BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Kusan su bakwai ne suka shigo aka gaggaisa sukai mai ya jiki sannan d’aya yaja musu addu’a aka Shafa suka fita,
Cire hijab d’in tai dai dai lokacin akai kiran sallah ta wuce ta d’auro alwala sannan shima ta taimaka mai yayi alwala sukai sallah.
Ba jimawa su Abbansa da Dad d’in Baby suka shigo Baby ta gaidasu cikin girmamawa Nabeel ma ya tashi zaune ya gaidasu, Abba ne ya kalli Baby yace”khausar wannan ramar da kikeyi tai yawa ko mai ciwon bai kaiki ba ina ganin gobe ki koma gida ki huta kwana biyu Abdussalam yaci gaba da zama dashi har a sallameshi, in yaso kya rink’a zuwa ganinsa”
Da sauri Dad d’inta yace ” a a wane irin ta koma gida in batai jinyar mijinta ba waye ya dace Yayi, wannan ramar tata ba wani Abu bane da an sallamesu zata murmure”
Basu dad’eba suka tafi Islam tabi Dad suka tafi,
Ana sallar isha’i ta mik’e tayi sallar ta shiga ta watsa ruwan sanyi, tasa wata rigar bacci shara ra ta k’ure fanka don yau zafi akeyi hadari ya had’o sosai kuma ruwan bai sauka ba don haka garin yai zafi sosai.
Sanin datai yau acike yake yasa ko kusan gadon bataje ba tai kwanciyarta kan kujera.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
9⃣4⃣
Yinin ranar dik Wanda ya kalli Nabeel yasan cike yake da farin ciki kowa yazo sai yace ‘Nabeel sauki ya samu irin wannan faraa haka’
Yayin da ita kuma Baby ta yini cur da kunyarsa dik iya k’ok’arinsa bata Bari su hada ido har dare kowa ya waste ya rage su biyu ya shiga tsokananta wai tasawa kanta kunya taki kallonsa,
Jin tak’i tanka mai yasa ya shiga tarin k’arya da sauri kuwa ta taso gunsa tana zuwa dama azaune yake ya zubo k’afa funsa tana zuwa yasa ta tsakiyansa ya rungumeta da hannu d’aya , d’an mirmishi tai tace “um yaya nah sarkin wayo”
Cikin muryan shagqab’a kamar yaro ya fara fad’in”to bake ce ba kika kwanta kan kujera kuma kinsan ina son jin d’uminki”
Hannu tasa ta lakuce mai hanci cikin wasa tace”sannu da son jin d’umi na”
Gyad’a kai ya shiga yi yana y’ar dariya, hannunsa na kan mazaunanta yana shafawa,
Ahankali tasa hannunta kan Lip’s d’inshi tana kewaya wa sannan tayo k’asa da fuskanta ta had’a hancinsu bakinta nakan nashi tana ta goga fuskansu daga bisani suka had’e harshensu suka shiga kissing juna ba k’ak’k’autawa, saikace zakin daya samu nama haka suke kissing juna kamar ba gobe ,jin tana shirin fad’uwa yasa tai k’ok’arin janye jikinta ta koma kan kujeran ta kwanta tana maida numfashi ,
Shima zamewa yai kan gadon ya kwanta yana lumshe ido ahankali ya shiga furta”hak’ik’a zuciyata tana sonki baby zan mutu da k’aunarki ina fatan Allah ya had’amu cikin aljanna,ina rok’a miki gafara dikkan zunubanki gurin ubangiji ina fatan Allah yasa albarka cikin rayuwarki baby, kin shayar dani dadin da ban San da irinsa anan duniya ba, kin saka sauki azuciyata a lokacin da zuciyar ke bukatar taimako”
Addu oi sosai Ya rink’a mata na nema mata aljanna gun ubangiji ita kuma cikin jin dad’in adduar take amsawa da’ameen’
Haka suka raba dare suna hira yanata bata labarin yanda zasuyi rayuwa in sun tare agidansu,ita dai mirmishi kawai rakeyi, can taji yai shiru tana kalkonsa taga yai bacci, d’an dariya tai tace” k’ara dakai baccin ai yau hira kawai kakeji tun safe”
Mik’ewa tai ta tofa mai adduoin kwanciya itama ta tofa sannan ta koma kujeran ta kwanta.
Cikin bacci ta rink'a juyo kamar ni shinsa da sauri ta mik'e taje kansa dafe da k'irjinsa ta sameshi yanata salati cikin kid'ima take fad'in"yaya nah meya faru me nene ko ulcer d'inka ce ta tashi?"
