BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin girmamawa Kamal ya gaida Dad yana tanbayarshi jikin Bilal ya amsa mai da sauki, Bayan shiru na d'an lokaci ya biyo baya Dad ya gyara zama yana fuskantar kamal yace"kamal na taho ne takanas k'asar nan domin naji abinda nake nema daga gareka, hak'ik'a kai kad'aine me bani wannan amsar, shin kamal meke faruwa da rayuwar Bilal a k'asar nan me yake damunsa harya haifar mai da ciwon zuciya shin ko yana da matsala da wajan aikinsa ne? Ka fad'amin komai karka b'oyemin har inka d'auke ni matsayin da Bilal ya d'aukeni ina sauraranka"
"Tofa anzo wajan" cewar kamal cikin ransa domin daman ya d'aukarwa ransa alk'awarin matuk'ar suka had'u da dangin Bilal bazai b'oye musu damuwar d'ansu ba muskutawa yai ya nad'e k'afa sannan ya fara magana"To zance na gaskiya Dad ciwon Bilal ya samo asali ne tun tsawon lokaci tun bamu gama karatunmu ba yaje gida Hutu ya dawo sai naga ya dawo da canjin rayuwa ba kamar da ba mutum me kuzari da k'arfin zuciya amma dik sai abin ya canja ya dawo me sanyi me yawan yin shiru da damuwa, koda yaushe ina tanbayarshi meke damunsa amma sai yace ba komai kasancewarsa me zurfin ciki don haka nasa mai ido har wata rana na shigo gunsa inata mai magana baijiba ya zubawa wayarsa ido na k'wace wayar sai naga photos d'in wasu y'an mata yake kalla guda biyu na sami gu na zauna ina tanbayarsa suwaye sai yace min k'annansa ne Baby da Islam nan dai na takura mai da bincike saiya ke bani tarihin rayuwarsa da Baby tun daga haihuwarta har irin azabtar da ita da yai shida mamansa daga k'arshe dai ya shaida min zuciyarsa ta kamu da k'aunarta kuma yasan har abada bazata tab'a yarda dashi ba, nan dai na kwantar mai da ahankali akan ya barta zuwa wani lokaci tunda naga har alokacin yarinyace Kuma ma tana secondary skul ne da sauranta, to ahaka yad'an samu nutsuwa yana kiran Islam awaya suyi ta hira inya ce ina Baby tace gata amma saiya kasa cewa ta bata wayan su gaisa sai dai yace ta gaisheta kawai, bayan tsawon lokaci ya sami labarin za'aimata aure da Nabeel tun daga ranar ya kwanta rashin lafiya kusan ma satinsa biyu a asibita da kyar ya farfad'o suka sallameshi ahaka yake kwance yau da lafiya gobe babu ya rame ya k'anjame har zuwa ranar daya lallab'a ya taho bikin to sanda ya dawo adaranma a asibiti ya kwana sabida masifar ciwo ga aman jini da yarink'a yi tun asannan suka sanar dani ciwon zuciya yana daf da kamashi nan suka d'orashi kan magani muka dawo sai yaza mana ko aiki bai zuwa suka bashi Hutu har ya warke Amma kullum ciwo gaba yake in nai yunk'urin sanar dakai saiyaita ban hakuri yana min kuka kan kar in fada maka don fadar baida anfani,to randa muka sami labarin rasuwar mutuwar mijin Baby nikam naita murna akan zata dawo gareshi amma shi sai naga ma kamar hankalinshi ya k'ara tashi nan yake fad'amin ai ko bata da aure bazai aureta ba don yasan bazata tab'a zama dashi ba ta tsaneshi don haka ma shi ya cireta aransa da maganar soyayya, dik da nasan k'arya yake amma saina bishi ahaka , kamar abin arzik'i ya cire damuwa aransa Ya koma bakin aikinsa tsawon watanni kawai muna office ya yanke jiki ya fad'i ana kaishi asibiti suka tabba tar zuciyarsa ta tab'u sosai, ina dawo wa naje namai bukkin jirgi na ran Monday ai kuwa cikin ikon Allah Dana koma asibitin na tarda ya farka harya dawo hankalinsa namai sannu ya amsa nan na shaida mai munyi waya dakai kace ya biyo jirgi cikin satin yataho gida baiyi musu ba don tunaninshi da gaske nake Kaine kasani,to ahaka bayan kwana biyu nakaishi airport ya hawo jirgi ya taho wannan shine abinda nasani Dad".
