BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Dik wata Kaduwa Baby ta gama yi dikda bata San me Mami zata ce ba amma tasan abin gagarumi ne matuk’a,
“Mami wai meke faruwa ne? Me nayi kodai wani laifin nayi muku ki sanar dani da gaggawa mami in nemi yafiyarku wlh kin sani cikin rud’ani”

“Kwantar da hankalinki Baby bikiyi mana laifi ba mune muka yanke miki hukuncin da nasan bazai miki dad’i ba amma kiyi hak’uri da abinda zakiji kinji yarinyar kirki, khausar mahaifinki ya d’aura miki aure da Bilal tun sati d’aya daya wuce”.

Agigice ta mik’e tsaye tana fad’in “me kikace mami me kunne na ke jiyemin? Wayyo Allah nah rayuwata wayyo yaya Nabeel d’ina”
Ganin bata cikin hayyacinta yasa mami ta mik’e ta rungumota jikinta tana bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi take fad’in”cool down Baby nah yi hak’uri kinji kwantar da hankalinki yi shiru”
Kuka take sosai tana shishshik’a dik jijiyan kanta ta tashi takai tsawon lokaci tana kukan daga bisani bacci ya d’auketa don ita d’abianta indai tai kuka sosai to sai tai bacci, ahankali mami ta zame ta kwantar da ita kan gadon,ita kanta mami k’walla take na tausayin Baby domin tasan dole zata shiga wani hali. Islam ce ta shigo tana cewa”mami Baby fa najita shiru”
“Islam bar Baby anan zata kwana jeki kwanta ke”

Da asuba mami ta tashi tai sallah Baby bata farka ba har wajan shida ganin lokaci nata k’urewa karta makara da sallah yasa ta tashe ta, mik’ewa tai tana salati daga nan ta shige toilet ta d’auro alwala tana idar da salla kuwa ta shiga kuka tana Neman zab’i gun ubangijinta, mami tazo kusa da ita ta zauna tana rarrashinta dayi mata nasih,ta d’ago rinannun ida nunta tace”mami Dad fa da kansa yace min ciwon so ke damun Broth har yasa mai ciwon zuciya to meyasa zai had’ani dashi bayan yasan daman can bawai sona yake ba yanzu inyaji an d’aura mai aure dani ai k’ara tsanata zaiyi, amma shike nan mami zanyi muku biyayya zan zauna dashi bisa umar ninku”
“Baby ki daina fad’in haka ki daina cewa Bilal bai sonki shi masoyinki ne na har abada kuma wadda kikaji Dad d’inku na fad’in Bilal naso ba kowa bace face ke kece zab’insa ciwon sonki ne yasashi a wannan yanayin, don haka ki taimakeshi Baby ki yarda zakiyi ingantaccen zaman aure dashi, sabida Baby in kika k’i amincewa dashi duniya zata zageni za’ace ni nake zugaki kinsan dai mutane za’aga kamar ban miki tarbiyya ba”.

“Shi Kenan mami na amince nayi muku biyayya banda kamarku nan duniya Ku iyayena ne yazama dole inyi biyayya gareku na amince da buk’atarku mami”. Dik maganan da take cikin kuka takeyinta Kai daka ganta kasan tana cikin tashin hankali,
Kauda kai mami tai tanata matsar hawaye.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION
(We are here to educate, motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍

            1⃣0⃣1⃣

To fa Baby ciwo ya dawo mata sabo bata da wani aiki sai kuka abinci ma sai mami tayi da gaske take ci tasa aranta bata da wani farin ciki a duniya don haka tasawa zuciyarta cewa zataita rayuwa ne cikin k’unci da ba’kin ciki, Dad sata yake agaba yaita bata hak’uri yana cewa”kiyi hak’uri Baby ban aura miki Bilal don na bak’anta ranki ba sai Dan inajin akwai alkairi tsakaninku, kiyimin Biyayya Baby zaki dace arayuwarki dikkan d’an da yai biyayya ga iyayensa hak’i’k’a baya tab’ewa” iri iren kalaman Dad da mami suke d’an sassauta mata ranta har take k’ara sawa ranta dole tai biyayya garesu.

A b’angaran Bilal kuwa sauk’i yanata samuwa Alhamdulillah don yanzu yana tashi ya zauna yaci abinci har in anyi magana yakan bada amsa don haka koda yaushe suke k’ara godiya ga Allah,
Bayan sati biyu da farfad’owarsa ya warke Yayi ras don haka aka basu sallama suka dawo gida, tun safe aka sallamosu har dare yanata baza ido yaga Baby ta shigo dubashi amma shiru don tunda ya dawo hayyacinsa sau biyu yaga tazo asibitin kuma zuwanta yaga alamar tausayinshi a idonta amma daga nan bai k’ara ganinta ba gashi ya dawo gidanma ba ita ba dalilinta sai Islam ce keta zirga zirga agunsa yana so ya tanbayeta ina Baby amma yana jin sashin zuciyarsa na gargad’ar sa, don haka yaja bakinsa yai shiru,

Ita kuwa Baby tunda taji an sallamosu ta kwanta zazzab’in k’arya don bata son mami tace taje gareshi don har ranta bata son ko ganin fuskarshi.

