BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda gidan ya fara cika baby ta shige part d'in Dad ta rife Don harga Allah kunya take ji ,ko cikin y'ay'an masu kud'i ba'a rasa masu d'abiar kunya don ita kunya halittace kuma baiwa ce ita kam Baby an mata baiwarta.
Jama'a kamar ana tuttulosu akeyi haka masu kid'an k'warya suka zo sukaita cashewa,k'arfe biyar na yamma y'an kawo lefe suka kawo akwatina set uku kalan feank sai kalan ja da porpul ko wanne guda shida, Kaya ne tsadaddu matuk'a kai gaskiya Nabeel yayi k'ok'ari ya iya zab'o Kaya da zai dace da matarsa.
Shigowar y’an kawo lefen yasa gidan ya k’ara kacamewa akai musu Tara da Kayan arzik’i dik da kasancewar dik y’an uwa ne,
Gidan bai Sara ra ba saida dare kowa ya watse, anan Baby ta fito daga part d'in Dad su Aisha sina ta mata tsiya wai ita y'ar k'auye ce waye- waye ko kulasu batai ba ta shige d'aki donyi sallar isha'i,nan ta zauna taita tasbihi tana godewa Allah daya bata miji kamar Nabeel, aduniya Baby tana jinta sama da kowace budurwa tunda ta sami Nabeel in maganar kyau ake zaka Tara maza d'ari baka sami me kyan Nabeel ba, in maganar ilmi ne ma haka uwa uba kirki da son mutane ga zumunci da rik'o da addini.
Akan prayer mat d’in Aisha ta same ta tace “to amarya ni zan wuce gida gasu fadwah suna jirana har sunyi bacci nayi nayi subi mama sunk’i gashi sun had’ani da aiki”
“To ki barsu mana da safe a kawosu”
” kin manta gobe suna da skul bari kawai in tashe su mu wuce yaya nazeef yazo yana can tare da sahibar tasa”
Mik’ewa tai tace”ok to muje ,ina su fadwan?”
“Suna d’aki a k’asa”
Sakkowa sukai down stairs suka shiga d’akin su na k’asa yaran dik suna kan gado suna ta baccinsu su uku bubbuga k’afansu sukai suna kiran sunayensu, dik suka tashi nan suka sasu gaba har parking lot Inda yaya nazeef yake tare da Islam ana ta soyewa, nan suka gaisa da Baby yana mata ala sanya akairi,
Bud’e motan sukai suka shiga Islam tace”yaya ka shigo mu tafi yaran nan fa bacci ne idonsu a k’arasa soyayyan a waya”
Hararanta yai yace”innak’i tafiya fa?”
Dariya sukaiy baby tace”ayi hak’uri yayanmu “
Mirmishi yai yashiga motan yana d’agawa Islam hannu suka bar gidan”
Suna komawa cikin gidan Islam tacewa Baby “ki zo kiga Kayan naki yaya Nabeel yayi fitasara akwati shida yacika miki da night wear’s”
Mirmishi tai tace”saurin me nake da zanga Kayan yanzu,kuma meye abin fitsara don yacika set guda da wannan Kayan ai ya nuna muku zamu Shana ne”
Kallon Islam tai k’yar tace”IH sis micijin sari ka nok’e a haka ki nuna ke me kunya ce sai munzo d’aki ki ta bid’ala”
“Ba wani bid’ala gaakiya na fad’a”
“Hhhmmm sis wai d’azu ina ji anata cewa ai ke kunya gareki da mune damu za’a karb’i Kayan auranmu amma ke gashi kin b’oye kanki”
Mirmishi Baby tai tace” ah kune buku iya takunku ba”
*** kwanaki suna ta tafiya biki na k’aratowa dikkan siyayyan Kayan auran Baby kama daga furnitures kayan kitchen da sauransu dik ta Internet aka siya mata kasan cewar ancigaba kana daga d’akinka ta online sai kayi ciniki da k’asar wake,to don haka da Dad yace su shirya suje suyi siyayyan mami ta bashi shawaran suyi komai ta online zaa kawo musu har gida ko a wace k’asa suka siya, don haka mami take b’ata lokaci wajan zab’awa Baby Kaya na Jan magana,don pics suke turo mata kamar hauka wanda ta z’aba sai su Fad’a mata kud’in ta tura musu ta accuont.