Cikin mutuwar jiki da tashin hankali k'arara Dad ya ke girgiza kai yace"na gode kamal na gode sosai kuma abinda nake so ka rakani gun aikin naku zan had'a dikkan takardun Bilal in tafi dasu domin yabar zaman k'asar nan har abada gida zai koma da aiki kuma insha Allah zan Aurawa Bilal khausar zan rabashi da wannan ciwon indai don Baby ya kamashi.
Cikin kwana biyu Dad ya gama had'a dikkan wani Abu mai mahimmanci na Bilal ya taho da tabbacin yana dawowa gida zai aurawa Bilal Baby,
Cikin dare ya sauka yana shiga gidan ya sami jikin Bilal ba dad’i matuk’a don sai aman jini yake yana kakkafewa hjy ta sashi agaba sai gursheken kuka take,cikin kid’ima ya d’aukeshi sukai asibiti nan akai kanshi da taimakon gaggawa amma Abu yaci tura daga k’arshe ma sai yashiga commer gaba d’aya zuciyan ta tsaya .
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION
???????????????????????????????? ????✍
Masoyan Baby khausar
ina Baku hak’uri da Lank’wasashshiyar murya kumin afuwa naji na shiru wlh abu buwa ne suka min yawa, ???? kusani kuna raina har abada muna tare????.
9⃣9⃣
Dikkan Wanda ke gidan hankalinsa a tashe yake har Baby Wanda ita kanta ba ishashiyar lafiyar gareta ba ciwon Bilal jitai ya danne nata musamman da Dad ya kirata awaya taji yanda yake kuka yana fad’in “Baby kiyiwa d’an uwanki addu’a yana buk’arat addu’a awannan halin don babu tabbacin Bilal zai wayi gari nikam na fidda rai dashi sai dai ince Allah ya bada sa’ar tafi . . . . . ” maganar ta tsaya sanda wani wawan kuka yaci k’arfinsa ya kashe wayan, itama rik’e kanta tai da hannu biyu tana zubar da wasu hawaye masu ciwo ga kukan Dad daya tab’a zuciyarta ga tunanin halin da Bilal yake ciki, dik da har zuwa yanzu ba wai ya ta daina tsanarsa dika bane kawai dai tasan tsanar ta ragu amma wani sashi na zuciyarta yana tuna mata matsayin Bilal gareta da yanda Dad d’inta yake bata labarin irin son da yakewa d’an uwanshi wato mahaifin Bilal yasha fad’a mata irin hidimar da yayanshi yai dashi da irin gudunmawar daya bawa rayuwarsa, yana fad’a mata tun bayan rasuwar yayanshi ya maida sonsa ga y’ay’an yayan nasa musamman ma Bilal da kamanninsa da d’an uwan nasa sun b’aci don haka yana son Bilal matuk’ar so, tunowa datai da wannan maganganun na Dad d’inta yasa ta mik’e da sauri ta shiga toilet ta d’auro alwala ta tada sallah,addu’a sosai ta rink’a yiwa Bilal tana nema masa sauk’i gurin Allah.
Yanda suka ga rana Dad da hjy Amina haka suka ga dare sunyi kukan sunyi sunyi harsun gaji Ganin ba mai bada magani sai Allah yasa Dad ya shiga masallaci yaita sallah yana addu'a ga Bilal ita kuwa momyn nasa tana nan zaune a kan benci intai kukan tai saita koma taita addu'a don an hanasu shiga ma inda yake an kaishi wani d'aki na
musamman Wanda dik cike yake da na’urori,
B’angaran mami ma dik bayan d’an lokaci tana kiransu a waya taji halin da ake ciki kuma itama daga nan gida tana nan tana ta masa addu’a.
Har wayewar gari babu sauk'i ko motsi baiyi ba don haka babu maganar kwanciyar hankali ko kad'an tare dasu, don haka Dad ya yanke shawarar fita dashi k'asar Egypt don yana ganin zaifi samun kulawa a can d'in tunda su suna da Kayan aiki sosai da k'wararrun likitoci, (Abinda ya manta ko a ina yake sai Allah yaso zai bashi lafiya).
To zuwan mahaifiyar Bilal tare dame gidanta ya k’ara karya zuciyar momyn Bilal don tana ganin yayar tata ta k’ara fashewa da kuka tana fad’a mata halin da yake ciki babu alamun Bilal zai tashi(Tsananin ciwo ba shine mutuwa ba y’an uwa,kuma lafiya ba ita ke nuna doguwar rayuwa ba.)
Hjy Halima cikin dakiyar zuciya da tawakkali ta shiga kwantar da hankalin k’anwar tata tana rarrashinta, shikuwa Dad yana can ya fara musu cuku cukun fita Egypt d’in kwana kusa.
