BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsawon lokaci aka samu Baby ta farfad’o shi kuwa Nabeel ba alamar ma zai dawo,

Tunda ta farka ta Shiga kuka wiwi tana kiran yaya , rarrashin ta mami ta shiga yi da kalamai masu sanyi tana shafa bayanta ahaka bacci ya kuma d’aukanta,

Sai cikin dare Nabeel ya farfad’o amma agalabaice gashi ya sami karaya a hannunshi na hagu , sassafe aka kira likita daga asibitin k’ashi yazo asibitin ya dubashi sannan yace akaishi asibitinsu sumai d’ori sannan a dawo dashi nan asibitin, wani private ne acikin sabon garin kano,
Tunda akai mai d’ori bai k’ara farfadowa ba sai washe gari,

Baby kuwa koda yaushe kuka ita akaita taga yayanta sai dai ai tai mata wayo da dabara anacewa yana asibiti daban shima, ahaka harta watstsake duka amma fa ta zabga uwar rama,

Lokacin shima daya dawo hayyacinsa da kiran sunanta ya fara ganin haka yasa ummynsa tace akawo Baby d’akin ta ganshi ya ganta,

Da k’afanta ta rinka takawa har d’akin tana ganinsa haka kwance da hannu sak’ale jikin wani k’arfe yasa ta fashewa da kuka, yasa hannunshi ya rik’e nata k’am yana fad’in “daina kuka Baby daina kimin add’ua kawai Allah ya ban lfy kinji” d’aga kai tai tana Sharan hawaye dake anbaliyya a idonta,

Abban Nabeel dake zaune gefe ya yace” kuyi hak’uri wannan itace k’addaranku jarrabaku yai domin yaga ima ninku, Allah ya Baku lfy gaba d’ayanku, Khausar ki kwantar da hankalinki kinji”

A d’akin ta yini kusa dashi da dare su mami zasu tafi ta mik’e tace mai saida safe, kai kawai ya d’aga mata suka tafi,

 Tunda sukaje gida ta kasa bacci dik da yanzu bata jin wani rashin lafiya ajikinta amma zuciyanta ba dad'i, Islam dake kwance tana bacci tai juyi kawai ta ganta zaune, tashi tai itama ta zauna ta ruk'o hannunta tace "sis me kike baki bacci ba haryanzu?"

“Ba komai”tace lokacin da idonta ke kawo ruwa
“Kiyi hak’uri Baby ki daina kuka Allah zai bashi lfy kinj irin taku jarrabawar Kenan, ki kwanta kiyi bacci kinga yanzu dare Yayi”
Zamewa tai ta kwanta badan tana jin baccinba.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????

BABY KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

❤❤❤HAPPY BIRTHDAY TO YOU ANNABI MARHABABIKA ALMUKUTARI❤❤❤

          9⃣0⃣

Tunda tai sallar asuba ta shiga kitchen ta fara shirya abinci kala kala Wanda zai dace da Mara lafiya bata fito ba sai wajan bakwai da rabi , ta shirya komai cikin kwando,

Da sauri sauri ta shiga wanka ta fito ta tashi Islam tace kije kiyi wanka mu tafi asibitin,
Shiryawa tai cikin doguwar riga bak’a ta d’auko d’an bakin mayafin rigar zatai rolling kawai sai taji wani sashi na zuciyanta na cemata kefa matar aure ce yanzu wannan d’an abin yamiki kad’an da sauri ta d’aurashi akanta ta d’auko wani yellow mayafi mai d’an girma ta yafa akanta,
Islam ma da sauri sauri ta shirya suka fito a parlour suka sami mami tace” ai nai zaton Baku tashi ba nazo taahinku Ashe har kun shirya to maza kuje nima gani nan zuwa kumai sannu”

