BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

         8⃣8⃣

Hadari ne ya had’o gagarimi Wanda yasa mutane sukaita tafiya gida dik kowa ya hargitse ganin ga dare Yayi k’arfe goma, dikkan abokan ango sai d’iban jamaa suke zuwa gida, ya rage daga ango sai amarya da Aisha da lslam sai Nabeela , motan k’arshe data dawo zaid ne da ibrahim abokan Nabeel suna shigowa hole d’in ruwa na sakkowa suma da gudunsu suka k’araso ciki,Islam ta kallesu tai dariya tana fad’in”haba kamar ba maza ba kuka shigo da gudu haka, ai sai Ku bada y’an maza wlh”

Dika dariya suka sa ibrahim yace” hhhmmmm ai ba maganan bada y’an maza in mutum ya tsaya wannan ruwan ya tab’ashi yanzu zazzabin maja zai kamashi”

Nabeel yace”yanzu dai haka zamu hak’ura har sai ruwan ya d’auke sannan mu tafi”

Dik zama sukai suna d’an hira zaid yace” ya kamata fa ace minyi sallar isha’i “

“Kai nufinka mu fita ana wannan ruwan, kawai kowa ya bari in ankoma gida Yayi tunda ita lokacinta me tsayi ne”

Ibrahim yace”a a muje reception su bamu key na d’akuna biyu Ku matan Ku shiga d’aya muma d’aya dik muyi sallan sai mu jira d’aukewan ruwan”

Tare da nabeel sukaje reception d’in sukai musu bayanin Suna son key d’in d’akuna don zasuyi sallah , suka biya kud’in d’akunan na awa d’ai d’ai,madadin suga Nabeel ya amshi key guda biyu said suka ga ya amshi uku da sukai mai magana sai yace ai shida matarsa d’aya y’an Matan d’aya saisu y’an mazan, kallonsa sukai k’ur da alamar tan baya Ibrahim yace” Kai me kake nufi wlh bazai yuyu mu d’auko y’ar muta ne mu kawota kazo ka mata iskanci ba ka bari zuwa jibi dik iskancinka ya k’are”

Ganin da yai suna shirin mai Iskanci yasa ya wuce ya barsu gun, Kai tsaye Inda su Baby ke zaune yaje ya kama hannunta ya d’agota sannan yace wa su Aisha su taso Dik suka bi bayansa, inda sukai dinner d’in a k’asa ne sai inda d’akunan suke a can sama hawa na biyu zuwa na hud’u numbers d’akunan ya kallah ya Mikawa Aisha key d’aya yace gashi Ku zauna acikin wannan, su kuma way’annan bari su k’araso su amshi wannan, dik matan suka shige Baby ta fara k’ok’arin shiga ya rik’ota ” ina zaki kum?”
Kallonsa tai bata ce komai ba tai k’asa da kai adai dai nan su zaid suka k’araso ya mik’a musu key d’aya batare daya ce komai ba ya fara bud’e k’ofan gefe ibrahim yace

“kai Allah dai ya shiryeka da zumud’i mudai sallah kawai zamiyi mu fito mu tafi gida ko ruwan bai d’auke ba”

Ko kula su bai ba yaja hannunta suka shige ya rufo k’ofan,

Jikin bangon ta jingina tana tsaye ya cire hulansa da agogo ya cire malun malun ya ajiye gefen gado sannan ya cire sau cikinsa da safa,

Ahankali ya k’araso kusa da ita ya ruk’o hannayenta tare dasa kanshi a wuyanta yana shinshina , rawan da jikinta yake yai matuk’ar k’aruwa ta fara fad’in ” yaya nah ka bari don Allah pls”

Kamar bai ji me tace ba ya zame net d’in dake jikinta ya cire he’d d’in dik ya watsa kan gadon sannan ya k’ara matseta ajikinsa yana sauke ajiyan zuciya, ido ta lumshe tana jin hawaye na zuba a idonta jin yanda dik ya shiga shafarta tako ina, ya kai tsawon lokaci yana tsotson bakinta da sarrafa ta har saida yaji Tsaiwan na shirin gagararsa sannan ya cikata tai k’asa ta tsugunna tare dasa kanta tsakanin cinyoyinta, shima bakin gadon yaje ya zauna tare da dafe Kansa yana maida numfashi sun d’au tsawon lokaci ahaka, daga bisani ya mik’e ya shiga toilet ya kama ruwa tare da d’auro alwala, yana fitowa yace ” Baby tashi ki d’auro Alwala muyi sallah”
Harya d’auko sallaya ya shinfid’a yasa hula bata motsa ba , ya k’ara kallonta karo na biyu yace” tashi mana my precious kiyi Alwala karsu zo suna jiranmu”

Ba tare data kalleshiba ta mik’e ta shige toilet d’in shi kuma ya tada sallah raka’a biyu bayan yai sallama ya juyo ya ganta tsaye a bayansa yace “ga hijab can kan bedside kisa “

Jansu yai sukai sallar, ya dad'e Yana addua'a sannan ya shafa itama ta shafa ta mik'e ta cire hijab d'in sannan ta ninke shima ya ninke salla yan yana shirin sa babbar rigansa yaji ana knocking yaje ya bud'e ,zaid ya gani tsaye yace "kai D'an iskan ango fito ruwa ya d'auke mu tafi k'arfe  11:00 fa yanzu"

“To naji jeka gamu nan fitowa”

Yasa hulansa da ago go, itama ta yafa net d’inta ta rik’e he’d d’in a hannunta, suka fito,

A bakin motocin suka same su su Islam na kallonta suka fara k’unshe dariyar gulma bata kulasu ba ta shige motan suka tafi.
????????????????????????????????????

BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????????