Sati guda suka turo da Kayan, don haka yanzu kuma gyaran jiki akasa agaba ranar da suka gama exam ranar me gyaran jikin da mami ta d'auko mata y'ar Sudan ta fara gyarata,
To b’an garan y’an mata kuwa suma basu wahlar da Kansu ba wajan rabon invitation kawai turawa k’awayensu sukai tayi ta chart, don haka gyaran jikin da akewa Baby yafi ratsata tinda ba inda take fita,
Mami bata da matsala zaunar da Baby takeyi ta fayyace mata komai na rayuwar aure da yanda zata risketa.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
8⃣5⃣
Da dare suna zaune a d’akinsu aka kira wayan Islam kasancewar Baby tafi kusa da wayan yasa takai hannu ta d’auka don mik’awa Islam (broth Bilal) ta gani akan wayan rassss gabanta ya fad’i don ita har ga Allah mantawa take da wani Bilal inba taji Dad ko Islam sun fad’i sunansa ba ko suna waya dashi, jiki a mace ta mik’a mata wayan ,
Islam da murnarta ta d’aga wayan tana fad’in ” my broth sai yau ka tuna dani ko?”
Baby batajin abinda yake fad’a amma dai taji Islam ta k’ara fad’in ” subhanallah meya sameka? Amma shine baka fad’a mana ba, ok to Allah ya k’ara lfy,yanzu sai yaushe Kenan zaka taho? A a yaya gaskiya ka taho dai jibin, haba mana ya daje ace dik wani shirye shirya kana nan zaa fara, ok to saika zo bye”
Juyowa tai ta kalli Baby dake ta chart tace” sis kinji broth Ashe bashi da lfy shiyasa naketa Neman number d’insa baya shiga kwana biyu, anma yace da sauk’i jibi ma zai taho”.
" um hmmm Allah ya kawoshi lfy"
Daga haka bata k'ara cewa komai ba,
ranar laraba shine ranar da za’a fara bikin za’ayi kamu Alhamis ayi dinner jumma’a a d’aura aure ayi waleema, sai kuma ran asabar mami tayi yininta ran lahdi za’a kai amarya.
Kallo d’aya zakaiwa baby kasan tasha gyara ta kuma tsumu sabida Yar Sudan tana tsimata da kayan gyara ciki da waje, kwana biyu Nabeel bai zuwa sabida zirga zirga dik ya kacame sai dai suna yawan waya don haka baiga gyaran da Baby tasha ba daya k’ara susucewa,
K'arfe hud'u aka sa za'ayi kamun anan cikin gidansu aka shirya filin baya aka tsara masu decoration sun k'awata wajan da kayayyakin gargajiya way'anda zasu sa wajan ya yi kyau sosai,
Tun k'arfe biyu su Islam Aisha Nabeela wadda ta dawo gidan da zama don tace gidan maza ba'a wani shagali sosai,da kuma dik yan Matan da suka zo kama daga k'wayen su na skul zuwa y'an uwa, dik sun tafi gidan kwalliya ,amma Baby ita me kwalliyarta har gida tazo zatai mata,
Yanda ta tsarawa Baby fuskanta da kwalliya zakai tunanin ba mutum bace sabida tsananin Kyan da tayi, cikin wata wedding gown aka shiryata kalanta light blue ga he’d da aka sa mata dai dai kanta ga wasu fation silver da d’an kunne da sarka dasu bangles dasu zobuna, takalminta da post d’inta ma silver ne, kai masha Allah gaskiya ta had’u .
