BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEM
0⃣9⃣
Yana shirin fita yahadu da Amira ta sunkoto Bilal wai yayi. Bacci karbarsa yai yasashi akafada yaje ya bude mota ya kwantar dashi .shima yashiga yazauna kusan 30min yana zaune hjy Amina ta fito fiskar nan ba faraa ido yai jajir sabida kuka
Gaba ya budemata amma saita. Shige. Baya kusa da Bilal
Baice mata komaiba. Yaja motar suka. Tafi har. Sikaje. Gida ba Wanda. Ya ce uffan suna Shiga. Ta shige dakinta shikuma yakai Bilal ya kwantar
Dakinsa ya shige yai sallah ya Dade yana addua Allah yasa aurannan yazama Alkairi agareshi. Daga bisani yashafa .yakwanta
Don baison zuwa wajanta yanzu yaga ta dau zafi sai zuwa gobe tukun
Itakuwa hjy Amina tana gado sai juyi take a gado tana kuka hakika nasihar da yayarta tai. Mata. Ta ratsata. Amma shikenan. Haka tana gani mijinta. Zai auri me aikinta. Haka taita saka da warwara har bacci ya kwasheta
Abangaran masu aiki suna da tarin yawa. Sabida abincin sadaka da akeyi. Kullum Yasa masu aikin yawa tsofaffi da yaran mata dik cikinsu hazida ce kadai budurwa don hakama hajiya ta ware mata dakinta ita kadai acikinsu . wanda sauran suke mutum biyar biyar adakinsu
Dik cikin masu aikin Hadiza jininsu yafi haduwa da wata dattijuwa iya Abu macece me kirki sosai don sauran masu aikin haushin hadiza sukeji yanda hjy take kula da ita sosai take fifitata akan.su
Yau tunda ta tashi takejin faduwar gaba don hakama bata shiga cikin gidan da wuri ba sai sha daya na rana tashiga gun hajiyar da sallamarta shiru ba Wanda ya amsa kai tsaye kitchen ta shige don shirya abincin rana ta fara harhada abinda zatai amfani dashi .taji muryar Alh yana fadin Hadiza da sauri ta juya tare da tsugunnwa tana fadun Alh ina kwana
Da fara arsa ya amsa yace tashi tsaye dama magana nakeso muyi
Rawa jikinta ya dauka tace to Alh .yakai minti biyu yana kallanta sannan yace hadiza zaki iya aurena
Da sauri ta gado ta dubeshi tana ja da baya tare da rufe bakinta da hannu don kuka ya kubce mata
Bai damu da yanayin da tashigaba yace hadiza ki shirya aurena nanda Dan lokaci don hajiya ta ban tarihinki dika .don haka tausayinki Yakama ni inason auranki don in inganta rayuwarki kinji karkiji tsoro ko shakkar wani ab… …….
Bai karsaba daga bayanshi yaji ance andaiji kunya wlh girma ya fadi rakumi ya shanye ruwan yan tsaki
Ke kuma munafika zo ki ficemin daga kitchen al gumguma .inna kara ganinki a sashinnan saina karyaki maci amana .
Jiki na rawa hadiza tabi ta kofar baya ta fice .tana rusa kuka cikin tashin hankali tayi bangaransu
Dik inda tai sauran masu aikin kallonta suke kowa da abinda yake fadi musamman yan gulma ca suke to me kuma yasami yar lelen hjy take wannan kuka haka
Bata tsayaba saida ta dangana da faking a tana shiga ta fada kan katifarta tana gursheken kuka
Iya Abu ce tashigo ta zauna gefan katifar tana fadin haba hadiza me yafaru kike wannan gursheke sai kace wadda ake zarewa rai tashi maza ki daina haka gashi can kinsa makiyanki dariya sunata murna yau sunga kukanki
Ajiyar zuciya tai tamike zaune .
Yauwa ko kefa yata share hawayanki ki fadamin damuwarki insha Allah zan share hawayanki .
Cikin inda inda ta fadawa iya Abu komai ita ma abin ya girmameta tagumi ta rafka daga bisani tace ki kwantar da hankalinki hadiza shi aure da kike gani nufin Allah ne inya tsara ke me dakice ga Wanga me gida tofa ba makawa saiya aureki koda kuwa kina garinku ne
Don haka ki sawa zuciyarki nutsuwa .ki mika lamarinki ga Allah zai isarmiki
Ammafa hakika wanga batu batu da girma yake um um um ni zainabu shikuwa Alh. Banda Abu nashi yana zamansa lfy da matarhi zaizo da wannan batu .
To Amma aishi komai nufin Allah ne .
Kuma abinda nakeso dake kija bakinki kiyi shiru akan maganar har muga yanda Allah zaiyi.
Da yamma hjy Amina ta Tara dika maaikatan gidan mata banda Hadiza don ita tanacan zazzabi ya rufeta .
Ta kare musu kallo can ta samo me Dan tsafta kuma bazata wuce shekaru talatinba bazawara ce barira sunanta
Tace ke daga yau nayi canjin hadiza dake .kezaki rika tayani aikin bangaran girkin Alh. Kuma kije kicemata nace ta kwashe kayanta ta mayar makwancinki ke kuma ki koma dakinta .
17/9/2017
????????????????????????
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
BAZAN GAJI DAMIKI GODIYA BA MY SWEET AFREEN ALLAH YABAR KAUNA_
1⃣1⃣
To itadai hadiza ta rasa mafita kullum kuka bata da zabi gashi Baba matar Mlm Khalil kullum nasiha take mata akan ta kwantar da hankalinta ta yarda wannan kaddararta ce
To da haka dai ta fara samun nutsuwa
Ayaune aka daura auran Alh Aliyu Abdallah Wanda jama a sukafi kira da AA Abdallah .da Hadiza Bashir me aikin gidansa
Wanda Mlm ya zauna a waliyin Amarya
Ana sallar ishai Baba matar Mlm da yan tsofaffi kawayenta. Suka kawo hadiza gidan mijinta wanda aka sata a bangarenta dake gefan na hjy
Sudai yantsofaffi nasiha kawai sukewa hadiza da haka suka barta ita kadai sai kuka take don tana tinani. Yanda zata had a miji da uwar dakinta .
