BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate, motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍

        1⃣ 0⃣2⃣

Doctor Al’ameen najin labarin ansa ranar auran Nazeef da Islam za’a had’a da khausar yace “ina bai yuyu aiwa su Islam aure abarsu ba don haka nan da nan ya tashi y’an gidansu sukazo gidansu Aisha akai maganar aure nan dai aka k’ayyade za’a had’a danasu nazeef tunda dai ya motso shima.

Dik labari ya baza skul d’insu ai Auransu Aisha ya taso nan da wata biyu zata auri lecturer d’insu Doctor Al’ameen Islam kuma yayan Aishan zata aura ga Baby ma an had’ata da broth d’inta, wasu gulmar da suke yanzu dik irin son da ake fad’in Baby nayiwa Nabeel amma bayan rasuwarsa da wata bakwai zata k’ara wani auran ai sun d’auka saiya shekara biyar zata kuma sauraran wani namijn sabida rashin amana, To Wanda yasan yanda abubuwan suka wakana ne yake k’ara tausayawa Baby.

A gida kuwa Sam Baby bata had’a hanya da Bilal bata yarda wani Abu ya had’asu koda maganar fatar baki ce don data dawo daga skul take shigewa d’aki ta rufe koda ya shigo parlour sai dai suyi hiransu da Islam ya fita, sabida shi kuwa ma ta kashe wayoyinta ta ajiye kuma ko ta Islam ya kira yace ta had’wsu takan cewa kice nai bacci ko tace tana gun Mami,
Kowa na kula da halin ko in kula da Baby ke nunawa Bilal amma ba halin magana sabida kana mata magana zata fara kuka don haka kowa ya zuba mata ido, sai dai shi aita nuna masa hak’uri da juriya wata rana sai labari,don haka shima yaja jikinsa gefe ya daina Zak’e mata,
Wani fili ne da Dad ya siya tangameme a unguwar kuntau yace zai ginawa su Baby da Bilal gini aka d’auka na ban mamaki da birgewa kuma aiki aka fara da gaggawa amma da inganci don company aka bawa kwangilar ginin filin ba wasa suka zuba ma’aikata,
Dikkan b’angarorin shiri suke sosai, Aisha da Islam sun dage da shiri amma ita kam Baby tana gefe ta zuba ido don ita yanzu ba wani Abu da yake burgeta a duniya komai lami take jinsa,

Lokaci na tahowa hidima na k’ara yawa lefe Dad ya shiryawa Baby bana wasa ba don yaci alwashin komai shi zaiyi baya buk’atar k’wandalar kowa, b’angaran Kayan d’aki ma Dana kitchen komai iri d’aya akaiwa Baby da Islam kama daga furniture’s Kujeru labulaye rug’s rugs Kayan kallo kai komai dai iri d’aya dai dai da cokali baa ban bantasu ba, dangin baban Islam sun aiko da miliyan guda ai mata Kayan d’aki Dana kitchen Dad yace bazai amsa ba sabida shi ya dace yaiwa Islam komai na rayuwa, da suka takura masa cayaiwa mami” ki sa mata a account d’inta wata rana zasuyi muku anfani Donni yanzu inna amsa in kaisu ina na gama mata komai don haka asa mata a account nata zai mata anfani,

    Wannan karon ma mami y'ar Sudan ta d'auko don yiwa amaren  gyaran jiki da tsima su Sosai ake gyara su dik da yawanci  in aka bawa Baby Kayan tsimin takance bazata sha ba don  babu anfanin da zai mata Wanda tasha ma tana so baiyi anfani ba balle wannan, haka ake hak'uri a k'yaleta don amaryar sai da lallab'e.

 To su Islam basu shirya wani events da yawa ba don basa samun had'in kan Baby dik abinda sukace mata sai tace kuyi dik abinda zakuyi amma nikam bani aciki,to dik sanda tai musu haka sai dai suyi tsit don haka ma suka hak'ura da komai  daga kamu sai  dinner, zasuyi dik awaje  guda suka shirya yi harda angwayen.