D’aga mata Kai yake cikin tsanani ciwo yana nuna mata alamar ta cire mai hannunsa daga ratayen da yake , cikin kuka take girgiza kai dikma ta rasa me zatai mai, da sauri ta bud’e k’ofan ta fita cikin rikita take kiran Abdul da sauri ya tashi yana tanbayarta lafiya? D’akin take nuna mai don haka ya bita suka shiga da gudu,Suna zuwa akafe suka sameshi ya suma da gudu Abdul ya fito zuwa office d’in doctor tare suka dawo nan da nan yashiga dubashi yana gwaje gwaje, nurse d’in dake bayansa ya kalla yace ta d’auko will chair a canja mai d’aki, baby na zaune sai kuka take ta rasa inda zata sa ranta taji dad’i ,tana kallo akazo aka daukeshi zuwa saman bene wani d’aki aka kaishi Kuma suka hanasu shiga haka sukaita zirga zirga daga k’ofan d’akin zuwa bakin benan,
Tunda suka shiga ba Wanda ya fito abinda yafi d’aga musu hankali Kenan, da wani zai fito ai da sunsan halin da ake ciki,to shiru kakeji har aka fara kiraye Kirayen sallar asuba, ganin abun yak’i cinyewa ga baby sai kuka take kamar ranta zai fita yasa Abdussalam d’auko wayansa ya fad’awa Abbansu halin da ake ciki,
Ahaka suka je sukai sallah suka dawo k’ofar d’akin suka tsaya sunata mai adduar samun sauk’i,ahaka Abba yazo ya samesu zai shiga Abdul yace”Abba sunce kar Wanda ya shiga baa shi ga wannan d’akin, ja yai ya tsaya gwanin tausayi,
Ahaka wani doctor ya fito da sauri suka bishi suna tanbayarsa ya Nabeel d’in, baice musu komai ya fara sauka daga kan benan suka bishi har k’asan ita kam baby tana tsaye k’am tana kallon yanda jikin doctor d’in ke rawa harya sauka k’asan,ta tafi dogon tunani ta jiyo k’arant Abdul yana fad’in”doctor kace wai muyi hak’uri yaya Nabeel ya rasu”
Cikin tsananin rud’u ta juyo da kallonta ga k’asan benan gani tai Abba ya dafe kansa da hannu biyu yana juyi cikin firgici, akaro na biyu ta k’arajin muryan Abdul”wayyo Abbah kanaji wai yaya Nabeel ya rasu”
Iya abinda taji Kenan ta yanke jiki ta fad’i sai ganinta sukai tana mirginowa kafan benan har saida tazo k’asa,
Da gudu sukai kanta aka shigar da ita emergency, Wani irin kuka Abdul yake yana kiran sunan Nabeel,
Innalillahi wa inna ilaihi ra’jiun,’kulli nafsin za’ikatul maut’
Nabeel kam ya amsa kiran ubangijinsa sai dai muyi mishi fatan dacewa.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
HADIYYATEE MINNI ILAIKA AGISINI YA RASULILLAHI
HADIYYATEE MINNI ILAIKA ABDULLAHI BIN ABDULLAHI ABU ABDULLAHI
ANA UHIBBUKA YA RASULUL MALAHIMI
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
9⃣5⃣
Dikkan zancan rasuwan Nabeel ya karad’e y’an uwa da abokan arziki, kowa kuka yake yanajin kamar shi kad’ai yai rashi, Abdussalam ma kukan yake yana juya kai fad’i yake”wayyo ni nayi sanadiyyar mutuwar d’an uwana da kaina na shirya wasan dawakai don murna da auransa gashi ya zame min bak’in ciki, wayyo d’an uwana ka tafi kabar zuciyoyinmu cikin tsanani da kewanka.
Kowa ka gani cikin tsananin tashin hankali sabida Nabeel mutum ne me wasa da barkwanci ga son mutane da zumunci yana son y'an uwansa so na hak'ik'a yanda yake wasa d k'annansa zaka d'auka abokanshi ne don haka suka shak'u da juna suke sonshi matuk'a suma.
Kowa ya k’ara so asibitin yace ina Baby in akace ta suma tana gun likitoci sai kukan ya tsananta,shi kanshi Dad d’inta yana zuwa ita yake Tambaya don yasan tana cikin wani yanayi mawuyaci,da akace ta suma ji yai ya k’ara shiga tashin hankali,
Ahaka dai aka bada gawar Nabeel akai gidansu da ita tare da d’unbin jama’a, ganin hankalin kowa naga gawar yasa hajiyan Bilal cewa ita zata zauna gun Baby kafin ta farfad’o su tawo gidan.
To kamar yanda addini ya tanadar haka akaiwa Nabeel wanka da sallah aka kaishi ga makwancinsa????.Allahu Akbar rayuwa Kenan kowa yazo saiyya koma yanzu dai gashi Nabeel ya tafi yafiyar da bazai dawo ba,
Allah yasa mutafi asa'a mu tarda alkairi.
Agefe Aisha Islam da Nabeela zaune dikkansu sun had'a kai da gwiya kuka suke kamar ransu zai fita ummyn ya Nabeel datafisu dauriya ta kallesu da sigar rarrashi race"kuyiwa Nabeel addu'a ayanzu ita yafi buk'ata ba kuka ba kuyi hak'uri nasan sabo kukewa kuka amma Nabeel kam ina sa ran aljanna ce makomarsa domin biyayyar da yaimin bazata tashi a banza ba. . . . ." itama kukan ne yaci k'arfinta tai shiru,
Mami kuwa dik hankalinta naga Baby tunda aka fita da gawar Nabeel kuma ta maida ranta can don haka ta yafito Islam da Aisha tace musu su tafi asibitin gun Baby su kula da ita dik da dai hjyn Bilal nacan amma dai sud'in zaifi kyau ace suna kusa da ita.
Suna zuwa asibitin hjy Amina ta taho gidan rasuwar ta barsu, dik cikinsu bamai iya mai cewa k'ala sai dai kuka kawai,
Har dare bata farfad’oba don haka dik su biyun suka zauna tare da ita,
Cikin dare ta farka da surutait fad’i kawai take”yayanah yayanah kazo don Allah ka dawo gareni yaya Nabeel kacewa Abdul karya k’ara cewa ka rasu, kacemai da ranka kana tare damu yauma za’a sallamemu mu wuce gidanmu musha soyayyanmu kamar yanda kake fata, yayanah don Allah kazo ka kama hannuna injika kamin magana inji muryanka ina sonka fa kaima kasani sosai nake sonka” dik abinda take idonta a runtse yake tanata juya kanta idonta na anbaliyya da hawaye,
Dikkansu Islam kuka suke rik’e da hannayenta sun kasa cemata komai har saida likitan yazo ya mata allura sannan bacci ya k’ara d’aukanta agalabaice.