BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ya k’araso ya zauna kusa da ita yaga har ya zauna bata d’ago ba hankalinta naga wayan,hannunsa yakai a hankali ya janye wayan d’agowa tai cikin d’okin ta kusa cinyewa tace”haba mana broth don Allah karsu kamani nafa kusa cinyewa don Allah ka bani”
Mik’ewa yai rik’e da wayan itama ta mik’e ya d’aga wayan sama yana dariya, tsalle tai ta kamo hannunsa tana so ta amshi wayan amma yak’i bari ta turo baki cikin kukan shagwab’a tace”Allah in aka kamani saika biyani Allah banso ka bani” dariya kawai yake yanda yaga tana buga tsalle tana son kamashi ta kasa, :d’in d’in d’iri d’in: sukaji alamar an kamata ai kuwa ya zaro ido da sauri cikin alamar jin tsoro yace” wayyo an kamaki ya zanyi?”
Murtuke fuska tai ta juya baya tare da rik’e k’ugu tana jijjiga kai alamar bazata yarda ba, k’unshe dariyarsa yai ya zagayo gabanta ya tsugunna tare da kama kunne yace”Amin afuwa ya’r k’anwata bazan k’ara ba kinji “
Rufe idonta tai tana cije lebe alamar bazata yarda ba, ya mik’e tsaye ya ruk’o hannunta tare da tausasa murya yace” Shike nan zan rama miki ai nima na Iya game d’in amma bari inci abincin zan biyaki “Tafiya yai hanyar dining d’in ya zauna yana bud’e food flask d’in tuwon shinkafa ne da miyar taushe d’ayan kuma farfesun Kayan cikin rago ne, ya gyad’a kai yana shak’ar k’amshin abincin , dawo wa yai ya kamo hannunta yace “zomu ci abincin don naga alamar ba’a tab’a komai ciki ba”
Ba musu ta bishi suka zauna ya had’a musu abincin a flat d’aya yace”maza muci da sauri in biyaki abinki”. Bata damu ba tasa spoon ta fara ci baka jin komai sai k’arar cokulansu har sika kammala ta mik’e tare da cewa” to zoka rama min abuna”
Shima mik’ewa yai ya dawo kan seater ya zauna tare da bud’e game d’in ya fara, zama tai kusa dashi tare da k’wak’ubarsa tana leka screen d’in tana ganin yanda yake ziba gudu cikin game d’in kamar me , dik abinda yake dauriya kawai yake don yanda ta k’wak’wubeshi dik tsikan jikinsa tashi take, yana daurewa ne kawai, ahaka yaita yi mata har inda ta tsaya ya mik’a mata yana mirmishi yace” to gashi na biya bashi saura me kuma?”
Stop tasa a game d’in sannan ta kalleshi da Yar dariya tace “tunda ka biya ka fita bari inje in kwanta saida safe”
Juya wa tai zuwa d’aki ya bita da kallo cikin ransa yake tunanin abubuwa da yawa yai d’an mirmishi ya wuce nashi d’akin bayan ya kulle kofa ya kashe Kayan wuta.
Taku ce
Layuza kabir Adam????
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate,motivate and entertain our reader’s)
????????????????????????????????????✍
1⃣0⃣7⃣
Da dare ta shirya tsaf cikin riga da zani na atanfa Holland green tayi kyau sosai tasa farin mayafi da takalmi da jaka, fitowa tai parlour tana jiranshi kusan 10 minutes duk ta gaji da jira don haka ta tashi ta nufi d’akinsa zumud’in da take ciki na zuwa gida shiya mantar da ita yin knocking kai tsaye tasa kai tana shiga ta sameshi tsaye gaban mirrow d’aure da d’an k’aramin towel yana taje kansa ya juyo yana kallonta da sauri ta juya tana fad’in ” I’m sorry broth”ta fice da gudu, dariya kawai yai yana jijjiga kai don ya fahimci yau cikin nishad’i take.
