BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Bashi ya dawo hankalinsa ba sai cikin dare hakanma ji yake kamar maransa taza fashe don ciwo koya ya motsa sai yaji ajikinsa ahaka yana jikinta bacci ya d’aukesu.

Hhhhhmmmmm bacci yai dad’i harda makara dikkansu basuji sallar asuba ba sai k’arfe shida da mintina ta farka tajita k’am ajikinsa ahankali ta fara zame jikinta don tashi tai sallah , karaf shima ya farka ya kalli agogo da sauri ya cikata ya mik’e toilet ya fad’a don d’auro alwala, itama d’akinta ta koma tai alwala tai sallarta gado ta koma don da bacci a idonta sosai, shima a d’akinsa yana idar da sallah yai addu’o’insa Wanda ya fara tabbatar da sun fara karbuwa bayan ya shafa ya koma gadon cikin kuzari da nishad’i yanata tunanin yanda jiya ya mak’alk’ale jiki me laushi da kamshi, wani mirmishi ya saki daya tuna yanda ta rikice tunaninta dik ciwon ciki ne ” hhhmmmm wlh bazan k’arfafa jikina ba haka zanta shagwab’ewa ina jin dadi”.

Taku ce
Layuza kabir Adam ????‍♀
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

     NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate,motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍

         1⃣1⃣1⃣

Wata irin shakuwa ce ta shiga tsakaninsu me ban mamaki babban abu ad’aya dake damun zuciyar Bilal shine dik yanda yaso da making love Baby bata yarda ko romance sukeyi in taga yana shirin wuce gona da iri kuka take sawa shi kuma daga ta fara kuka sai ya barta ya koma gefe yaita jinyar kansa,
Kullum da ciwon Mara yake kwana sabida matsala da yake fuskanta amma hakan bayasa yai fishi kawai yana sawa aransa ne wata rana sai labari,

Yau jumma’a ta tashi da ciwon mararta don kusan wata biyu in zatai baya damunta da ciwo kamar da amma yau kam taji abin ba sauk’i tun tana daurewa har abin ya faskara gashi Bilal ya tafi office don itama basu da lecture yau shiyasa take gida, ciwo sosai takeyi tana juyi bisa gado ahaka kiran wayan Aisha ya shigo da k’yar ta mik’a hannu ta d’auki wayan”hello sis ya gida ya hutawa kira nai nai miki albishir Islam dai an samu sunje asibiti ance akwai baby na 6 weeks a cikinta amma wai tana jin kunya shiyasa tak’i fad’a yanzu ma yaya ne yake sanar dani” harta kai k’arshen zancanta bataji Baby ta tanka ba don haka ta kalli wayan taga tana kai kuwa”sis ko bakiji na ne?”
Salatin da taji tanayi ne yasa ta saurin fad’in”sis bakida lafiya meya faru subhanallah”
Cikin ciwo tace”sis ki taimakeni zan mutu”
“Ya Allah kinga bari nazo yanzu gani nan insha Allah amma kafin in k’araso bari in sanar da broth”.
Da sauri ta kira number d’in Doct.Ameen take sanar dashi zataje gidan Baby bata da lafiya,
“To Allah ya sauwak’e amma kiyi driving a nutse naji dik kin rikice”
Batace mai komai ba ta kashe wayan tasa hijab da tasauri ta d’auki key d’in motan ta fice, gudu take sosai harta kai gidan tanataiwa me gadi hone ya bud’e ad’ari ta shiga tai parking , tana shiga d’akin ta sameta harta suma a kid’ime ta d’auko ruwa ta watsa mata nan take tai ajiyan zuciya”Baby ciwon mara ne ko?”
Cikin wuya ta d’aga mata kai, shuru tai jimmm sannan taje ga F.A.B ta duba alluran da ake mata aikuwa ta samu d’aukowa tazo tai mata cikin ikon Allah ba’a 8 minutes ba ta fara jin yana d’an sassautawa, sai sannan Aisha ta d’aga waya ta kira Bilal kiran duniya tak’i shiga network na bada matsala Island ta Kira itama bata shiga ba sai yayanta ta kira tace”yaya Nazeef don Allah ka kira sis ka fad’a mata Baby ba lfy yanzu ma gani agidan nata”
“Meya samu babyn?”
“Ciwon ciki ne wlh don Allah Islam tazo yanzu kaji”
“Ok Allah ya bata lafiya zatazo yanzu”.

