BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna shiga parlour ya rik'o hannunta tazo jikinsa sosai yace"Baby tun muna k'ana na idona da zuciyata basa son ganin b'acin ranki har izuwa yanzu, Baby nasan meye damuwarki kuma nayi dik yanda zanyi don kawar miki da ita,zoki rakani". Hannunta yaja suka koma parking space ya bud'e motan ya d'auko albums d'in baice mata komai ba har suka koma parlourn, sai da ya kai ta har d'akinta sannan ya ajiye albums d'in a kusa da ita yace"Baby gashi indai rashin wannan ke saki kuka bana fatan k'ara ganin kukanki".
Yana ajiyewa ya juya ya fice.
Taku ce
Layuza kabir Adam????♀
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate,motivate and entertain our readers)
HAPPY NEW YEAR
ALLAH YASA MUN SHIGEKI ASA’A ALKAIRAN DAKE CIKIN 2018 ALLAH KA HAD’AMU DASHI SHARRIN CIKINTA KA KAREMU.????
1⃣0⃣8⃣
Bin bayanshi tai da kallo cikin tsananin mamaki da irin k’arfin halinsa wato dik abinda take so Bilal naso kenan? Kai amma taji dad’in wannan abin da yai mata ko ina ya samo oho to ko agidansu Nabeel ya amso tunda bayan gidansu gidansu Nabeel kad’ai ke da wannan albums d’in, to ko a d’akin Dad yaje ya d’auko be Sani ba? To waima abin tanbayar a ina yasan tana buk’atar Albums d’in har tana kuka akansu?to Allah shi yabarwa kansa sani koma dai ya akai ya samo mata yayi me wuyar sai dai tace ta gode mishi sosai da sosai kuwa don yau ya mata abinda bai tab’a mata makamancinsa ba har taji dikkan wani haushinsa da takeji ta daina, har taji wani girmansa ya sauka a zuciyarta tunda har ya iya had’ata da abinda ya danganci Nabeel alamun yana son Nabeel kenan,in kuwa haka ne ya wanke kansa tas agunta wlh. barin tunanin tai ta d’auki flat guda d’aya ta nufi t,v d’in d’akin nata, tasa amma fafur yak’i tafiya tai tai ta k’iyi kawai saita dawo babban parlour tasa ai kuwa nan da nan ya fara zama tai dirshen tana kallon yanda aketa nuno jama’a wajan dinner d’insu kafin daga bisani aka hasko fuskokinsu ita da Nabeel suna sakarwa juna mirmishi Wanda da gani kaga cikakkun masoya, kamar abin arzik’i taketa daurewa kafin daga bisani ta fashe da wani irin kuka data tuna har abada shi da ita sai dai gani a photo ko video irin haka, kuka take me karamin sauti amma me ratsa zuciya don jikinta har rawa yake kamar me.
yana zaune bakin gado ya dafe kansa hannu biyu biyu idonsa yai jajir dik jijiyoyin kansa sun tashi don tsananin b'acin ran kishi, lalle shirme kawai yakeyi dik kulawar da yake bawa Baby abanza har yanzu zuciyarta naga Nabeel, yana cikin wannan halin yajiyi kamar shishik'ar kuka ya kasa kunne sosai yaji hakanne, Mikewa yai yayo parlourn yana fitowa yaga yanda take zaune ta hade jikinta waje d'aya sai juya kai take tana kuka ,tsayawa yai akanta tsawon lokoci bata Sani ba don haka ya juya ya koma d'akinsa ko gani bai yayi sosai sai huci yake yana kyarma tofa kishi ya tayarwa y'an maza ba magana, fad'awa yai kan gadonsa kansa na sarawa da wani matsanancin ciwo kafin meye jikinsa ya d'au zafi nan da nan zazzab'i ya rufeshi jikinsa kamar wuta, zuciyarsa sai zafi take kamar ta faso k'irjin ta fito.