  Suna shiga asibitin Baby taji gabanta na fad'uwa nan tashiga fad'in "innalillahi wa inna ilaihi ra'jiun". Jiki amace ta tura k'ofan d'akin ganinsa tai zaune bakin gado suna hira da Abdussalam tunda dama shike kwana dashi, k'arasawa tai gabansa fuskanta d'auke da rauni da tausayi, hannunta ya ruk'o yana d'an mirmishi yace " Baby nah har kin k'araso sannu da zuwa"
 Muryanta can k'asa tace"yayana sannu ya hannun naka"

“Da sauk’i Alhamdulillah biki ganni zaune ba”

Islam ta gaidashi damai ya jiki ya amsa yana tsokananta kamar bamai rashin lafiya ba, Abdussalam ne ya gaidasu suka amsa suna tanbayarshi ya mai jiki,
Islam kujera ta samu ta zauna Baby kuwa na tsaye gabansa hannunta cikin nasa ya d’an matsa yatsunta yace” Kinyi shiru Amarya ko biki gama warwarewa ba Abdussalam yacemin suma kikai kinga doki ya kada miki mini”. Ya k’arasa maganan da d’an mirmishi
Nan da nan hawaye ya kunce a idonta tunowa datai da lokacin da dokin ya nanashi da k’asa,

Kallonta yai yaga sai shashshek'ar kuka take ya rasa ma mezaice mata,

Abdussalam ne yace “haba Aunty na ki daina kukan haka ba gashi kina ganinsa ba ai abinma yazo da sauk’i, yaya ka rarrasheta bari Mu Baku waje”

 Fita sukai shida Islam suka koma babban parlour  inda y'an dubiya ke zama,

Ruk’ota yai da hannunsa me lafiyar ta shigo tsakanin k’afafunsa ya shiga d’an pitting d’in bayanta yana mata magana cikin kunnanta”Ki daina kuka Baby na kinji ba komai ai haka Allah ya tsara mana ni banjin ciwon komai ma jikina da zasu sallamemu ma yau mun wuce gidanmu mun fara shan amarcinmu ko”
B’oye fuskanta tai a wuyanshi, yai y’ar dariya yace “meye abin b’uya kinga yanzu da tuni na zama cikakken ango ko”

Sauri tai ta janye jikinta daga nashi jin datai ana shirin shigowa,

 Su ummy ne da Abbansa suka shigo  Baby ta tsugunna ta gaidasu  suka amsa suna tanbayarta yame jiki cikin jin kunya ta amsa da sauk'i,

 Ya gaida su Abba yaje ya zauna gefan gadon yace"Nabeel ya jikinnaka?"

“Da sauk’i Abba”
Sun d’an zauna ummy tace” kaci Abinci ne”
Ya girgiza Kai yace” a a gashi ma Baby tazo dashi”

Kallon Baby tai tace” tashi ki zuba mai yaci kinji y’ar albarka”
Cikin jin kunya ta tashi ta zuba mai jalof d’in wake da hanta sannan ta tsiyayo mai kunun alkama da gyad’a ta zo ta d’ora mai a gefan gadon, ta juya zata zauna yace “kinsan bazan iya ci da hannu d’aya ba ki taimaka ki bani”
Jitai kamar zata nitse don kunya yanzu gaban iyayensa zaice ta bashi abinci a baki don rashin kunya,
Ganin ta rikice yasa Abba ya mik’e ya fita ummy kuma ta d’auko wayanta ta shiga dannawa,
Cokali tasa ta shiga bashi yana karb’a yana wani lumshe ido ahaka har ya k’oshi yace “to kema kici”

Girgiza kai tai alamar a a”yace ummy kinga wai bazata ci kimata magana”
” Khausar ki zuba kici mana zaki zauna da yunwa ne”
D’an kad’an ta zuba taci dik da ba wani dad’in shi take jiba,

A haka y’an dubiya sukaita zuwa har dare yauma tana ganin su mami zasu tafi ta mik’e ya kalleta yace”mami ya kamata Baby ta rink’a kwana an an tana taimakamin da wasu abubuwan”
Kafin tai magana mami tace”ai daman anan zata zauna intaje gidan me zatayi ke Islam tashi mu tafi”
Tana gani suka fita haushi kamar zatai kuka meyasa Nabeel zai min haka inshi baijin kunya ai ita tana ji ace wai zata rink’a kwana dashi a asibiti ai sai wani ya fassara su,
Bata k’ara cemai komai ba ta tashi taje toilet ta wanke fuskanta tazo ta hau doguwar kujera ta kwanta shi kuma Abdussalam ya kwanta a parlour,