Me gidan Hjy Halima ne yasamu Dad ya zaunar dashi yashiga yimai nasiha yana tuna tar dashi shi Musulmi ne ya maida lamarin ga Allah zai Isar masa shi maji rok’o ne akowane lokaci zai Iya bashi lafiya don haka abi komai asannu,maganar fita Egypt d’in nan adakata aga yanda Allah zaiyi zuwa kwana biyu. kasancewar Aminun yayansa ne yana ganin sa tamkar yayan nashi yasa yake nutsuwa yaji maganarsa don haka yanzu ma shiru yai yana nazari dik hankalinsa bai tare dashi.
Tsawon kwanaki biyun babu wani ci gaba dik jikinsu ya mutu sun fidda tsanmani gareshi,haka dik Wanda yazo dubashi sai dai ya lekashi ta window don baa barin shiga gunsa, dik Wanda yazo sai kaga yana zubda hawaye ganin irin tarin injinan dake kewaye dashi tun daga ka har k’afa,
Su Baby kullum suna zuwa asibitin ita da Islam tana gani in sukazo yanda Islam da maminsu zasuyita goge hawaye suna b’oye kuka sabida tausayin halin da yake ciki amma ita kam sai dai taita binsu da ido,harga Allah tana tausayin Bilal Kuma tana mai addu’a amma tafi tausayin kanta da halin da take ciki sabida tana ganin tashi zuciyar ciwo n kawai daga Allah ya kamashi amma ita tata ciwo ne me ciwo ciwo ne Wanda baida magani ciwon rashin masoyi rashi na har abada Wanda babu magani sai dai hakuri, amma shifa ciwonshi me magani ne ko yau akai dace sai asamo maganin da zai warkar dashi don haka tana ganin kanta zata kokawa ba wani ba.
A kwana na hud'u da shigar Bilal commer ne aka bawa Dad dama ya shiga gareshi don ya damu yashiga, yana zuwa Kansa ya fashe da kuka yana fad'in"Tashi Bilal tashi kaji don Allah ka tashi kaji albishir d'in da zan maka na samo ma maganin ciwonka Nazo da k'arfina in shaida maka na baka ita har abada amma na riske jikin naka ba dad'i,inma na fad'a bazaka jini ba baza ka gane ba, Bilal ka tashi don Allah, hak'ik'a yau d'innan Zan cika alk'awari yau zan aura maka ita k'ara ace ko bayan awa d'aya da aura maka ita ne kabar duniya bazanyi bak'in ciki me yawa ba nasan na sauke wannan nauyin na had'a ka da it - - - - -"
Jin yanata surutu kamar zautacce yasa likitan ya kamoshi ya fito dashi yana kuka tamkar k'aramin Yaro,
Dad ya nemi zama da Mami,hjy Amina Hjy Halima da me gidanta, malam,sai kuma babban amininsa Alh Bello yakasai,
Bayan kowa ya maida hankali gareshi ana sauraran abinda zaice, batare da Jan batunba ya warware musu dikkan musabbabin ciwon Bilal da kuma hukuncin daya yanke na d'aura auran Bilal da khausar a yau d'innan da yardar Allah,
To ganin irin mawuyacin halin da Bilal d'in ke ciki na rai kwakwai mutu kwakwai yasa ba Wanda yai yunk'urin kawo wani wani nak'ashu cikin maganar sai dai Fatan Allah ya sanya Alkairi yasa ayi asa'a.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(We are here to educate,motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????????
1⃣0⃣0⃣
To da gaske dai magana ta mik’a tunda gashi Dad ya d’au waya ya kira dikkan Wanda ya dace ya shaidawa ya fad’i Abu kamar almara zaa d’aura wuran khausar da Bilal.
K’arfe hud’u da kwata bayan idar da sallar la’asar muta nan da basu wuce hamsin ba suka shaida daurin auren Baby da Bilal, Wanda da yawan mutane dik wanda yaji batun auran sai ya shiga mamaki da al’ajabi wasu na fad’in dama rabon Bilal ne ya kashe Nabeel to Allah yasanya alkairi.
Dik bidirin da ake tsakanin angon da amaryar ba Wanda yasani tunda shi ango ba lafiya ita kuma amarya bata San wainar da ake toyawa ba, sai da dare Dad ya shigo gidan jikinsa dik asanyaye Baby ta bishi da kallo na tausayin mahaifin nata dik ya rame ya susuce ba wani nutsuwa tare dashi tun rashin lafiyar Bilal, ta kalleshi da kauna irin ta tsakanin d'a da mahaifi tace"Dad sannu da zuwa ya jikin broth d'in"
Waje ya samu ya zauna yana cire hularsa yace”yawwa sannu Baby jikin Bilal to gashi dai Kunlun muna nema masa sauk’i gun ubangiji”.