Anyi kamu Iya mata,washe gari dinner tunda aka fara shirin tafiya Baby bata tashi tayi ba kowa na shiryawa har Islam tayi wanka me kwalliya nata shiryata sunyi sunyi Baby tak’i tashi don haka aka kira Mami tana zuwa ta kama hannunta ta tafi da ita d’akinta nasiha ta shiga yi mata”Baby kiyi hak’uri ki rufamana asiri karki nunawa duniya baki son auran nan za’a zagemu musamman ni za’ace ni ke saki komai, Baby ki yarda da k’addararki ki d’auka ahaka Allah ya tsara rayuwarki kiyi hak’uri kinji Baby”.

Kwanciya tai jikin mami tana kuka tace "mami  shike nan ya tabbata yaya Nabeel yabar rayuwata shike nan ni d'in matar broth ce, mami ya zanyi? Wayyo Allah yaya Nabeel ka tafi ka barni cikin wani hali ,Allah ina rok'onka daka gafartawa farin cikin rayuwata Allah kasa yana cikin rahmarka"

    Shafa kanta mami kawai take hartai shiru daga nan ta had'a mata ruwan wanka ta kamata har toilet d'in ta barta,bayan ta fito mami tacewa me kwalliyar tazo d'akinta ta shiryata,anan akai mata komai tayi kyau har ba'a magana, amma fa fuskan nan ba rahma ko d'aya tai kirtata da ita.

    Tunda sikaje gun dinner d'in bata kalli inda Bilal ke zaune ba,abinda zai baka tausayi ko wane ango yana rik'e da hannun amaryara suna hiransu cikin k'auna da kulawa, amma ga Bilal ba haka abin yake ba don dik jikinsa amace yake ganin yanda Baby ta had'e giran sama da k'asa don haka shima yaja bakinsa ya kulle.

 Nan aka umarci angwaye da amare su fito tsakiyan fili, tunda suka fito jikin Baby ke rawa anata musu lik'i kanta ak'asa ta kasa kallon kowa, jin anata mata ruwan kud'i y'an dubu dubu ank'i a tsaya yasa ta d'ago idonta ahankali taga waye ummmy mahaifiyar Nabeel ta gani tanata mirmishi tana mata lik'in,bata San sanda  hawaye ya Kunce a idonta ba sharrrr yake zuba afuskanta ganin haka da sauri ummmy tabar filin don itama ziciyanta ta karye,

Ahaka akai dinner d’innan dik Rabin jama’ar jikinsu ya mutu da gannin halin da Baby n ke ciki,haka dai aka tashi ba dad’i.

Dik bikin haka aka gamashi agidansu Baby ba wani nishad’i sosai.

Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(We are here to educate,motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍

         1⃣0⃣4⃣

Yanda yaga rana haka yaga dare, ya tashi yanata salloli yana rok’on ubangiji ya dafa masa a rayuwarsa ya sa sonsa a zuciyan Baby koda k’ank’ani ne yasa auransu ya zama alkairi, bayan k’afafunsa sun Gaza ya zauna ya d’auki sha kumdum yana karantawa har aka fara kiraye kirayen sallah,alwala ya k’ara d’aurawa yai raka’a’tanil fajir sannan ya fita yaje masallacin dake bayan gidan nasu, a masallacinma ya dad’e bai dawo ba yana ta zikri da tasbihi da Neman dacewa gun ubangiji,har saida yaga haske ya farayi sannan ya taho gida idonsa cike da bacci dik yai mai nauyi, kai tsaye kitchen ya Shiga yaga ma’aikan da aka kawo musu sun duk’ufa aikin girki , d’aya bayerabiya ce baza ta wuce shekara 25 ba, d’ayar kuma bahaushiya ce ita Zata kai shekara talatin, sai Yar k’aramar Yarinya me wanke wanke bazata wuce 15 ba, bangaran maza Kuma su uku ne me gadi da me kula da shukoki da share dik filin gidan sai Kuma me wanki da guga,
Gyaran murya yai dik suka jiyo da sauri suka rank’afa suna gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska yana ranbayarsu ya aikin suka amsa da Alhamdulill yace”Ku kula don Allah kuyi aiki da tsafta Kuma da gaskiya don ban San k’azanta ko kad’an wlh,ina fatan kun fahimta?”