Ita kuwa Baby sai da tai kukanta kamar ba gobe ta k’oshi anan barci ya d’auketa ta b’ingire , kaset dai ya k’are t.v ta gaji taita shuuuu shuuuu ita kad’ai.
A d’aki Bilal ciwo gaba yaketa yi har ya fita hayyacinsa , a wannan halin ya kwanan kafin meye kuwa yayi muzu muzu dashi.
Kiran sallar asuba ne ya farkar da Baby ta farka idonta dik yai mata nauyi ya kunbura da k’ar ta lallab’a ta tashi ta kashe t.v da taketa aiki.ta wuce d’akinta tai alwala tai sallar asuba ta dad’e zaune tana adduo’i ga Nabeel sashin ranta, jin da tai har kunsan shida amma har lokacin ba mothin Bilal ba dalilinsa, atranta tace” nayi alk’awin canja zamana dashii tun daga yau kuma yanzu ya kamata ta fara. Tashi tai ta nufi d’akin nasa tai sa’a kuwa a bud’e yeke ta shiga parlourn ta ga dik glof d’in a kunne har tayi tunanin ko ya tashi ne bari ta koma sai kuma wata zuciyar tace ta dai shiga cikin d’akin don haka ta shige tana bud’e k’ofan ta hangoshi kan gado ya rufe rabin jikinsa da bargo sai rawan sanyi yake idonshi a rufe da gani kasan yana cin uwar wuya, da sauri ta k’arasa kan gadon tana fad’in “broth lfy meke damunka?daman baka da lfy baka fad’aminba” dik ta gigice hawa gadon tai ta d’ago kansa ta d’ora kan cinyarta tana jijjigashi tama rasa wane taimaka zata fara bashi, da sauri ta d’auko wayarshi dake gefan gado ta lalubo number family doctor d’insu, yana d’auka ta Fara fad’in”doctor ka taimaka min kazo gidanmu broth bashi da lfy yana buk’atar taimako”
Shima cikin kid’ima yace”khausar kuna ina gidanku ko gidan Dad d’inku?”
“Doctor gidanmu can kuntau fa”
“Ok gani nan yanzu insha Allah”
Tana ajiye wayar tashiga shafa kansa tana mai sannu tama rasa abin yi, ahaka Doctor ya kirata yace”gani nazo “
Fita tai ta shigo dashi cikin d’akin, yana zuwa ya bud’e jakarsa ya d’auko kayan aiki ya fara chakking d’insa allura yai mai sannan ya sa masa drip me d’auke da magunguna, bayan ya gama dik abinda ya dace ya juyo ya kalli Baby yace “muje parlour ina son magana dake”
Hannu Bilal ya fara d’agawa cikin mayen baccin da ya fara d’ibansa yana wa doctor alamar yana son magana dashi,motsowa yai sosai kusa da gadon ya matso da kunnansa ga bakin Bilal d’in “Doctor don Allah karka fad’awa Dad banda lafiya kacewa Baby ma karta fad’a mai” jinjina kai kawai yai ya d’auki akwatin kayan aikinsa ya fice Baby tabi bayansa .
Kujera ya samu ya zauna sannan ya fuskaci Baby ya fara”khausar meya faru da mijinki daga jiya zuwa yau?”
D’an zaro ido tai tace” wlh doctor ban San meya sameshi ba tunda dai muka dawo daga gida ya shiga d’aki bai k’ara fitowa ba to sai bayan danai sallar asuba naga har k’arfe shida bai fito zuwa masallaci ba shine na shiga inga lafiya to shine ina zuwa na sameshi ahaka”,
D’an kad’a kai yai sannan yace”ko a gida ko bayan dawowarku ba wani abu daya b’ata masa rai ko ke kiyi tunani bikiyi mai wani abu ba da zai d’aga hankalinsa koya b’ata ransa?”
