BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Kiran sallar asuba ne ya farkar dashi ya bud'e ido ahankali yajita manne da k'irjinsa ajiyan zuciya ya sauke ya shiga shafa gashinta zuwa bayanta,ganin bata ko motsa ba yasa ya fara hura mata mata iska akan idonta, mik'a tai ahankali ta bud'e idon nata karaf suka had'e tai saurin lumshe nata jinta datai lafe cikin k'irjinsa,d'an mirmishi yai yace"tashi anyi kiran sallah karmu makara"
Ba tare data kalleshi ba ta zame jikinta daga nashi ta sauka a gadon toilet tashige ta dauko roba da ruwa a k’aramar buta ta fito yana ganinta dasu yace” bari zan kama ruwa zoki cire min igiyar hannun nan in sauka”
Yanda ya buk’ata tamai ya shiga ya kama ruwa ya fito ta taimaka mai yai Alwala ya kalli gabas ya tada salla azaune, itama alwalan tai tazo ta tada sallah, bayan idarwarta ta dad’e tana kwararowa mijinta addua akan Allah ya bashi lafiya,bayan ta shafa ta juyo ta kalleshi tare da fad’in “barka da asuba, ya jikin naka”
Da mirmishi ya amsa akan fuskanshi”kin tashi lafiya ya kwanan asibiti? Ya kwanciya jikin Mara lafiya”
Da sauri ta rufe fuskanta tana d’an dariya k’asa k’asa,
Ahankali ya k'ara kiran sunanta"Baby nah ina so ki taimakamin inyi wanka kafin gari ya gama wayewa mutane su fara zuwa"
“Yaya kana ganin hannunka d’aure taya zakayi wanka kasan fa ba’a son ruwa ya tab’a ko kad’an”
“Baby nah wlh na matsu inyi wankan nan rabona fa da wanka tun randa wannan tsautsayin zai faru, banjin dad’in jikina ji nake kamar bani ba”
Ganin yanda yake magana da damuwa a fuskanshi yasa ya bata tausayi, mik’ewa tai taje ta kunce igiyan da hannun ke rataye jiki ta wuce toilet ta had’a mai ruwa me zafi Wanda zaiji dad’insa ta fito”yaya kaje kayi na had’a ma ruwan”
Mik'ewa yai rik'e da hannun sa ya shiga toilet d'in tsayawa yai yana tunanin ta yanda zai fara,
Gyara bedsheet d'in tai ta kad'e gadon ta tattare dik abinda ya dace jin shiru bata ji alamar watsa ruwa ba yasa taje bakin k'ofan tana fad'in"yaya nah ya dai baka fara wankan ba"
Daga ciki yace"Baby wanka ya gagareni yau bansan ta yanda zanyi da hannu d'aya ba"
Wani masifaffan tausayinshi ya k’ara kamata aranta tace” meye anfanin zamana a asibitin nan inhar bazan taimakawa mijina a lokacin da yake Neman taimako ba”
Da sauri ta shige toilet d’in ta sa hannunta ta b’alle zif d’in rigan dake jikinsa a nutse ta cire hannun karayar sannan d’aya hannun, yarrrr taji tsikan jikinta ta tashi ganin gashi kwance luf luf a k’irjinsa da sauri ra kauda kanta,fitowa tai d’akin ta d’auki wata babbar Leda tazo ta nad’e hannun don kar ruwan ya tab’a, a ahankali ta tsugunna tace”yaya ka kunce wandon acire”
Ba musu ya kunce ta zame mai ya rage daga shi sai d’an gajeran wando, ta d’auko soso da sabulu tazo tasa ruwa ahankali ta fara cud’a mai jikin yana zaune kan wata kujera, dik abinda takeyi kalkonta yake da mamaki na irin kunyarta Sam rak’i yarda su had’a ido da ganin yanda take ma hankalinta a tashe yake don haka ma daya ga bata ce ya fidda k’aramin wandonba bai dame ta ba yasan inya fad’i haka zata iya fasa taimaka mishi, a nutse ta wanke shi tsaf ta d’auko towel ta d’aura mishi a k’ugunsa, tsayawa tai tsam gabansa ba tare data ce komaiba, ya gane me take nufi don haka ya zame k’aramin wandon da hannunshi d’aya ya gyara zaman towel d’in ajikinsa, juyawa tai zata fita yasa hannunshi d’aya ya ruk’ota jingina tai abango tana kallon gefe tace” ya dai da wani abun?”
