BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba daya ya rasa inda Zaisa ranshi don murna .kara komawa yai .gun hadiza yana fadin .yanxu me ake bukata na baby akaro . a haba Alh. Me zaa bukata yanzu .dik irin tarin kayan dakasa akai oda na baby .ai daga nan har shekara .babyn nan batada da bukar wani Abu .

Gyada kai yai yana leka fuskar babyn .yace ammafa hadiza. Kinmin wayo .babyn nan kamarku daya ba abinda ta baro naki .
Amma nanda shekara daya insha Allah zaki .kara haihuwa saiki haifomin me kama Dani.
Mirmishi kawai take ita dai .

Tofa aiki yasamu a inda ake nemansa .shirin bikin suna ake tukuru .rabon kati Alh yake tako ina na sunan tilon yarshi daya shafe shekaru goma yana fatan samu .

Ranar Asabar din data zagayo .akai gagarumin taron sunan Babyn Data amsa suna KHAUSAR .dik Inda ka kalla. Manyan jakunkuna zaka hango da hoton jinjirar ajiki an rubuta BABY KHAUSAR A.ABDALLAH

abokan kasuwancinsa daga kasa kasa sukazo tayashi murna .kuma ko wanne da irin gagarumar kyautar da zaiwa babyn da mamanta .
Haka dai akasha shagalin suna .aka kashe naira kamar ba gobe .Yarinya fa tayi goshi .don ta Tara abinduniya.matuka kama daga sutturu .mota gida .dakuma tanfatsetsan kanfanin da mahaifinta yaimata .kyautarsa .da sunanta ajiki.

????????????????????
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????

BABY KHAUSAR

            NA

LAYUZA KABIR ADAM

      1⃣3⃣

Sannu sannu yau gashi baby khausar .kwananta Arbain a duniya tayi kubul kubul da ita ga wani kyau da Allah yaimata baiwa dashi

Soyayyarta kuwa azuciyar mahaifinta baa magana don indai ya fita .office kafin ya dawo ya kira waya kusan sau goma yana tanbayar lafiyarta

Inkuwa yana gida ko baa dakin mamanta zai kwanaba .sai ya dauketa yaje bangaransa da ita yaita mata wasa .haka zasu shashance shida Bilal gurin mata wasa ita kuma tana bangale baki..
Don shi Bilal yanzu bashi da wani aiki Wanda yawuce wasa da baby .yana dawowa skl zai zo bangaransu .yana knocking .yana fadin. Aunty budemin kofa nazo gun Sister na .baby haka zaizo .yazauna yaita mata .wasa .
Tun momynsa tana hanashi .tamai fada ta bigeshi .amma yana share hawaye zai koma.

Wannan dalilin yasa bakin cikin hjy Amina karuwa don haka .tasami wata kawarta hjy maryam take bata labarin matsalar datake ciki
Mirmishi hjy maryam tai tace to ai hjy Amina tun farko lefinki ne .
Mun Dade muna baki shawara akan kibi hanyarmu . yanzu matsalarki zata warware amma .waike ta Allah saiki rinka barin bakin cikin da namiji yana Neman kasheki

Jijjiga kai tayi tace .gaskiya hjy maryam nikam bazan iya bin malamai ba . sam wannan hanyar bata birgeni .kara dai .inta mai hayaniya muyi fada .akan inbi malamai
. to tunda kuwa haka ne sai kicigaba da zuba ido kina ganin bakin ciki .wlh kina zaune kwanan nan zaki ganta da wani cikin badai tayi arbainba .zakisha mamaki.
Itadai hjy Amina haka ta tashi tayo gida
Jiki a sabule.
Gashi yanzu yayarta hjy halima basa kano .sun koma Lagos .don anyiwa mijinta transfer a gun aiki. Sun koma can gaba daya
Da tana nan ma taje gunta tasan ko ba komai Tamata magana me dadi taji sanyi aranta .koda bazatai aiki da maganarta ba

Shirye shiryen tafiyarsu kasashe shida shida hadiza  Alh.yasa agaba kamar yanda yai mata alkawari. 

Yanzu saura kwana biyu su tafi.
Don haka .yasami momyn Bilal a daki .yace
Amina kamar yanda kika sani jibi .laraba .zamu tafi Dubai nida hadiza daga nan zamu zazzaga wasu kasashen. Yanzu ga wannan calk din .dik abinda kuke bukata keda .Bilal ku dibi kudi .iya abinda kukeso. Da sauran hidimar gida da albashin Maaikatan gida dik kiyi.

Haba Alh. Yanzu kayimin Adalci Kenan kadauki hadiza .ku tafi ni kabarni agida?
Da mamaki ya kalleta yace banganeba Amina me kikeson cewa .meye abin rashin Adalci anan .sau nawa muka fita kasashen duniya dake .ko saudiya sau nawa kikaje .fitarki bazai kirguba Amina
Amma tunda na auri hadiza .ko Abuja kinga naje da ita?
Kije dik abinda zakice kice .tunda bakiga Adalcin da nake .mikiba.