Washe garin dawowarsu Dad ya Tara kowa na gidan tare da Alhj Bello mahaifin Marigayi Nabeel, sai Abban Aisha da kuma abokin Bilal wato kamal daya zo dubashi daga india, a parlour suka taru tun shigowar Baby bata kalli gun da Bilal ke zaune ba sai dai shi ya zuba mata ido cikin tsananin k’aunarta da tausayin kanshi akan tamai nisa,
Dad bayan yai sallama tare da bud’e taron da salatin Annabi ya fara”wannan taron na tarashi ne akan mutun biyu wato Bilal da khausar, kamar yanda dikkan ninku kuka sani na d’aura auran Bilal da Baby tun sati uku da suka wuce dik da Bilal bai San da batunba to yanzu na sanar dakai kamar yanda abokinka kamal ya sanar dani musanbin ciwonka Wanda ka kasa fad’a min to na samo labarin kuma na kawo ma magani da ikon Allah domin na d’aura auranka da Baby kuma ina fatan bazaka watsan k’asa a ido ba kuma ba yanzu zaku tare ba har saina gama yi muku shirin gun zama sosai, ko Kuma ina ganin ma had’a bikin za’ai Dana su Islam, domin gashi Alhj Turaki yazo min da maganar yayan Aisha yaga Islam yana Neman auranta, don haka mun bashi Kuma zamu sa lokacin auran nan kusa insha Allah, inda me magana ina sauraransa!”

Tsit parlour Yayi ba abinda kake ji sai sauke ajiyar zuciyar Bilal ya rasa gane wane hali yake ciki sabida tsananin farin ciki da murna don haka ajiyar zuciya kawai yakeyi idonshi a rufe ya jingina jikin kujera,ita kuwa Baby ji take kamar ta mutu zuciyanta sai zafi take badan tana gudun karta tozarta iyayenta ba data fashe da kuka ko taji sauk’i aranta, ita kuwa Islam murna da kunya ne suka hanata motsawa sabida zata kasance da burinta nan kusa, su kuwa manyan sunyi shiru ne don su bawa yaran damar magantuwa amma ganin sunyi shiru yasa Alh Bello magana” To hak’ik’a babu abinda zamuce sai godiya ga Allah da hukuncin daya yanke garemu na canja lamarinsa a yanda yaso kuma mun karb’a munsan shine dai dai, sannan khausar ina me Jan hankalinki ga biyayyar aure ki zama Mace ta gari ga mijinta, kaima Bilal ka rik’e matarka bisa amana da hak’urin zama da ita amatsayin ta na mace me rauni, sannan Alh Turaki mun bawa Nazeef auran Islam dikda kasancewarmu dangin uwa gareta to mun amsa maka ne bisa dama da dangin mahaifinta suka bamu, a k’arshe ina k’ara Godiya ga Allah”

Abban Aisha ne ya d'ora"To mun gode da karamcinku garemu muna fatan Allah yasanya Alkairai cikin wannan aure ya tsone idon mak'iya kuma muna k'ara addu'a ga marigayi Nabeel Allah ya jaddada rahma gareshi "

Dikkansu amsawa sukai da Ameen, sannan Dad ya kuma gyara zama yace “Alh Turaki muna ganin batun lokaci ya kuke ganin za’a tsaida tunda dai ba wani Abu ake jira ba Abu dik gida ne”
“Eh to Alhj A. A ina ganin mu tsaida wata biyu domin su Bilal kaga tunda su da d’aurin auransu bai kamata muja abinba”
“Eh hakan Yayi ko Alh Bello?”
“Eh madallah Allah yasa muna raye”
“Ameen Ameen, to Ku Baku da magana?” Dad ya fad’a yana kallonsu mami da momi dika fatan alkairi kawai sukai nan akai addu’a aka shafa kowa ya tashi, saida kowa ya fita Dad yaiwa su Alh Turaki da Alh Bello rakiya suka hau motocinsu sannan ya dawo nan ya sami kamal yasa Bilal agaba yanata rarrashinsa sabida kukan da yake, da sauri Dad ya k’arasa yana tanbayar lafiya Kuma yake kuka? Nan kamal yake shaida mai kukan dad’i yakeyi wai ya rasa bakin godiya shine yasa kuka, mirmishi Dad yai sannan ya d’an buga Bayan Bilal d’in yana fad’in” be a man Bilal karka zama ragon maza me kuka kan mace zata rainaka fa”
Kallon kamal yai yace”kamal kuje d’akinsa ka rarrasheshi tunda shi abin kuka yanzu baimai kad’an”
Ya fad’a da sigar tsokana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button