Matsowa yai jikinta sosai ya d’ago fuskanta yana son kallon idonta amma r
Tak’i” Baby nah me yasa kike kauda kanki daga gareni? Ki barni in kalli k’wayan idonki in nuna miki jin dad’ina ga hidimarki gareni”
Bata d’ago idon nata ba cikin sanyin muryanta tace” dikkan abinda nai maka hak’k’inka ne akaina ya zama dole in kula da kai koda baka cikin halin jinya balle kana buk’ar taimakona a halin yanzu karka damu mijina”
Har cikin ransa yaji dad’in kalamanta, k’ara had’a kansa yai da nata yashiga shinshinar fuskanta ahankali ya gangaro ga bakinta yasa nashi ciki da mamakinsa da sauri yaji ta cafci harshensa tana tsotsa kamar ta sami sweet- . . . . .
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
9⃣2⃣
Sun dad’e tsaye ahaka Suna aikawa junansu sak’onni kala Kala dikkansu sun jigata tsaiwar ma gagararsu take numfashi suke saukewa atare atare da sauri sauri tai k’arfin halin janyewa ta fita da sauri tunawa datai a asibiti suke kuma ako wane irin lokaci wani zai iya zuwa, jiki amace shima yabiyo bayanta ya fito ya zauna bakin gadon yana maida numfashi, “precious zoki bud’e jakan can akwai kayana ciki ki fiddomin kinji”
Mik’ewa daga kujeran da take zaune taje ta d’auko mai Kayan Riga da wando ne na shadda farare tas an yanke hannun rigan d’aya, mai ta d’auko ta shafa mai sannan ta taimaka mai yasa Kayan yai Fe’s dashi.
Komawa tai toile d’in ta kintsa shi ta d’auraye sannan ta fito tazo ta zauna, wayanta ta d’auko ta kira Islam ta fad’a mata dik abinda take buk’atan tazo mata dashi da wuri kafin afara zuwa sabida tana son yin wanka, bayan ta ajiye wayan ta juyo gareshi ai kuwa kamar yanda ta zarga idonshi na kanta, d’an murmishi tai tace”kallo kuma yaya nah, koda Matsala ne?”
Girgiza kai yai yace “yau yaushe?”
Tace ” laraba”
“Hhhhmmm da tuni Yuu kwana na uku da zama cikakken ango”
Juyar da kai tai tana fad’in”kai ko yaya nah ka fiye Jan magana”
“A a ba wani Jan magana gaskiya na na fad’a ai”
Katse xancan tai da fad’in “bakajin yunwa? Naga jiya baka wani ci abincin kirki ba”
Girgiza Kai yai yace”um um banjin yunwa jiyama don aji tausayi na abarmin mata ta ne yasa nak’i cin abincin dik nai kalan tausayi”
Dariya tai tace”kai yayana sannu da aiki ai dana sani ban zauna ba inga k’arshen kalan tausayin”.
Haka sukaita hiransu cikin farin ciki har Islam tazo, knocking akai taje ta bud'e Islam ce ta bata hanya ta shigo tana kar ban Kayan hannunta bata zauna ba tai sauri ta shige toilet tai wanka data fito tazo ta bud'e jakan ta zaro kayan Riga da siket ne na atanfa kalan orange da fari ta d'auko mata farin hijab me hannu ,komawa toilet tai tasa Kayan sannan tazo ta shafa mai ta d'an goga humra tasa lips stick tasa hijab d'in, dik da ba kwalliya taiba tayi kyau sai dai tayi rama idonta dik sunyi zuru zuru fuskan tayi fayau, juyowa tai ga Islam daketa zuba hira da ya nabeel Wanda shi dik Rabin hankalinsa nakan baby dik motsin datai idonshi nakanta, tace "Islam Kaya fa kala d'aya nace ki d'auko min k'ara kullum akawomin in canja amma kin ciko jaka da tarkace harda wasu . . "
Shiru tai bata k’ara saba ganin ya kafeta da ido “ya dai yaya nah?”
Girgiza Kai yai alaman ba komai sai dai fuskanshi d’auke da mirmishi take.
Su Nabeela dasu salma ne suka zo da Kaya breakfast, wai ummynsu tace saita had'a mai abincin rana zata zo tunda jikinnashi da sauk'i.