Fita yai ya koma dakinsa ransa yana suya .
Jin andafashi yasa ya jiyo yasan Bilal ne
Ya akai my son .Dad bacci kakeyi ne .inata maka magana bakajiba .a a .my son ba bacci nakeba . ya akayi. Dad kaje ka dauko mana Baby .muyi mata wasa .
A a Bilal kaina ciwo yake bari zuwa anjima zan dauko mana .ita.
Jibi zamuyi tafiya .ma My son zaka daina ganin sister dinka .
Ware ido yai .kai indai da baby zaa tafi nima zanje .
A a Bilai kaga bukiyu Hutu ba sai zuwa next week. Da kunyi saimu tafi tare.

????????????????????????????
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????

 BABY KHAUSAR 

           NA 

LAYUZA KABIR ADAM

YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA UBANGIJINMU ALLAH .TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD
(S.W.A)

        1⃣4⃣

Karfe goma Am jirginsu yatashi .zuwa U.S.A. .Wanda shine karo na farko da hadiza ta taba barin gida Nigeria. Cikin farin ciki suka sauka a hadaddan hotel. Wanda Alh.yakamamusu daki na Alfarma.kwanansu goma a a kasar Sukai gaba haka sukaita zagaya kasashe .sannan sika yada zango a saudiya .inda hadiza taita kuka saboda dadi .yau gata a garin manzo . Haka sukai ummara . sosai takewa iyayenta addua .tana nemarmusu Dacewa da jannatulfirdausi.

 Sunyi tsaraba kamar baa San darajar kudiba Baby khausar tasha Kaya don dik inda Dad dinta yaga Kayan yara kama daga suttura zuwa Kayan wasa da Kayan kwalliyar dakin yara haka yake kwasar mata .

Ita kuwa hadiza Bilal da mom dinsa tafi dibarwa .da iya Abu .sai Mlm Khalil da sukaiwa tsarabar Jallabiyu na maza .da huluna .da takalma

Ranar da sukai Wata biyu da kwana biyu suka dawo gida dikkansu sun canja .sunyi wani irin kyau .fatarsu ta kara mirjewa .musammam baby khausar datake Yarinya .yanzu watanta uku da rabi .tayi wayo sosai .

Dawowar tasu ta tsakar darece .don haka ya kwana dakin hadiza .yana fitowa daga masallacisallar asuba . yashiga bangaran Hjy Amina .lokacin tana toilet. Tana fitowa
Taganshi gefan. Kujera dake dakin zaune .yanajan casbaha dinsa .kallo daya tamai ta kauda kai ta dauki praye mat .tashinfida tare da tada sallah .
Baice mata uffaanba .saida ta idar .sannan ya dubeta .yace .Amina bikiganni ba ne.
Na ganka .meya faru .ko kaga wani Abu ne
.a a banga komaiba na sameku lfy?
Ya hidima da gida ya my son .dik lfy .ko bakaga alamar hakamba .

Mamaki ne yake cin ransa .matuka na yanda gaba daya Amina ta canja rayuwarta .rabon dayasami kwamciyar
Hankali.daga gareta tun randa .taji maganar auransa.
Amina daya sani da hankali da nutsuwa .amma yanzu dik babu sai wulakanci da raini. Wanda da dik ba dabiunta bane .
Shin wai. Daman dik mata haka suke
Da irin wamnan banzan kishin .
Amma ai ko kishinne. .yakamata ace xuwa yanzu ta hakura .tsawa shekara da rabi .da .auran amma haryanzu .kullum wulakancinta . karuwa yake .akanshi……. Tsawon mintina yana wannan tunani .daga bisani yamike yashiga dakin Bilal yasameshi .bai tashi a bacciba. Shafa kansa yai sannan yafito yashiga .bangaransa .
Dik yai kura .don haka .ya dawo falon .hjy ya kwanta kan 3 sitter. Yaci gaba da .jan casbahansa.

Rayuwa .gudu take .yanzu .gashi baby khausar .takai shekara 2 a duniya .kuma tuni an Dade da yayeta tafiyarta take ko ina .gwanin shaawa da ita . shakuwa ce bata wasa ba tsakanin ta da Bilal . wanda da gwarancin ta take cewa .broth. Shikuma yace mata sis baby. Inya shigo gunsu .da gudunta take rungumeshi. Tana zillo.shikuma ya goyata yaita mata doki .abinda tafiso Kenan.

Shikuwa Bilal ko a school. Kullum ko islamiyya koda yaushe .sister na baby kaza kanwata dik tafi kannanku kyau ni kanwata .kama take da Fulani da larabawa.don haka dik wanda yasan Bilal yasanshi da labarin baby khausar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button