“Eh mun fahimta Alhaji insha Allah zamu kula da kyau”
Gyad’a kai yai cikin gamsuwa ya juya ciki.

Kai tsaye d’akinsa ya nufa yai wanka sannan yasa kayansa marasa nauiyi ya fito parlourn ganin dining d’in yai tsaf an shirya Kayan abincin zuwa yai Ya bubbud’e
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

        NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate ,motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍

            1⃣0⃣5⃣

Haka rayuwan su take gudana inba shi ya shiga sabgarta bata ko kallonshi shi ko bai gazawa koda yaushe cikin hidima da ita yake yana mata dikkan abinda take so har yau da sika kai sati biyu cif agidn kuma washe gari ne zasu koma makaranta dama hutun sati uku suka samu sunci d’aya agida kafin bikinsu don haka dik tai shirye shiryenta na komawa skul, tana zaune ta kira mami don haryanzu bata zoba kullum sai tace gata nan amma taji shiru, tana d’agawa tace”darun mami ya akayi ?’
Cikin shagwab’anta tace “mami gashi har zamu koma skul biki zoba kuma bayan kinyimin alk’awari”
“Baby karki damu zanzo bani da lokaci ne kullum inada aiki sosai a asibita amma insha Allah ina nan zuwa very soon”
“To mami ina jiranki”
Sukai sallama

Da dare tana kwance akan 3 seater tana kallon wata tasha an hasko shahararran malaminnan Dct.Isah Ali Ibrahim fantami yana lector akan biyayya a aure da azabar da Allah ya tanadarwa macen da take k’untata zuciyar mijinta tare da nuna ita take sama dashi,yanda yake maganar yana kausasa harshe yasa dik jikinta yai sanyi gumi ya fara keto mata ta fara tunanin yanzufa shariyar da takewa Bilal itama acikin lefi take Kenan nan da nan wata nadama ta kamata dadin dad’awa data tina irin kulawar da Bilal yake bata yake k’arar da lokacinsa akanta tab’ d’in gaskiya ya kamata ta gyara rayuwarta tasan me takeyi to in banda ma abinta meye lefin Bilal cikin lamarin auran nan tunda shima bai San an d’aura ba tama rigashi samun labari, Kai gaskiya ya kamata hankalina ya dawo jikina tunda dai bashi ya kashe min Nabeel d’ina ba ma k’addarata ce tazo min ahaka to ya zanyi. Dik cikin ranta take wannan tunanin, jin ana knocking yasa ta m’ik’e taje ta bud’e shine tsaye da k’atuwar Leda ta matsa ya wuce sannan ta maida k’ofan ta rufe, “sannu da zuwa “ta fad’a ahankali, cikin mamaki ya kalleta don bata tab’a mai magana in bashi ya fara mata ba amma sai ya basar ya amsa cikin kulawa”yawwa sannu Baby ya zaman kad’aita? Ko dake gobe ai za’a koma skul zaki rage zaman shiru d’in ko?”
D’an mirmishi tai kawai taje ga t.v ta kashe yace “ya kika kashe ba lecture kike jiba?”
“Um um na gama ji”
“Hhhhhmmm ba wani kin gama kawai dai bakya son inji me yake cewa kila akanmu yake Baku wani sirrin”
D’an zaro ido tai tace”kai ni dai banji hakanba “
“Hhhhmmmm “
Kawai yace ya wuce d’akinsa, zama tai kan kujera tana mamakin ya akai yasan me akeyi a wannan tashar? To koma mene oho”
Bayan yai wanka ya d’aura alwala yazo yai sallar isha’i sannan ya fito dining don cin abinci. Ganinta yai kwance tanata biga game a wayanta abin ya d’aure mai kai don bata tab’a zama a parlour matuk’ar yana gida to yau meke faruwa kodai Allah ya amshi addu’arsa ne ta fara sanyi .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button