BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari da safe tunda baby ta tashi gabanta ke fad’uwa dik jin jikinta take amace, ta rasa meye dali li don haka ma dik tsiyan da su Aisha ke mata bata tanka ba daga k’arshema sai gani sukai ta fashe da kuka abinma mamaki ya basu nan suka shiga rarrashinta ahaka bacci ya kuma d’aukan ta, cikin baccin taji ana mata magana ta d’ago ido wata Yarinya ce ummy tace ” Aunty baby wai kizo inji yaya Bilal ” “yaya Bilal?” Ta mai maita cikin ranta tun ran laraba fa taji ana cewa yazo kuma bashi da lafiya ma daya zo, mik’ewa tai tace”kice mai ina zuwa,amma yana ina”
“Yace ki sameshi a part d’in Dad”
Da sauri ta shige toilet tai wanka tana fitowa ta kalli agogo saura awa d’aya ad’aura mata aure da habeebinta, “Masha Allah” ta fad’i aranta sauri tai tasa dogon rigan abaya tasa d’an mayafin akanta ko mai bata shafa ba tunda tasan yanzu za’aimata kwalliya , d’akin ba kowa dik y’an Matan sun fice , fitowa tai sai hayaniyar k’awayen mami kawai takeji, kai tsaye tai part d’in Dad da sallama ta shiga parloun a tsaye ta Ganshi ya juya baya yana kallon window, kallo d’aya tai mai tai k’asa da kai sanye yake da faran shadda da babbar Riga d’inkin yasha aiki ash calor don haka yasa hula ash da takalmi ga agogon dimon a d’aure a tsintsiyar hannunsa ,idonshi sanye da siririn farin glass yayi kyau matuk’a,
Waje ra samu kan kujera ta zauna tare da fad’in “ina yini ya jikin naka?” wanda ita kanta bata San ta furta ba, ahankali ya juyo ya kalleta sau d’aya ya maida Kansa gefe yace” jiki da sauk’i Alhamdulillah , ya taro”
” cikin sark’ewar murya tace” Alhamdulillah”
shiru ne yabiyo baya tsawon 3 minutes ya nisa yace” Naso tahowa ayi komai dani tun sanda Dad ya fad’amin saura wata guda to amma banda lafiya tun lokacin yanzuma kawai tahowa nai tunda ya zama dole inzo, Baby kiyi hak’uri da yanayin rayuwa adik yanda tazo miki ki zauna da mijinki cikin aminci da rik’e sirrin juna kiyi mishi biyayya, nasan Nabeel mutum ne na gari zai rike da amana ina muku fatan alkairi arayuwar auranku,Allah ya Baku zuri’a ta gari”
Shiru ne ya k’ara biyo baya can yasa hannunshi kan t,v ya d’auko wani d’an akwati irin wanda ake sa sark’a ya mik’o mata ” Baby ga gudun mawa ta nan Allah Sanya Alkairi”
D’ago da idonta tai ta kalleshi dammmmmm gabanta ya fad’i ganin irin muguwar ramar da yayi dik da idonshi cikin glass yake hakan bai hana taga ruwan daya taru a idonshi ba hannu tasa ra karb’i d’an akwatin tare da fad’in” na gode Allah ya ‘kara zumunci”
” Bari in wuce masallaciny naga lokacin sallar ya kusa kuma ana idarwa za’a d’aura”
“To” kawai tace ta tashi ta fita,
Tana komawa d'akin ta zauna bakin gado ta bud'e akwatin, sarka ce da d'an kunne da bangles da zobe na gwal k'irar dubai tafkekiya an rubuta KHAUSAR & NABEEL Da siririn ributun goal a tsakiyary sar k'an wani irin dad'i taji da k'aunar sark'an ya shigeta, tun tana k'arama ake mata ado da sark'an goal har zuwa yanzu amma bata tab'ajin wadda ta shiga ranta farat d'aya kamar wannan, "to meye dalili" ta fad'a aranta, wani tsagin na ranta ya bata amsa da fad'in dan da sunan Nabeel ne ajiki shiyasa ai kuwa tana tuna haka tai mirmishi tare da rungume sark'an a k'irjinta tana kallon ago go saura minti arbain ta zama mallakin Nabeel rufe idon ta tai lokacin data tuna da wata magana da Nabeel ya fad'ama ta jiya, jitai an turo k'ofan su Islam ne suka shigo suna ta surutu Aisha takai hannu ta amshi sark'an hannunta dariya tai tace" oh wannan sark'anfa masoyan asali a ina aka k'erata?"