Dik y’an matanma anko sukayi na wani material Feank calor sika sa he’d blue,
Kamar yanda aka tsara harda maza a kamun don haka ango ma yai shigansa cikin shadda light blue malin malin ya kafa hulanshi ita ma blue tsan tsan kyansa ya k’ara bayyana,
Tofa waje yayi waje kid’a ne kawai yake tashi cikin taushi dik jama’a suna zazzaune kan kujeru shigowar ango da amarya kawai ake jira, aiko ana fara cewa ga ango da amarya hankali ya dawo kan hanya, yana rik’e da hannunta suka shigo k’awaye da abokan ango na binsu abaya, d’ay daga cikin wak’ok’in bikin nasu aka saka, suna tafe masu video da masu photo suna ta d’aukansu,abin gwanin sha’awa ahaka har suka k’arasa wajan zamansu aka ci gaba da shagali sannan aka kira hjy haleema mahaifiyar Bilal don Taiwa amarya kamu nan tazo da mutum shida nabinta da kaskon turaren wuta kanshi nata tashi tazo Taiwa amarya kamu ana ta tafi sannan shima ango k’awar mamanshi tazo tai mai kamunshi,nan akaci gaba da shan shaani har magriba sannan aka tashi.
Washe gari da safe dik y'an matan suna d'akin su Baby suna ta zuba gidan acike yake dank'am da jama'a , Islam ta shigo d'akin tace"Baby kizo inji mami tana parlourn Dad "
Tana shiga ta tadda hjy haleema dasu Aunty ameera yayyan Bilal dik sunzo daga Lagos d’in da hjy Amina sai mami agefe da Dad azaune kan sofa, waje ta samu ta zauna kanta a k’asa ta gaida kowa, Dad yai gyaran murya yace “KHAUSAR dalilin dayasa akai kiranki shine hjy Amina ce tace akiraki domin ta k’ara neman yafiyarki akan dai dik abinda ya faru abaya, domin tun tuni take cewa ki yafe mata amma tace har yanzu bakya mata magana alamar dai biki yafe ba, to awannan karanma da zaki bar gidan nan ki tafi gidan mijinki tana k’ara Neman yafiyarki “
Cikin miryan son yin kuka tace”Dad nifa tun tuni na yafe mata”
Mami ce tai gyaran mirya tace” batun yanzu ba Baby nake miki nasiha akan ki zama me yafiya Allah yana son mutum me yafiya, Baby kicire dik wani k’ullaci aranki”
Shashshek’an kukan tane ya cika palourn hjy Amina ta taso tazo ta rungume Baby tana cewa” ki yafemin Baby kiyi hak’uri da abinda ya faru wlh nayi nadamay ki d’aukeni matsayin uwa yanzu, ki yafewa Bilal ma wlh ni nashiga tsakaninki dashi nai muku farrak’u sabida naga irin son da yake miki yana jin haushi yanda nake miki Abu, ki yafe mana Baby badan halina ba don Allah”
Kukan da takeyi ne yasa jikin Baby matuk’ar sanyi ta
Cikin nata kukan itama tace”na yafe miki daman ni na dad’ee da yafe muku keda yayan”
Hjy haleema ce jawo Baby jikinta ta shiga sa mata albarka tana k’ara mata nasiha akan zaman aure da hak’uri.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
8⃣6⃣
Da dare k’arfe 8:00 aka fara tafiya dinner kowa ya tafi sannan ango da marya sai k’arfe Tara suka shiga wajan yauma shigansu iri d’aya amma yau farar shiga sukayi ita material irin d’inkin amaren Indian shi kuma farin tsadaddan wani boyel sai shining yake komai nasu fari kama daga Kayan harsu takalmi hulanshi da sauransuy yau sunfi jiya kyau sosai kuwa , don tun amota Nabeel ya susuce sai kallon ta yake yi yana mirmishi, shagali sosai akayi agun ba Magana , baa tashi ba sai k’arfe kusan d’aya sannan suka dawo gida,