BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Taku ce
Layuza kabir Adam ????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

           9⃣6⃣

To yau da gobe haka baby ta ci gaba da karatunta zuciyanta cike da k’unci da rashin sukuni dik da kaso da yawa cikin damuwanta iyayenta da ya’n uwanta sunyi nasarar rage mata ita, amma abinda basu sani ba shine gabansu ne take sakewa ta cirewa ranta Damuwa amma da zaran ta keb’e ita d’aya tofa zata Dasawa ranta tunaninshi da tino irin rayuwan da sukai da zamansu na asibiti to daga haka fa sai kuka shike nan zata rasa nutsuwarta,

Vidio d’in bikinsu kuwa tun daga na day one har zuwa randa ya sami tsautsayin nan haka ta had’o Kansu tasa acikin kayanta tana so ta kalla amma tana jin fad’uwar gaba dik sanda ta d’auko da niyar hakan sai dai ta mayar amma fa photo kallonsu har ba iyaka,

Ahaka ranar wata alhamis sun dawo a skul da sauri ta shige toilet tai wanka ta fito ta zauna ta fara tsantsara kwalliya haka kawai yau take jin wani nishad'i Wanda ita kanta bata San dalili ba, 
 Shirya kanta tai cikin wasu riga da wando na kiran Pakistan ta taje gashin kanta ta d'auko ribom kalan kayan tasa tasa d'an kunne da sark'a  fation  ta fito farlou Islam na zaune tana cin abinci ta bita da wani kallon mamaki don raban Baby da kwalliya tun rasuwan Nabeel ko skul haka take tafiya ba ado ba komai sai dai kawai tai wanka tasa kaya dik wannan adon babu shi, bata tanka mata ba har tazo ta zauna kusa da ita fuskanta d'auke da fara'a tace"sis shine biki jirani ba kike cin abincin ko?"

D’an mirmishi Islam tai tace” naga Kin haye sama tun d’azu shiyasa na fara ci nai tunanin baki jin yunwa ne”
Gyad’a kai kawai Baby tai ta jawo kulan abincin ta zuba ta fara ci fuskanta d’auke da mirmishi, abin yai matuk’ar d’aure mata kai wasu bak’in abubuwa take gani tare da Baby Wanda ta dad’e da daina ganinsu,
Sai bayan sun gama cin abincin sun dawo kan Kujeru sun zauna Islam ta kalli Baby tace”wai yau meya faru dake ne nake ganin nishad’i k’ara ra tattare dake kodai kodai?”

Mirmishi tai tace”wlh Nima bansan dalili ba kawai yau jina nake cikin farin ciki”
“To Allah yasa farin cikin ya dawo Kenan sis”
” hhhmmmmm”
kawai tace ta zubawa t.v ido suna nan zaune suna hira zinbir Baby ta mik’e Islam tace ” ya dai sis?”
Da gudu tai up stairs tana fad’in”ina zuwa Abu Zan d’auko”

Dawo wa tai d’auke da flat na c.d a hannunta guda biyar tana zuwa ta d’auki guda d’aya tasa ta danna play ahankali wak’an bikinsu ta fara tashi daga bisani bayan wajan 3 minutes hotuna suka fara bayyana kan t.v d’ina dik na gun kilisa ne an nuno pic’s kusan guda Hamsun na mutane da Kuma nata da Nabeel tare da hoton dawakai,
daga ita har Islam d’in sunyi tsit dik attention d’insu na ga t.v d’in Wanda fad’uwar gaba dik ta cikasu da rauni a zukatansu musamman ma Baby da har ilahirin jikinta ya fara d’aukan rawa, bayan dik photos d’in sun gama wucewa sai kuma aka fara hasko kilisan inda dawakai suke tafka gudu cikin fili haka Tiryan tiryan aketa hasko dik abinda ya faru gun kilisan, zuwa lokacin dik fuskokinsu sun jik’e da hawaye Baby harda shishik’a, kamar an hankad’o haka aka hasko lokacin da dokinnan ya suri Nabeel yai sama dashi yana juyi dashi cikin filin, wata k’ara Baby ta saki yif kakeji ta fad’i, cikin gigita Mami da take shirin shigowa parlour ta k’araso da Sauri, cak ta d’aga Baby sukai waje tasa ta mota sai asibiti,ba’a sha wahla ba ta farfad’o amma da ciwon k’irji Wanda ta samu tun rasuwar haka sika bata magunnuna da allurai aka sallamesu suka dawo gida ana sallar isha’i suna shigowa ta kwanta don bacci ne a idonta sosai sabida alluran da sukai mata, har Dad ya shigo ya gyara mata kwanciya don tare suka dawo daga asibitin,