Shiryawa yai cikin farar shadda hap yasa hula da takalmi bak’ak’e yai kyau matuk’a,
Fitowa yai rik’e da kye d’in mota kallo d’aya tai mishi ta gano tsabar kyan da yai aranta tace”kai gaskiya ba yabon kaiba zuri’armu na da kyau” amma a zahiri saita kauda kai gefe kamar bata ga fitowarsa ba, rank’wafowa yai saitin fuskarta yana fad’in” Amin afuwa na b’ata miki lokaci ko tashi mu wuce”
Bata tanka mai ba ta mik’e suka fita.
Suna tafe yana d’an janta da hira in taso ta amsa in bata soba tai shiru ahaka suka k’araso gidan tun kafin ya gama parking ta fito da gudun gaske tai part d’insu”mami mami nah kina ina?”
Zaune ta tadda mamin a parlour tana karanta jarida ta fad’a jikinta da tsananin murna ta ruk’unk’umeta,Mami ma cikin farin ciki ta k’ara sata ajikinta tana fad’in”Oyo yo my daughter daga ina haka”
“Mami daga gida muke, wayyo mami nah nayi kewanki wlh sosai”
Ya’r dariya mami tai Wanda dai dai nan Bilal ya k’araro mami tace”Bilal sannunku da zuwa yau kam ka fanshemu k”orafi ya k’are yau ga Baby a gida”
Dariya yai ya tsugunna suka gaisa cikin girmamawa, “Baby yanzu wannan rik’on da kika min kamar wadda Zan gudu in barki”
“Mami fa nayi kewanki ne ni dikma tausayinki nakeji dik gun shiru sai ke kad’ai” ta fad’a idonta na kawo k’walla, dariya mami tai tace”to mene ne Baby Ai alheri ne ya rabamu ni harma na saba da zaman ni kad”ai ,ina nan dai ina jiran jikoki sai su maida gurbinku”
Kauda kai Baby tai tana cewa “haba mami nidai bandani yarinya ce”
Dariya sukaita mata,mami tace “to Ku tashi ku shiga wajan momy”.
Da sika je part d’in mami bata nan tana gun Dad kasancewar itace da girki nan ma suna sallama tai tsalle jikin Dad tanata ihun murna ,Dariya Dad yai yace”Kai Baby sai yaushe zaki girma ne wannan tsalle ajikina ai saiki karyani da nauyi”
Kukan shagwab’a ta fara tana buga k’afa”Nidai Allah Dad ni yarinya ce ba wani girma da zan k’ara” momy ce ta amshe”Ai kuwa da gaskiyarki Baby ba wani girma da kikai “
Dariya duka suka sa mata ta zame k’asa ta gaida Dad da momyn cikin girmamawa.
Abincin da aka zubawa Dad yace”kuzo to muci abincin” bayan sun gama ci suka shiga hira Dad yanata k’ara nuna musu mahimmancin zumunci da k’aunar juna.
Mik’ewa Baby tai tace”bari inje gun mami”.
Hira suke sosai da mami tana dariya, yau jinta take asama kamar karta bar gidan,cikin dabara mami take k'ara nuna mata dabarun zama da miji dik da ita Baby ba shigarta wannan yake ba, k'asa tai da murya cikin kalan tausayi tace"mami don Allah ki taimaka ki tanbayarmin Dad ya bani wannan albums da flat d'in nawa wlh mami wani Abu nake son dubawa aciki"
“A gaskiya Baby bazan Iya tunkarar Dad d’inku da wannan maganarba sabida zaima Iya zatan koni nake son ya baki kuma ma baby wannan albums d’in ba abinda zaiyi sai tayar da Hankalinki tunda dai Allah yasa zuciyarki ta fara sanyi kiyi hak’uri kawai”.