D’an mirmishi tai tace” ya Bilal ne ya kawo min gift d’inta,
Karb’a sukai tayi suna fad’in kai amma tayi kyau Allah yasanya Alkairi” mik’awa Islam tai tace”isy kikaiwa mami ta ajiye, wai ina kukaje ne?”
” gidanki muka je kai gaskiya Baby zaku shana gida ya fita fa”
Bata ce komaiba kawai mirmishi tai Nabeela tace” Yaya fa yayo waya wai akwai dinner k’arfe bakwai da abokansa suka shirya mai yace Ki zama cikin shiri ya kira wayanki a kashe”
D’an zare ido tai tace “wayyo ai na manta ban kunna wayanba wayyo mijina Allah yasa bai fishi dani ba”
Shewa suka d’auka gaba d’ayansu suna oh masu miji manya nan suka shiga Mata tsiya,
K'arfe d'aya da rabi bayan idar da sallar jumm'a a masallacin al furk'an aka d'aura auran KHAUSAR A ABDALLAH DA ANGONTA NABEEL BELLO YAKASAI a sadaki dubu d'ari wanda d'unbin jama'a suka shaida.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
MASOYAN BABY KHAUSAR INA BAKU HAK’URIN
JINA DA KUKAI KWANA BIYU SISTER NA CE BA LFY INA JINYARTA A ASIBITI AMMA YANZU TA WARKE ALHAMDULILLAH , YANZU ZAKU RINKA SAMUN POSTING KODA YAUSHE INSHA ALLAH
8⃣7⃣
Bayan d’aurin aure dik mutanan Dad gida sukayo inda aka shirya k’asaitacciyar walima ta maza zallah abinci ne kala da iri sai wadda kake so zaka ci ga ga nama iri iri kama daga gasashshen rago da farfesun naman sah zuwa soyayyun kaji , bayan gama yin walimarsu Abokan Dad suka kira Baby wadda aka shirya cikin doguwar rigar shadda gezna Y’ar asali kanta sunkuye tazo ta zauna ta gaishe su nan sukai tai mata nasiha kan rayuwar aure daga bisani sukai tai mata kyaututtuka mutun biyu cikinsu suka bata mota, sauran kuwa tsabar kud’i sukaita bata , Baby dik jinta take wata iri wai ta zama matar aure yau itama ta zama cikakkiyar mace , kwata kwata bata gane a halin da take ciki sai hawaye daya k’i tsayawa a idonta,
Haka ta koma d’akinsu jikinta na ta rawa gabanta nata fad’uwa Tana shiga d’akin ta kwanta a gado ko zuciyarta zata daina bugawa,tan bayar kanta take shin ko wace mace aka d’aura mata aure haka take shifa wani yanayi ita kam ta kasa gane meye wannan takeji ita dai baza ta kirashi da farin ciki ba ko akasin haka,
Takai kimanin 30 minutes akwance ita ba bacci ba ba kuma ido biyu ba, mik’ewa tai ta gyara mayafinta zuwa parlour anan dik ta Tarar dasu Aisha kowa tanbayarta yake ta tashi a baccin, kai kurum take gyad’a musu me mata make up tace “tun d’azu nake jira ki tashi ad’an k’ara gyara fuskan sai ki canja Kaya ko?”