Islam a rikice ta shigo gidan dikda itama ba ishashshiyar lafiya gareta ba,
A zaune ta samu Aisha ta tusa Baby gaba ta rafka tagumi ita kuma tanata bacci don alluran data mata tana sata bacci,
“Sister ya jikin nata?”
” Da sauk’i gashi namata allura ma”
Zama tai tana ajiye mayafinta agefe tace”oh ni yaushe Baby zata rabu da wannan ciwon ance sai tayi aure toga auran anyi amma ba sauk’i”
Kallonta Aisha tai tace”sis muje parlour muyi maganar karmu tasheta”

Aisha ta nisa tace”sis kin San wani abu kuwa ina ganinfa da Baby tace miki har yanzu bata San dad’in abinda kike mak’alewa ba da gaske take na fuskanci da gaske har yanzu bata taba yarda da broth ba”
Jin jina kai tai*wlh nima na kula da haka kawai naga ita dashi suna bagararwa ne shiyasa nima ban matsanta da bincike ba”
“To yanzu meye mafita sis kingafa wannan abin bashi kad’ai zai cutar ba har da ita tunda gashi tana gani ciwon marar nan yak’i barinta”
“Sis inada wata dabara tunda kinga dik abinda zamu cewa Baby a banza zata d’aukeshi tunda ta karanta ta sani tasan illar da take must, mu dik abinda zamu fad’a mata ba yarda zatai kawai mu had’a Baki da family doctor d’inmu “

Shiru Aisha tai tana nazarin zancan Islam tace” To ya za’ayi me zamu had”a baki da doctor d’in”
Zama sukai suka tsara dik yanda zasuyi amma sai Baby ta warke zasu had’a plan d”in .

Saida tai baccin awa uku sannan ta farka tanata kuka don ji take bata tab”a ciwon da yakai wannan ba , sudai sannu kawai suke mata Islam ta had’o mata Lipton me zafi ba suga taita kurb’a ahaka cikin ya fara saki komai yana narkewa taimaka mata sukai taje toilet ta gyara kanta ta fito, sannu suketa mata ta dawo ta kwanta, har lokacin in sun kira wayan Bilal a kashe, sai la’asar ya dawo gidan rundaga ba k’ofa yake fad’in”bloody yau nai lefi na dad”e ko”
Shiru yai ganin Aisha ya fara mirmishi ” ah manyan bak’i ne damu yau haka?”
Itama fara’a tai tace”wlh kuwa broth sannu da zuwa”
Zai amsa Islam ta fito daga d’aki”broth ka dawo sannu da zuwa”
” au dikanku ne kenan akaimana ziyara sis ya jikin Baby tace min kwana biyu bakijin dad’i”
” eh wlh amma na warke itama Batada lafiya ne shine mukazo jinya”
D’an zaro ido yace”wace ba lafiya?”
“Baby mana tana cikin d’aki ai”
Bai tsaya jin k’arashen zancanba ya fad’a d’akin tana zaune a tsakiyan gadon ta cure k’afanta a cikinta da sauri ya haye gadon”ya subhanallah meya sameki bayan fitar nawa my blood?”
Fad’awa tai jikinsa tasa kuka tana nuna mai cikinta da hannu “cikinne yake ciwo toyi hak’uri daina kuka zai warke kinji insha Allah sannu” rarrashinta yake tayi yana share mata hawaye tunani yake wannan ciwon marar ai tunda tazo batayi ba sai yanzu ko tsallake yake mata?
Jinya dai dika ta koma hannun Bilal su Islam sukai musu sallama suka wuce gidajansu.

Bayan kwana biyar Baby ta gama period d’inta ta dawo normal, ranar da yamma ta dawo skul family Doctor d’insu yazo gidan bayan sun gaisa yake sanar da ita zuwa yai suyi magana me mahimmanci, waje ta samu ta zauna ta bashi dik hankalinta ya fara bayani “Baby magana ce babba nazo da ita akan mijinki tsawon lokacin da kukai aure Bilal ya tab’a fad’a miki cikinsa namai ciwo?”
“Eh doctor yana yawan yin ciwon ciki gaskiya “
“To khausar abinda ke faruwa shine ciwo yaiwa Bilal yawa a mararsa sakamakon sha’awa dake damunsa kullum kuma baya samun biyan buk’ata dalilin haka na dubashi na gono wata k’atuwar matsala wadda ta jawo sai anyi masa aiki an cire mai”
A gigice ta d’ago ido”doctor aiki kuma?”
“Eh dole ne cikin biyu ayi d’aya kodai aimasa aiki Wanda inyazo da k’arar kwana shike nan in kuma ba haka ba to saiya samu biyan buk’ata sosai to in har yana samun hakan kuma aka d’orashi kan magunguna sai kiga andace basai anyi aikinba”
Dik jitai gumi ya jik’ata tace “doctor abar magana aikinnan don Allah”
“To ai zab’i na gareki khausar in kinso sai a janye batun aikin amma cikin biyu dole ayi d’aya”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button