BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Aisha tai ta turo k’ofan ta shigo ” sis yaya Nabeel yace ina milk d’in da fruits d’in insa a fridge anjima in tilas ta miki kisha”

” to tunda ni y’arku ce ai sai kumin d’ura, wlh Sis lamarin maza sai su wai duba ledan nan kiga abinda ya siyo min”

Jan ledan tai ta bud’e pard ne leda guda sha biyu aciki,

Dariya Aisha tai sosai tace “tabd’in tunda aka fara suyo pard ai saura su bra”

Duka Baby ta kai mata tana cewa “kema kin zama tabbatacciya wlh sis Allah ya shiryaku”

Cikin dariyan da take tace “ameen”

Taku ce
Layuza kabir Adam ????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

WANNAN PAGE D’IN NAKU NE Y’AN UWA ABOKAN AIKI

AUNTY AMAH
AUNTY NASMAT
SHAXEE
ZEETTY
QUEEN HAUSY
BEAUTY QUEEN
Z RANO
MARYAM
RUKY
ZAHRA ( A )
SARA ADEEYA
AMEERA
HAFSA
MMN NOUR
ZUWAIRA MADARA

KAMAL KAMALA
AND KING BOY ISAH
MUNA HAD’E IRIN MATUK’AR HADANNAN
ALLAH YA KARA MANA HADIN KAI JAMA’AR ZAMANAWA????✍ INA K’AUNARKU DA SAURAN DA BAN ANBATA BA

       8⃣2⃣

Bayan Nabeel ya daga gidansu Baby kai tsaye gida yayo yazo yai wanka ya shirya cikin k’ana nan Kaya ya fito zuwa parlour anan yasami ummynsu yake shaida mata Baby ce bata da lfy ,

“Subhanallah, meya sameta ?”

“Wannan dai ciwon cikinne nima bayan asuba Islam ta kirani take fad’amin to naje nakai musu allura an mata yanzu bacci take, amma d’azu suma take tayi”

“Kai uban giji ya yaye mata wannan ciwo, can zaka koma yanzu?”

“Eh can zani “

“To kace ina mata sannu kaji, insha Allah anjima insu nabeela sun dawo zamu shigo mu duba ta”

“Ok zan fad’a mata Bari inje”
Yasa kai ya fice,

Sai da ya biya 7:30 Restaurant ya siya mata kunun gyad’a tunda yasan masoyiyarshi ce,

Lokacin daya shiga gidan yasamu ta farka har Aisha ta hada mata ruwan wanka tana shirin shiga ya shigo ganin zata shiga yace

“Aisha anya zata iya wankan nan da kun bari ta d’an k’ara samun k’arfi zuwa jimawa kad’an”

“Yaya wlh munce ta bari zuwa jimawa ta dage saita shga”

“Kallonta yaga yanda take layi yace”Baby na yi hak’uri zuwa jimawa kiyi”

“A a nidai ina so inyi yanzu”
” To Aisha rakata ki taimaka mata kinga fa layi take yi karta fad’i”

Rik’eta Aishan tayi suka shiga toilet d’in shi kuma ya fito parlour gun inna suka fara d’an tab’a hira ita kuma Islam ta fara gyara d’akin,

Bayan wajan 20 minutes Aisha ta fito parlourn tace ” yaya ka shiga ta shirya”

Mik’ewa yai da sauri ya shiga d’akin da sallama, can k’asan bakinta ta amsa tana kwance kan gadon tana kallon sama,
Samun gu yai ya zauna bakin gadon ya zuba mata ido kusan Minti guda sannan yace’sannu precious, ya jikinnaki ?”

Idonta a rufe tace “da sauk’i”

“Sannu Allah ya k’ara sauk’i,tashi ga kunun gyad’a kisha”

Girgiza kai tai alamar bata sha, marai raice mirya yai cikin yanayin son atausaya mai yace” pls Baby na kiyi hak’uri ki daure kisha ko kad’anne kinga zaman da yunwa ba dad’i amma in kika sha zakiji ckin naki ya miki dad’i kuma jikin zai miki k’arfi kinji Baby nah”
Kanta na gefe tace” yaya fa banjin dad’in bakinnawa ne”

“Eh nasa ni hakuri zakiyi kisha kad’an don Allah”

Ayanda yake maganar kamar zaiyi kuka shi yabata tausayi ta dafa gadon ta mik’e zaune sannan ta jin Gina da jikin gadon, Islam ya kira ta shigo yace”d’an zubo mata kunun gyadar da nazo dashi kisa spoon ciki”
“To ” tace tai waje minti uku ta dawo da cup ahannunta ya karb’a yace”kinsa mata sugar ?”