“To Allah ya bashi lafiya”
“Ameen amma ina ganin ma sauk’in yazo da yardar ubangiji tunda mun gano maganin matsalarsa kuma mun had’ashi dashi”
D’ago kai tai sosai ta kalli Dad sannan tace”Dad meye ne musabbabin wannan ciwon nasa?”
Shiru yai can yace”to abinda dik Abokinsa ya shaida min shine wata Yarinya yake tsananin so tun tsawon shekaru kuma yana tunanin bazai samu soyayyar taba don haka ya kasa sanar Mata har aka aurar da ita, to shine tun lokacin zuciyarsa ta kamu”.
Cikin jin tausayinshi ta girgiza kai”kai amma shima broth Yayi k’auran baki daya sani ya sanar da ita bai sani ba ko za’a dace”
D’an mirmishi Dad yai yace”to kinaji nace miki har an aurar da yarinyar fa”
“Wayyo bashi da rabo ne Allah ya musanya mai da mafi alkairi”
“Ai Baby ita d’in dai itace alkairin gareshi don mun sami tabbacin yanzu babu aure tare da ita don haka zamu nema mai aurant- – – -“
Sakkowar Islam parlourn ya katse musu hiran tace” Dad sannu da zuwa,yame jikin?”
“Da sauk’i Islam ina mamin naku ne?”
“Tana d’akinta Dad”
Mik’ewa yai ya haye up stairs,
Baby ta kalli Islam tace”sis kinsan meke damun broth Ashe ciwon so ne “nan dai ta fad’a mata dik abinda Dad ya shaida mata ta d’ora da fad’in” wlh harna k’ara jin tausayinshi Ashe ciwo d’aya ke damun mu,ko dake k’ara shi tunda gashi ance yarinyar ma sun rabu da mijin nata kinga da alamun zata Iya zama rabonsa ni kuwa fa har abada babu abinda zai cike wannan gurbin na rashin masoyi” ta k’arashe maganar tana goge k’walla.
Dik wata kafa da Baby zata San an d’aura mata aure da Bilal an toshe ta don dik Wanda yasan maganar ana fad’a mai karya sanar da Babyn don bata sani ba tukun, mami ta sanar da Islam da Aisha sannan ta gargad’esu da kada su bari wani yaiwa Baby zancen koda sunje skul suyi taka tsantsan.
Wasa wasa saida Bilal ya kwana goma cikin commer sannan ya farfad'o Dik da ba wai da wani sauk'i sosai ya farko ba amma dai yanzu yana motsa har yana bud'e ido ya kalli kowa amna ba baki kuma baya Iya tashi sai dai a d'agashi a kwantar.
A yaune Mami ta shirya sanar da Baby halin da ake ciki don haka ta kirata d’akinta tazo ta sameta zaune bakin gado, waje ta samu ta zauna kan kujeran dake kallon gadon tana d’an mirmishi tace”mami nah Allah dai yasa lafiya”
D’an mirmishin itama tai tace”lafiya qlau Baby sai dai inaso ki ban hankalinki nan don magana zamuyi me mahimmanci sosai”
Jin batun mami yasa Baby komawa serious ta k’ara gyara zama tana fad’in”to mami ina jinki”
Mami ta kalleta sosai sannan ta fara"khausar meye matsayin Dad d'inki gareki Kuma Nima wane matsayi kika ajiyeni?"
Cikin yanayin tsoro ta kalli mami sannan tace"mami Dad ubane gareni Wanda yake k'aunata yake son farin cikina,ke kuwa uwa ce gareni baya Goya marayu me tattalina da tarbiyantar dani me son ganin cigaban rayuwata, mami keda Dad banda kamarku har abada"
Jinjina kai mami tai tace”to khausar har in matsayinmu yakai kiyi mana biyayya to wannan karon munzo gareki da Neman alfarma bada umarni ba munzo ki rufa mana asiri ki tallafi rayuwar d’an uwanki ki ceci ran dake Neman cetonki ki taimakawa zuriar gidanku ki faranta ran mahaifinki danawa ki amince da duk abinda zan fad’amiki, khausar nasan abin zaizo miki awani irin yanayi amma kiyi hak’uri ki d’auka k’addaranki ne ahaka kinji Baby nah”.