Kuka takewa mami kamar me tana mata magiya akan ta anso mata,”Baby wai biki San aure kike ba biki san kai wani abu na Nabeel gidan Bilal zunubi zaki d’ibarwa kanki ba”
“Mami in har auran Bilal yana nufin rabani da dik wani abu na Yaya Nabeel to hak’ik’a bazan tab’a daina danasanin wannan auranba wlh”
Toshe kunne Bilal yai cikin tsananin bacin rai don tun da suka fara maganar yake tsaye akansu basu Sani ba, sad’af sad’af ya juya ya fice ransa cike da k’unci, dole ya dai daita nutsuwarsa ya koma part d’in Dad, zuwa yai ya tsugunna gabansa cikin k’ask’antar da kai”Dad nazo gunka ina neman wata alfarma Dad ka taimaki rayuwarmu ka anshi rokona, Dad karka juyawa buk’atata baya don Allah Dad na Sani tun k’uriciyarmu kake Neman dikkan abinda zai faranta ranmu har zuwa girmanmu Dad ka tai makemu”
Cikin damuwa Dad yace”Bilal meke faruwa ne me kake so da kake gudun fad’amin haka, ka kwantar da hankalinka ka fad’amin abinda kake so insha Allah in baifi k’arfina ba zan maka,Bilal ina sauraranka”
“Dad don Allah daman so nake ka bamu wannan albums d’in na gun Baby daka k’wace”
Cikin mamaki Dad ya kalleshi yace”Bilal kanka d’aya kuwa meke damunka ne shin kasan meye a cikin albums d’in?”
“Eh DAd na Sani photunan bikinsu da marigayi Nabeel ne”
Numfashi Dad ya ja ciin bacin rai yace”Bilal ka san me kake Kuwa shin kai d’in so kake zama mijin tace ,shin baka da kishin auranka?ka zama lusari dik abinda Mace ke so shi kake so ko? Sabida tana tsoron tanbaya ta shine kai ta turoka ka amsar mata to bazaka tab’a samun kwanciyar hankali ba matuk’ar albums d’innan yaje gidanka, To ahir ina jan kunnanka da karka sake soyayya ta rufe idonka ka zama soko cikin gidanka”.
Saida Dad ya kai k’arshe da fad’ansa sannan Bilal ya k’ara duk’ar da kai yace”Dad dik abinda kake tunani ba haka bane wlh Dad Baby ma bata San zan tanbayeka ba bata ma taba min wannan maganarba,yanzu ne na sameta tanata yiwa mami kuka akan ta k’arb’ar mata agunka tace bazata iya ba Dad shine nake Neman alfarma agunka ka taimake mu ka bamu”.
Mirmishi Dad yai yace”hhhhhhmmmm Bilal baka San mata ba amma zan baka sai dai bana fatan wani abu ya biyo baya”
D’akinsa ya shiga ya d’auko manya manyan albums d’in guda uku da kuma flat na videon bikin ya mik’a mai cikin tsananin murna Ya karb’a yana godiya ya fice, motansa yaje ya bud’e baya ya saka sannan ya koma part d’in mami ya sameta tana ta share hawaye yi yai kamar bai gani ba yacewa Mami”zamu tafi mami dare yayi”
“To Bilal zaku wuce Allah ya kiyaye yai muku albarka ya kareku sharrin mak’iya”
Shi kad’i yake amsawa , mami ta mik’e don yi musu rakiya, palourn Dad sukaje sukai mai sallama shi ma ya biyosu shida momy zuwa parking space har sun shiga mota Dad ya kalli Baby yace”Baby ya dai naga idonki kamar kinyi kuka!”
Karaf kafin tai magana mami tace”wai bata son tafiya ne shine take kuka”
Momy ce tace “To ai dole tai kuka daga zuwa sai tafiya kai Bilal in zaku k’ara zuwa kuzo tun safe kabarta ta huta zuwa dare saiku tafi”
“To momy zamu dawo kwana kusa insha Allah”
Ahaka dai suka bar gidan tanata matsar ido, sunyi nisa ya d’an rage gudu ya juyo yana kallanta tsawon lokaci sannan yace”My sis wai wannan hawayen name nene? Ya dace ace kin bashshi haka, wlh Baby badan fad’an da Dad zaiyi ba kullum da sai na kawoki gida kin yini har ke da kanki sai kince kin gaji da zuwa”,share hawaye tai tace”nifa ba kukan gida nake ba”
“To kukan me kike?”
“Ba komai”
Shiru yai bai k”ara magana ba har sukaje gida.