Da asuba Dad nayin salla ya shigo part d’in don ganin jikin Babyn azaune ya sameta kan sallaya tana lazimi tana ganinshi ta shafa ta gaisheshi cikin girmamawa ya amsa yana tanbayarta jikin ta tace da sauk’i,nasiha ya k’ara mata sosai akan tayi hak’uri da rayuwa dik yanda tazo mata taci gaba da yiwa Nabeel addu’a,
Idonta cike da hawaye ta d’aga Kai alamar tom,
Haryaje bakin k’ofar fita ya juyo yace “sannan kiyi hak’uri da kallon video d’in bikinku da dik wani Abu da zai tinasar dake mutuwar Nabeel kinji Baby “
D’aga kai kawai tai don kuka yaci karfinta Dad na fita ta kifa kai taci gaba da rusar kuka cikin tausayin kanta.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAN

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

        9⃣7⃣

Asubar fari Bilal yaiwa gidan tsinke cikin yanayi Mara dad’i domin kuwa a galabaice yake ya rame Yayi bak’i Yayi ba kyan gani dai abin,ba k’aramin tashi hankalin Dad da hjy Amina yai ba sabida Wanda bai San Nabeel sosaiba bazai ganeshi ba, cikin kid’ima Dad ya rungumeshi yana fad’in “My son meke faruwa dakai meya sameka haka kai wannan ramar da bak’i haka ko rashin lafiyar ne”
Cikin yanayi na galabaita ya gyad’a kai alamar eh.
Rungumoshi yai yashiga dashi d’aki jikinsa sai rawa yake ya d’auki waya yakira family doctor d’inshi,
Hjy Amina daketa kuka taja numfashi tace”Alhj ina ganin kawai mu kaishi asibitin basai munjira zuwan doctor d’inba”
“A a bari dai yazo ya dubashi inya kama akaishi can to sai akaishi”

 Ba'afi 20 minutes ba Doctor d'in ya k'araso da Kayan aikinsa nan da nan ya shiga dubashi tsawon lokaci ya kalli Alhj yace"  gaskiya da matsala  Alhj ina ganin mu wuce dashi asibitin"

Nan hankalinsu ya k’ara tashi Dad yace”To doctor fatanmu dai yasami lfy”.

   Bayan tsawon bincike doctor ya tabbatarwa da Dad cewa Bilal ciwon zuciya ke damunshi kuma ya samu ne sakamakon wata damuwa daya sa aransa don haka yana da kyau aguji b'ata ransa Kuma arink'a bashi dik abinda yake so.

Sosai hankalin su ya k’ara tashi Dad yace”yanzu doctor baka ganin akwai wani Abu da za’ayi ya rabu da wannan ciwon?”
Gyara glass d’in idonsa yai yace “to agaskiya Alhj idan irin wannan ciwon ya kama mutum rabuwa dashi lokaci guda yanada wahla musamman ma na Nabeel Wanda abinda bincike ya nuna ba wai yanzu ya kamu da ciwonba ya dad’e yana cinsa ahankali yanzu ne Yayi k’arfi ajikinsa don haka kawai za’a d’orashi akan magani kuma a kiyaye dikkan abinda za’a tab’a ransa”

Haka suka dawo gida jikinsu dik amace hankalinsu bai tare dasu,kasancewar anwa Bilal allurar barci yasa ya kwanta yake ta fama.