D’aki suka koma aka k’ara gyara fuskan sannan ta canja kaya zuwa Riga da zani na super Holland me yarfin ja tasa Jan takalmi jaka da mayafi,
ja jaye ta dawo parlour, anata mata gud’a,
Bayan sallar magriba aka tattafi gun dinner sai ango da amarya da babbar k'awarta Aisa shima ango da abokinsa wanda zai jasu a motansa, yauma shigarsu iri d'aya ita da angota sunyi masifar kyau, abaya suka zauna shida ita gaba kuma sai abokinsa na driving da Aisha a gefansa, tun da suka shiga motan taji yazo jikinta ya nanik'eta yasa hannayenshi ya sak'alo ta sosai dammm taji gabanta ya fad'i karo na farko daya tab'a mata haka,
Tsam tai da ranta kamar ruwa yaci ta,hannunsa yasa ya tallafi hab’anta tare da d’ago da fuskanta ya zuba mata idanuwansa, lumshe nata tai bata bari sun had’a idonba ba, tsawon lokaci yana kallonta yana jin wani irin farin ciki na shigarsa, sosai yake sha’awan rungumeta a k’irjinsa amma tunawa da yai a mota suke yasa ya bari,
Aisha ce ta juyo da niyar yiwa Baby magana taga irin zaman da sukai, kauda kai tai tana y'ar dariya tace, "Ya Nabeel ya da haka"
D’an cikata yai yace” Aminiyarmu ban sanki da gulma ba wannan aikin Islam ne”
“OK to nayi shiru”ta fad’a tana rufe bakinta,
Zaid yai Dan mirmishi yace abokina baka da dama,
Ahaka suka ci gaba da tafiya Nabeel na Kara nanik’ar baby ita kuma tak’i ko da motsi kwata kwata ta rasa meke damunta don wannan rik’on da yai mata ma ji take Kirjinta yana bug’awa kamar zai fito.
A haka suka k'araso wajan bayan zaid yai parking Aisha ta fito Ta kalli Baby tace " to amarya bari mu shiga ayi arranged d'in yaran suzo mu shigo daku"
Gyad'a kai kawai tai ba tare da ta bud'e idonta ba,
Ita da zaid suka wuce ciki don sanar da zuwan ango da amarya.
Yana ganin su zaid sun bar wajan ya k’ara matsawa jikinta sosai har k’irjinsu yana had’uwa Dana juna ya d’ago fuskanta ahankali yashiga hura mata iska akan lumsheshshun idanunta yana sauke mata wani numfashi me tsuma masoya, ahan Kali yasa hannunshi ya ruk’o nata ya shiga murzasu yana d’an matsa su, dik ilahirin jikinta rawa ya d’auka, ta rasa awane yanayi take, goshinsa ya d’ora kan nata yana d’an murzawa ahankali, atare suke sauke numfashi da sauri sauri k’anshin turaran jikinsu na dukan hancinsu ,ji yake kamar ya maidata ciki don haka ya k’ara nanata a k’irjinsa yasa hannunshi ya zagayeta yana shafa bayanta, rik’on da yai mata ne yasa hed d’inta fad’uwa ko ta kansa baibi ba yashiga shafar gashin yana sinsinawa , dik abinda yake ko sau d’aya bata bud’e idonta ba balle tayi wani yun k’urin hanashi abinda yakeyi ba,
Islam ce ta k'araso jikin motan don basu damar fitowa kowa ya zuba idon ganin shigowarsu, tana zuwa tasa hannu taja murfin motan kasancewar me bak'in glass ne yasa bata ga yanayin da suke ciki ba, shi kuma Nabeel k'auna ta rufe mai ido baiga k'arasowanta ba balle kuma Baby,
Jan murfin motan yai dai dai da sanda yasa harshensa cikin bakinta, da k'rfinsa ya ruk'o murfin tun kan ta gama bud'ewa, jikinsa a mace yasawa motan lock sannan ya d'auki he'd d'inta daya fad'i k'asan kujera yasa mata, ya d'auko handcheaf ya goge fuskanshi da bakinsa ya gyara zaman hulanshi, ahankali ya sa bakinsa a kunnanta yace" bud'e idonki mu fita suna jiranmu,
Bud’e k’ofan yai tare da rik’o hannunta suka fito sauran y’an mata da samarin suka rufa musu baya suka shiga kid’a mai taushi yana tashi cikin aji da wayewa suke taka rawa.
Taku ce
Layuza kabir Adam ????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????
❤❤❤❤❤❤❤
ASHE HAKA SO YAKE DA DAD’I ALLAH KABARMU DAME SONMU DA GASKIYA HAK’IK’A YAN ZAMANI MASOYAN GASKIYA NE,TUNDA HAR DAMUWAR D’AYANSU KAN SASU CIKIN K’UNCI ABINDA AKAIWA MUTUM D’AYA YAKAN ZAMA NAMU DIKA Y”AN K’UNGIYAR ZAMANI ALLAH YA K’ARA HAD’A KANMU, DIKKAN WANDA YAKE CIKINMU YAKE DA WANI MUGUN K’ULLI CIKIN RANSA AKANMU ALLAH YAI MANA MAGANINSA.????
MUNA TARE IRIN MATUK’AR TARA NAN????????????