Yau kwanan hadiza biyar a amatsayin amarya a gidan zuwa yanzu ta sake jiki ta yarda wannan yin Allah ne .
Kuma da taimakon nasihar iya Abu kullum take mata don yanzu ta dawo bangaran Hadiza da zama .tunda Alh.yace zai samo mata mai tayata aiki tace a a iya Abu ma t isa ta debo kayanta aka bata daki guda akasa .suke zamansu .
Kullum bangaran hadiza a rufe yake sabida tana tsoron haduwa da hjy. Son haka ko Alh.ne zai shigo saidai yai anfani da keys dinsa ya bude
Cikin ikon Allah watan hadiza biyar agidan ta sami ciki aikuwa tunda iya Abu ta lura da cikin ta kira Alh.ta fadamai kuma tacemishi .dik suyi shiru da bakinsu don irin wannan ba ason yadawa sabida maganr mutane
Aikuwa Alh yaja bakinsa yai shiru ba wanda ya fadawa sai Mlm Khalil
Yau da gobe cikin hadiza yakai wata takwas ba ta taba fita ko inaba ko awoma likita ke zuwa har gida ya yaimata Alh yadaukewa hadiza dik wata damuwa .tayi kyau ta kara fari .
Yau tunda ta tashi takeson fita ko harabar gidanne don rabonta da waje tun randa aka kawota .wani irin masifar tsoron hjy Amina takeji .wanda bata fatan ko hanya ta hadasu.
Wajan karfe biyar na yamna .tafito barandar gidan tfy take .ahankali irin ta masu tsohon ciki .tana kallon gidan kamar bashiba yazamemata wani iri tana shirin shiga Gardiner din gidan taci karo da Barira .
Salatin da Barira keyi tana tafa hannu yasata jin faduwar gaba .ah lalle hadiza harcin amanar taki yakai ki dau ciki agidannan .tabdin jamm kafin kace me harta zura da gudu kaiwa hjy.rahoto
Jikinta amace ta koma bangaranta .itama cike da tsoron me zaije yazo
Barira kam ta kaiwa hjy lbr mafi muni da Tayar da hankali
Kamar zata hau iska haka har Alh.yadawo yasameta tanata sababi da masifa akan ya cuceta ya rufe mata hadiza Nada ciki.haka suka kwana tana sababi .shi abin har mamaki yake bashi yanda dik halayen hjy Amina suka canja ta zama . masifaffiyar gaske .
Tinani yake wai shin haka dik mata sukeyi in aka musu kishiya?
Bayan sati biyu .cikin dare hadiza ta farka da nakuda gashi ranar Alh yana dakin hjy.tun tana daurewa har tazo ta tashi Iya Abu .ai kafin iya Abu taje kiran Alh .har ta haihu .
Iyace ta gyarata tsafuhh ta gyara babyn da wajan zuwa sallar asuba har sunyi fes itada kyakkyawar babynta .tubarkallah masha Allah.
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
HHHMMMM RAAYI RIGA .NIKAM NAWA RA’AYIN KENAN .RUBUTA NOVEL.????????
1⃣2⃣
Wayyo haihuwa kyautar Allah .wanda babu me iyai maka wannan kyauta komai son da yakema
Hakika wanda Allah yabawa kyautar haihuwa .yamishi kyauta me girma
Wai dama haka mutum yake tsintar kansa .in akace yau gashi matarsa ta haihu.
Wannan shine subadadin da AA Abdallah
Yaketa yi lokacin daya sa babynsa akirjinsa . yanajin wani irin nishadin da nutsuwa yana shigarsa . zir hawaye yafara bin kuncinsa .
Iya Abuce ta lura da yanayin daya shiga. Tai gyaran mirya .tace ai Alh.ba kuka zakayi ba .godiya. Zakayi ga Allah daya baka sai yakara maka .
Alhamdulillah yashiga fada yana .kara rungume .babyn .har zuwa wani lokci .sannan .yaimata kiran sallah .da Adduoi.
Juyowa yai yaga iya Abu ta fita .ahankali yasa hannu ya rungume hadiza .yana samata Albarka da godiya .
Yace hadiza na baki kyautar .Plaza dina da ke haj kam. Sannan na baki kyautar sabuwar mota ta . na baki kyautar gidan gona ta na kumbotso. Sannan na baki kyautar million daya .kuma zan miki viza .in kinyi arbain .zamuje kasashen duniya daga biyar har zuwa ishirin in kina so. Bayan haka ki fadamin wani abinda kikeso .
Cikin shishikar kukan farin ciki .tace .Alhamdulillahillazi bi niimatihi ta tummassalihat.
.Alh. Na gode ma da kulawarka .Allah yakara budi da arziki me albarka
Wayanshi ya dauka yashiga kiran yan uwa da abokan arziki yana gadamisu.
Daga bisani ya koma part din hjy da fara arsa .yake cewa Amina kina ina ne yau Alheri ya sauka agidannan .hadiza ta haihu .ansami ya mace kyautar Allah .(littafin Ashmaad)
Wani matsiyacin kallo tabishi dashi .sannan tace to Allah yaraya .
Amin Amin yake fada yana kokarin daga wayarsa da aketa kiransa don mishi barka .don haka ma bai lura da yanayin da take ciki ba yafice .yana wayanshi.