Ganin batai mai magana ba yasan fishi take, wayanta ce tai k’ara tana d’auka taga mami ce tun kafin ta amsa sallamar datai tashiga mata fad’a” haba Baby ke saikace ba wayayyiyar mace ba har sai nace miki ki zauna ki kula da mijinki, ashe dik abubuwan da nake koya miki bai shiga jikinki ba kinyi karatun boko kinyi na addini amma dik abanza, to ina Jan kunnanki daki kula da mijinki kinji ko”
Jikinta asanyaye tace “to mami” ta kashe wayan,
Tana d’ago da kai taga ya zuba mata ido ta lumshe idonta tana mirmishi tace”yada kallo haka yaya nah”

Shima mirmishi yai yace “ba komai Babyna kwanta kiyi baccnki”

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????

BABY KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

      9⃣1⃣

Tsawon lokaci ba Wanda ya kuma magana,
“Baby kinyi bacci ne”
Ya furta ahankali , juyi tai tace”um um”
“To meyasa bikiyi ba har yanzu,ko rashin sabo ne kinji wajan ba dai dai da irin naki ba ko?”

D’an mirmishi tai ta tashi zaune tace” wlh ban San meyasa ba yanzu ban iya yin bacci kona kwanta sai dai inta juyi”

Ziba mata ido yai tsawon lokaci harta tsargu ,hannunsa yasa ya kirata dashi ahankali ta tashi taje bakin gadon ta zauna ya ruk’o hannunta da hannunshi me lafiyar yasa yatsunsa biyu cikiny tsakiyan hannunta yana juyasu aciki tare da matsa was, ahankali takejin wata nutsuwa na saukar mata idonta ta lumshe tana tunanin abubuwa da dama,

Cikin muryanshi data fara dashewa yace”Baby na hak’ik’a Allah yana jarabtar bawansa akan abinda yafi so nikam nasani ya jarrabeni ne akan sonki,ina sonki khausar ina k’aunanki fatana ki kasance mallaki na ni kad’ai har Abadan”

“Yayana yanda kake sona inaji araina bai kai son da nake maba, ina sonka tun daga kaina har zuwa k’afana dikkan zuciyana cike take da begenka fatana koda yaushe mutuwa ta d’aukemu rana d’aya sabida inhar ka rigani tafiya raina bazai taba daidaita ba har zuwa randa nima zan bika, honey ka rayu dani tsawon rayuwarmu”
Kuka ne yaci k’arfinta ta kifa kanta a k’irjinsa ta shiga rai raiwa,
Shima kansa bai San meyasa zucuyarsa yin rauni ba saiji yai hawaye nabin fuskanshi, ya d’ora hannunsa me lafiya kan bayanta yana shafawa ahankali yana pitting d’insa kusan 10 minutes sannan ya sami k’arfin halin yin magana”me yasa kike zubar min da tsadaddan hawayenki meyasa kike da saurin kuka ne Baby nah? Kina tare dani baki da sauran bak’in ciki kiyi shiru kinji”
D’aga Kai tai cikin yanayi na shagwab’a, k’ara matseta yai ajikinsa ya matsa mata ta kwanta akan gadon sosai, itama tsintar kanta tai da rungumeshi ahaka bacci ya d’auketa, yana jin saukar numfashinta yasan tai bacci,ido ya zubawa kyakykyawar fuskanta yana k’ara jin wani zafaffan sonta na ratsa dikkan gab’b’ansa , had’iyan miyau yai lokacin daya sauke idonshi kan lips d’inta ahankali ya d’ora nashi akai yashiga goga su cikin salon shauk’i ahaka har bacci ya d’aukeshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button