Dad ne ya shigo ya k’ara duba jikin Baby yake sanar dasu abinda ke faruwa da Bilal da zuwanshi gidan, cikin yanayin jimami da tausayawa Mami take cewa Dady”To Alhj yanzu me kake tunanin yana damunsa,kodai akwai wani Abu da yake nema ba’a mishi ba?”
Girgiza kai yai yace”bana tunani Bilal nada matsalar wani Abu daga b’angaranmu sai dai ko da wajan aikinnasu yake da damuwa amma dai ki bari so nake ya farka daga barcinnan ko zuwa gobe ne zan tanbayeshi”
Jiki ba k’wari Mami ta shiga part d’in su Bilal ta jajantawa hjy sannan ta lek’a d’akin Bilal d’in ta ganshi yana barci kamanninsa dik sun canja.

Washe gari Jikin na Bilal ba laifi yafi jiya amma dik da haka inka kalleshi baza ka so ka k'ara ba,bayan an tursasa mai ya d'anci abinci hjynsa ta bashi magun gunan yasha likita yazo ya k'ara duba jikin nasa  yatafi,
 Mami tazo ta duba shi Islam ma ta shigo ta mai sannu data dawo d'aki tace"sis kije ki duba jikin broth gaskiya yana cikin wani yanayi sosai"ta k'arashe zancan tana  share hawaye ganin haka yasa jikin baby yai sanyi matuk'a ta mik'e tana fad'in"muje in dubashi"

Bayan sun shiga ta zauna kan kujera idonta akansa ya bata tausayi matuk’a ganin ramar da Yayi tace” broth sannu ya jikinnaka”
Idonshi a lumshe ya amsa da”jiki da sauk’i Baby”
“To Allah ya k’ara afuwa yasa kaffara”. “Ameen na gode”
Sun d’an zauna ta mik’e da tacewa Islam”sis tashi muje inaso in kwanta”.

Dad ne yazo yasa Bilal agaba da magiya  akan ya sanar dashi damuwansa amma fafir Bilal ya dage akan shi bashi da wata damuwa ko kad'an, hjy tasa kuka tana fad'in" don Allah don Annabi bilal  ka fad'amana damuwarka wa kake dashi da zaka fad'awa bayan mu ka taimaka ka fad'a mana komai kake so Bilal Kaine sanyin idaniyata fa"

Maimakon yai magana kawai saiya fashe da kuka mai tsanani har yana shid’ewa, rarrashinsa Dad ya shiga yi yana shafa bayansa shima idonshi cike da k’walla.

Bayan  kwana  biyu Dad ya gama yanke shawarar tafiya k'asar India domin yaje ya had'o dikkan takardun Bilal don yasa aranshi bazai tab'a kara bari Ya koma k'asarba ya gama zamanta Kenan tunda ya fuskanci a can dik ya d'auko wannan mugun ciwon da yake Neman kaishi lahira.

Takuce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????

BABY KHAUSAR

        NA  

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
????????????????????????????????????✍

      9⃣8⃣  

Dad shi kad’ai ya tafi batare da ya fad’awa Bilal inda zaije ba yadai cemai zaiyi tafiya kwana uku zai dawo,
Da tsakar rana suka sauka a k’asar don haka Kai tsaye Dad ya wuce gidan Bilal Wanda yake na ma’aikatarsu ne kasancewar sun sanshi sosai yasa gardmans d’insu sukai mai iso har cikin gidan, bayan sun bud’emai ya shiga suke sanar dashi Ai Bilal d’inma baya nan tsawon kwanaki, bayan ya zauna yake amsa musu da eh yana can gida Nigeria,
To wanka ya samu Yayi yana fitowa ya tarda sun kawo mai copy da gurasa sama sama ya tab’a yace su kira mai kamal abokin Bilal Wanda good gidanshi ke jikin na Bilal d’in shima d’an Nigeria ne tare suka fara karatu da Bilal har yanzu da suka sami aiki suna tare kasancewar su musulmai kuma hausawa y’an k’asa d’aya yasa suka rik’e juna matsayin y’an uwa ba abokai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button