Ganin dik yara ne isu isu a d’akin yasa ya ta zuba musu abincin ita dashi ta had’a musu tea a Kofi d’aya tazo ta zauna kusa dashi tana bashi abaki inya kurb’i tea d’in itama saita kurb’a sannan tasa cheaf d’in abakinsa itama taci, batare da wata damuwa ba sukaci abinsu suka k’oshi. kowa baiyi magana sai Islam ta karya kai gefe tana fad’in” Allah sarki soyayya jibi Baby bako kunyarmu tasa miji agaba suke cin abinci,kuma ma wani Babban abin tashin hankalin ina gefe sis kin manta dani kinsan sarai banyi break d’inba na fito sabida kince inzo da wuri amma ko kibi ta kaina da Dane kuwa bazaki iya cin abinci ki barni ba”,
Dariya su salma suka farayi yayin da Baby ta mik’e tsam ta tazo ga Islam ta zauna tare da rik’o hannunta tace” sorry sweetyna Allah ba k’yaleki naiba kinga shi bashi da lfy ne shiyasa na fara kula dashi amma daman kema hankalina na kanji,karki damu bari in zubo in baki abaki kinji Yar k’anwata karki fara tunanin harna canja miki”
Abincin ta zubo tazo ta zauna ta d’ora kan cinyarta tace”gashi kici ko in baki. Abaki?”
Dariya tai ta d’auka ta fara ci tana”ai har zuciyata ta fara harbawa da gudu na d’auka daga aure zaki manta dani agefe”
Shima dai ya Nabeel dariya kawai yakewa Shirman Islam don yaga da gaske gasa take sonyi dashi,
Zamansu a asibitin wata irin k'auna da shak'uwar juna ya k'ara musu, don da kowa ya watse zasu kulle k'ofa su bar Abdussalam a reception akan kujera yake kwana su kuwa gadon suke kwana tare dik da ba wani yalwatacce ne ba haka suke mak'ale juna susha soyayyansu,
Azahiri Nabeel ya gaji da zaman asibitin don dik dare saiya Shiga wani yanayi dik yanda yake rage kewa bai gamsuwa dik k'ok'arin Baby na ganin ta rabashi da wata damuwa don yanzu bata mai geji da jikinta dik dare saiya jagwalgwaleta son ranshi suke yin bacci, to amma shi ya damu asallameshi su tafi gida tunda karayar ce kad'ai matsala zata warke agida, da har abbansa yaiwa doctor magana akan abasu sallama amma fir ummynsa ta hana don dik ta gama gano zumud'inshi tasan sarai suka koma gida bazai hakura hannun ya warke ras ba zai fara zalama, don haka tacewa doctor karya sallamesu sai ya warke in sunje gida bazai bi dokokin da akasa maiba,
Yau tunda ya tashi da fishi ya tashi ba fara’a tare dashi ko d’aya ganin haka yasa ta kama kanta bata shishshige maiba dik abinda ya dace tamai tamai ta koma gefan kujera tai zamanta,tana wasa da wayanta, Shi kuwa kwanciyarsa tare da rufe idonsa kamar me bacci nan kuwa bakan Yayi kawai, ita dik saita takura ganin basu saba irin wannan zamanba ad’akin gashi yau y’an dubiya ba Wanda yazo break ma driver ummy ta bawa ya kawo musu, sai wajan sha biyu Aisha tazo nan taji dad’i suka shiga hiransu’Aisha tace”yaya yau bacci yake yi sosai”
“Um” kawai Baby tace taci gaba da hiranta,
Saida yaji an kira sallar azahar sannan ya bud’e idonshi yace”Baby ban ruwa zanyi alwala”
Mikewa tai tsam ta kawo mai ruwa a buta da roba ta taimaka mai yai alwala ya tada sallah, ita da Aisha ma sallar sukai kafin nan sik y’an dubiya sun zazzo harsu mami.
wajan magriba tana zaune itada Islam suna hira don Aisha ta tafi gida, Abdussalam ya shigo yace”yaya ga friend dina zasu dubaka”
Juyowa yai ya kalli baby” ki memo mayafinki ki suturta jikin ki”
Hijab d’in da take sallah ta d’auka tasa tana mamakin wannan hade fuska da yake yi yau.