           8⃣9⃣

Washe gari asabar ne mami tayi yininta na manya a meenat hotel inda manyan mata suka rak’arshe suka cashe,

Hjy Amina ta saki jiki hidimar biki ake da ita sosai mami bata nuns komai don ita ilmi ya ratsa ta bata da damuwar kowa aranta,

Bilal kam tunda yazo bikin nan jinsa yake kamar akan k’aya don haka ya shirya kayansa tsaf a daran yau ya sami Dad ya fad’a mai gobe lahdi zai wuce ana masa kiran gaggawa daga can India d’in da safe zaibi jirgi ya wuce tunda dai an gama biki kai amarya kad’ai ya rage, Dad bai hana shi ba yace to,

    Washe gari lahdi k'arfe bakwai yai musu sallama sai india,

A b’angaran Baby kuwa tunda ta tashi da safe take kuka kamar ranta zai fita tasan yau kwanan gidansu ta’are mata sai dai da wani dalili, kowa rarrashinta yake yana nuna mata. hak’uri da rayuwar aure,

 Abdussalam ya shirya gagarumin hawan doki kasancewarsa me harkar dawakai yasa ya shirya kilisa da abokansa tare da shirya gasa a gun ga dik Wanda ya cinye yana da kyautar mota Wanda yazo ta biyu kuma mashin na uku kuma kud'i, shikam Nabeel Sam Sam bai son yin kilisar nan haka kawai yaji bata kwanta mai ba amma ganin irin kud'ad'en da k'anin nasa ya kashe kan shirya kilisan yasa ya amince zai je, hatta Kayan sarautar da ango da amarya zasu sa Abdussalam ya siya musu da alKabba,ayanda aka tsara in an d'auko amarya daga gida sai awuce da ita filin sukuwa Inda za'ayi hawan, in angama kawai sai  akaita gidanta ,  Fili fa ya cika yai mak'il da jamaa, k'ungiyar abokan Abdussalam sun zage sai zuba kilisa suke abin abin birgewa dik Wanda yake wajan fa mirmishi yake , nan masu gasa suka fara zubawa  wani abokin Abdulsalam d'in ya fara kaiwa inda aka tsaga ai kuwa nan tafi ya tashi raf raf raf,  sannan na biyu ya k'araso shima tafin akai mai sai na uku, sauran dik dasuka k'araso  dariya kawai akaitayi, nan aka gabatar da kyaututuka ga way'anda sukaci gasar, 

Nabeel da Baby dake zaune a inda aka shirya musu da kujerun sarauta dik sunsha Alkyabba sunyi kyau matuk’a da gaske, ya kalleta yace” precious ko zamuje ki hau dokin ne naga sun birgeki”

Mak’ale kafad’a tai tana y’ar dariya tace” um um nikam bazan hauba sai dai kai”

Gyd’a kai Yayi yace” kin San wlh kuwa sha’awar hawan dokin nake dik tsimi ya tasar min kinsan fa da nima nayi harkar kilisa”

D’an zaro ido tai tace “da gaske? Wlh yanzu Bakaga yanda suka birgeni ba”

“Da gaske sun birgeki?”

D’aga gira tai tana mirmushi

Ya juya ido cikin k’warin gwiwa yace”ai kuwa tunda suka birgeki yanzu zanje na hau don ki k”ara Shiga farin ciki”

Masu hotuna ne suka yo Kansu y’an kilisan sukazo suka zagayesu akaita musu da vidio,
Nabeel ya ruk’o hannun Abdussalam yace”zan hau doki d’aya in d’an zagaya a fili don amaryata tace da kuka hau dokunan kun birgeta”

Dariya Abdussalam yai yace “OK ba damuwa ango na amarya” wani zanbad’ed’an doki Abdussalam ya jawo zuwa gaban Nabeel yace “bisimilla hau”

Kallo d’aya zakayiwa dokin ka tabbar da k’arfinsa ja ne gashi dogo ga k’iba kai da gani ya kiwatu, Nabeel ya kalleshi yace” kai wannan dokin ai saiya Yar dani yamin girma asamo k’arami”
Dariya aka hau mishi Abdussalam yace “kai yaya Nabeel karka bada y’an maza sai kace bakai harkar nan ba”

Kallon Baby yai yace” Baby nah in hau kin yarda?”

D’aga mai kai tai alamar e, da saurinsa ya muk’e hannunshi cikin nata suka fara takowa gun dokin yai wani tsalle d’aya ya haye dokin, ai kuwa nan fili ya d’au ihu da tafi ango zai yi sukuwa kan doki, rik’e lunzamin dokin yai yace Baby ta tsaya jikin dokin amusu hotuna, nan da nan masu camera da video suka fara aikinsu akansu tsawon mintina ana musu Baby ko tsoron dokin batai ba ta tsaya jikinsa,

Ba Wanda ya zata kawai sai gani akai dokin ya suri Nabeel ya kwasa da gudu takan mutane ya shiga bi yana haniniya wasu da yawa da basu San kan garinba sun d’auka Gwarzontaka Nabeel keyi Wanda kuwa suka San harkar nan suka fara salati don sunsan kwanan zanjan nan fa waje ya rud’e da ihu ganin da akai dokin ya fara juyi alamar yana son yardashi kafin sukai ga jallin taimaka mai har ya kaishi k’asa kuma yasa kafansa ya takashi kana yaja da baya ,

Wani k’ara Baby ta saki ta fad’i k’asa a sume, wasu sukai kanta wasu kuma sukai gun Nabeel d’in, lokacin da aka d’agoshi ba inda ke motsi jikinsa nan fa aka shiga koke koke nan da nan aka sasu a mota sai asibiti cikin tashin ahankali,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button