Jim tai sannan tace” doctor nidai har yabar d’akina babu wani abu na b’acin rai da nagani tare dashi”
Jan numfashi yai yace”To shike nan amma fa yanda na auna zuciyarsa abinda ta nuna ta shiga cikin matsanancin b’acin raine Wanda ciwon da muke fatan ya bar zuciyar gaba d’aya ya dawo mai lokaci guda, don haka Baby ya zama dole matuk’ar ana son rayuwar Bilal arink’a kiyaye dik abinda zai tab’a ransa don in har yana ci gaba da fuskantar irin wannan b’acin ran akoda yaushe wata rana za’a wayi gari aga zuciyar ta fashe don haka ki kula da dik abinda zai jawo mai b’acin rai, sannan yace karki fad’awa Dad d’inku baida lfy nima yaja kunne na akan haka.
Jikinta amace lib’is tace “to doctor na gode sosai Allah yasaka da alkairi”
Sallama yai mata kan sai da yamma zai dawo ya duba jikin.
D’akin ta dawo ta zauna taga har yai bacci ta kalli ago go taga bakwai da rabi harta gota ta mik’e ta gyara mai rufar bargon sannan ta fice ta koma d’akinta, hawa gado tai ta d’an kwanta dik jikinta amace tana jin ranta ba dad’i da yanayin da Bilal ke ciki da wannan tunanin bacci ya d’auketa.
Misalin Tara ta farka da sauri ta diro akan gadon ganin irin dogon baccin da tayi toilet ta fad’a tai wanka cikin sauri sauri ta sa kaya wando ne three quarter da Riga half kasancewar zafin da ake yasa ta yin shiga me sauk’i haka wayanta ta d’auko taga tarin miss call d’in Aisha da Islam kusan guda sha biyar ga Test suna tanbayarta lafiya bata shigo skul ba kuma tasan lecture d’insu na 8ne,
Number Aisha ta kira tana d’auka tace”sis lafiya kuwa?”
“Wlh naga miss calls d’in Ku sis ina bacci ne abinda yasa ban shigo ba broth ne ba lafiya”
“Ayya meke damunsa?”
“Kawai dai fever ne amma in kin fad’awa isy kice karta fad’awa su Dad sabida yace baiso su Sani”
“Ok to kiyi mai sannu don Allah “
“Um hmm zaiji” sai anjima ta kashe wayan tana k’ok’arin Shiga d’akinnasa, yanda ta barshi haka yake bacci sosai yakeyi amma yanzu numfashinsa ya dai daita ba kamar d’azu ba ,fita tai zuwa dining don taji cikinta ba komai , ruwan tea tasha tare da d’an k’wai ta dawo zuwa d’akin ta zauna bakin gadon tana kallanshi dik da bacci yake hakan bai hana kyansa bayyana ba karo na biyu ta k’ara kallonsa tace cikin ranta”gaskiya broth ba k’aramin kama yake da Dad ba koni ban kama k’afar kamanninsa dashi ba”
Gani tai ya fara motwasa tai saurin rik’e hannunsa da akasa drip d’in don baifi rabi bane ya tafi kasancewar kad’an aka bud’eshi sabida bugun zuciya balle shi me cuwon zuciyar ma, ahankali ya bud’e ido ya kalleta tace”sannu ya jikin naka?”
Ahankali kan leb’ansa yace”da sauki”
Shiru ya biyo baya can yace”ina son fitsari ki ciremin drip d’innan”
Zare roban tai yaje yai ya dawo ta mayar masa nan baccin ya kuma d’aukansa, tana ta zaune tai tunanin bari taje kitchen tasa su shirya masa abincin marasa lafiya Wanda zai iya ci inya farka, ta kusa fita a d’akin wayansa tai k’ara ta dawo ta d’auka zaid taga ansa da har bazatai picking ba sai kuma ta d’aga”hello d’an uwa ya kake ya amarya?”
“Bashi bane”
“Wake magana to?”
“Khausar ce yana kwance bai jin dad’i”
“Occhhh Allah dai yasa ba ciwon bane”
“Eh zazzab’i ne”
“Ok inya tashi amai sannu zan k’ara kira”,amarya sai anjima”
Kashe wayan tai gaba d’aya don kar aita kira.