“A a bansa ba”
” to kisa mana ai zaifi dad’i”

Mirmishi tai tace”yaya ya zaai mutumin dake ciwon ciki abashi Abu da sugar balle itama datake cikin wannan situation d’in”

Dafe goshi yai yana” ochh na manta ne”

Matsowa yai kusa da ita sosai ya d’ebo kunun a spoon yakai bakinta, kallonshi tai a kai kaice tace “me zakayi?”

Yace “baki zanyi mana”

Girgiza kai tayi tasa hannu ta ta amshi cokalin ta d’iba takai bakinta ahankali , d’ago idonta tai taga ya kafeta da kallo itama kafeshin tai sannan ta d’an juya idon nata ta lumshe , yarrrrr yaji tsikan jikinsa ya tashi , akaro na biyu ta k’ara d’iba takai bakinta nanma idonshi na kanta, turo baki tai cikin shagwab’a tace ” kallo fa”
D’an mirmishi yai ya langab’ar da kanshi gefe batare da yace mata komai ba, itama kauda fuskanta tai daga gareshi, ta d’ansha kad’an tace” yaya nah nak’oshi”

Zuba mata ido yai na y’an seconni sannan yace”to Baby nah sannu kinji dibi ida nuwanki har sun fad’a Allah ya yaye miki wannan ciwon”

Kad’an ta bud’e bakinta tace “ameen”

Tashi  yai ya fito da kofin  kunun ya  mik'awa Aisha don takai kitchen,

Mik’ewa tai ta kwanta sosai tare da Jan blanket ta rufe jikinta zuwa wuya,

Daya shigo ya ganta ta kwanta sai yaja bed site ya zauna suna kallon juna, ganin irin kallon da yake mata yasa tasa hannunta kan fuskan ta, mirmishi yai ya janye hannun nata,

“Wai me yasa ake son b’oyemin wannan kykykyawan fuskan”

Basar da maganar tai tace”d’an bani wayana kan mirror”

Mik’ewa yai ya d’auko mata wayan”me zakiyi da waya kina fama da kanki?”

“Islam zan kira”
Danna number d’in isy tai “Islam ki hadowa yayana break mana, ok”

Kallonta yai yace”da biki ce mata ba ma zanje office akwai Kayan da za’a kawomana zanje in taresu”

Kallonshi tai ta kad’a kai alamar bata yardaba,
Kafin ya k’ara magana Islam ta shigo da flask d’in tea da Kayan madara,ta ajiye zata fita tace mata “Islam ki had’a mishi mana kika ajiye”

“Ohh sis banfa gama shigo da kayan bane zan d’auko mai flask d’in chiefs ne”

Bayan ta kawo ta had’a mai komai sannan ta fita,
Sama sama ya karya ya wuce office yana cewa “precious bari inje anjima zan dawo”

Gyad’a mai kai tayi ta bishi da ido Tana jin wani bala’in sonshi na k’ara ratsa dikkan jikinta.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

BABY KHAUSAR

      NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

           8⃣4⃣

To haka suka ci gaba da zaman jiran dawowar su mami tsawon wata guda anyi sallah babba sunyi hidimar sallarsu cikin farin ciki kamar yanda ko wane musulmi yake shiga,

Bayan sallah da sati biyu su mami suka dawo dasu Abban Aisha sun shiga farin ciki sosai nan su baby suka he suka raka Aisha gida murna kamar zata tashi sama don murna ganin iyayenta da yan uwanta wanda ta shafe sama da wata guda bata gansu ba sai dai waya nan gidan suka yini sannan suka dawo gida suka dasa yiwa mami hira, dik abinda akai bata nan ji suke kamar ta maida su ciki don murna,haka da Dad yazo ya zauna shima sukaje suka kwak’ubeshi ,

To tun dawowar su Dad ba abinda aka sa agaba sai shirin biki don yanzu ya rage wata biyu bikin,

Kamar yanda gidansu ya Nabeel suka shaida gobe zasu kawo lefe don haka fa gidansu Baby a kacame yake ana ta shirye shiryen Tatar lefe, mami gayya tayi kamar bikin ne yazo, don haka ma’aikata ta d’ebo daga hotel sukai snacks kala kala manya manyan farantai aka cika da kayayyakin guda ashirin, sannan aka bada aikin rago agasa goben sai a karb’o ,

Su Islam da Aisha haka suka matsawa Baby akan sai tazo sunje kunshi ita kuwa tace fafur baza ta ba ita gobenma baza ta zauna agidanba kunya takeji, masifa sukaita mata akan wai ta zama y’ar k’auye ai andaina yayin wannan abun, ita dai jinsu kawai takeyi, don haka sukai tafiyarsu suka barta,

Yau kam tun safe k’awayen mami suka cika gidan y’an uwansu dai rabuwa sukai wasu gidansu Nabeel wasu suka taho nan d’in, hidima ake kamar ba gobe to abinka da naira ta zauna,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button