wlh”
“Eh naji ka fita parlour zanzo in sameka can”

“Ok tunda kin gaji dani bari in fita” yasa Kai ya fita parlourn

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta bud’e idonta ahankali cikin ranta take mamakin yaya Nabeel wane irin mutum ne shi aduniya baya jin kunya a dik lamarinsa kai tsaye yakeyi, to inda yana jin kunya me Zaisa don tana up ya siyo mata pard kai wlh namiji ma dai sai abarshi da fitsara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button