BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Taku ce
Layuza kabir Adam????‍♀
????????????????????????????????????
BABY KHAUSAR

       NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate,motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍

       1⃣1⃣2⃣

Haka ta tashi tai wanka ta tsara kwalliya dik jikinta amace yake ayau kam tasa aranta zata bawa Bilal hak’k’insa taza faranta ransa matuk’a,

Dik shirin tararshi da tai bai dawo da wuri ba har akai sallan isha’i ga wayanshi akashe inta kira dik sai ta shiga Damuwa, zama tai a parlour ta rafka tagumi tana tunanin dalilin rashin dawowarsa, jitai an rufe mata ido ta baya ta tsorata sosai ta bud’e baki zatai magana taji an d’ora hannun abakin cikin tsoro ta shiga k’ok’arin k’wacewa, ” Ohh bloody sarkin tsoro to d’an uwanki ne”
Jin muryansa yasa ta fad’a jikinsa tana sauke ajiyan zuciya ya rungumeta yana shafa kanta”bloody kinga na dad’e ko? Wlh bak’i mukayi suka rik’emu a office kiyi hak’uri”
“Ba komai broth amma meyasa ka kashe wayanka?”
“Muna meeting ne shiyasa”
“To meya faru naji muryanka haka kamar ranka a b’ace?”
“Banjin dad’i kaina kemin ciwo sabida k’wak’walwata yau dik bata huta ba”
“Ok sannu muje kayi wanka kaci abinci zai daina”

Ruwan wanka ta had’a masa yashiga yai yana fitowa ta taimaka mai yasa kaya ya fito dining sukaci abinci, yana dawo wa d’aki ya yau gado suna d’an hira ko 10 minutes baiba yai bacci ,
Kallonsa tai tai wani tunani aranta kawai sai tai mirmishi ta kashe haske itama ta kwanta.

Da safe ma da wuri ya shirya yace inta shirya driver ya sauketa a skul don zasu k’arasa meeting da bak’insu na jiya yana so yaje da wuri yaita bata hak’uri .

 Kwata kwata yau bataji dad'in zuwa skul ba don ta saba da tafiya tare dashi suna tafe suna hiransu me cike da shak'uwa.

 Yau ma bai dawo da wuri ba amma dai yanata kiranta awaya yana bata hak'uri, sai wajan tara ya dawo yauma taci kwalliyanta tasha kamshi dik inda ta motsa k'amshi ke tashi tana zaune parlour tana jiran dawowarsa ya shigo    ta mik'e don tararsa da sauri ya k'araso ya rungumeta itama tasa hannu ta rungumeshi suna tsaye kusan 3 minutes sannan ya cikata ya zauna itama ta zauna gefansa tana masa sannu da zuwa ya amsa muryansa a dishe kallonsa tai  tace"ya dai ?"

“My blood mura tamin mugun kamu bikiji yanda kaina ke Sarawa ba”
Cikin kalan tausayawa tace”wayyo sannu ga muryanka harta dashe”
Hannunsa rik’e da Kansa yace ” Tai makamin da copy me zafi insha ko mak’ogarona zai min dad’i”
Kitchen ta nufa dik masu aikin sun tafi makwancinsu ta jona kettle tasa ruwan sannan ta d’auko citta, kanumfari, na’a n’aa,lemon grass da d’an zob’o kad’an tasa aciki tasa Lipton da suga ta rufe, dawowa tai parlour ta sameshi dafe da kan yanata aikin face hanci da gani kaga Wanda sabuwar mura ta kama sannu tamai ta wuce ta d’auko mai magunguna tare da ruwa ta kawo mai, d’an mirmishi yai yace”hhhmmm kaga anfanin zama da doctor kenan “
D’an mirmishi tai kawai ta tsiyayo ruwan tare da b’allo maganin ta mik’a masa yashanye ta tashi ta koma kitchen d’in don duba shayin ai kuwa tai sa’a harya tafasa nan ta tace ta zubo mai a cup ta kawo mai , saida ya d’an Sara ra sanan ya kurb’a kallonta yai yace”um um um wannan shayin daga ina kinji dad’i kuwa?”
D’an mirmishi tai kawai, nan da nan ya shanye yanata santinsa ita dai mirmishi kawai takeyi, ya mik’e”zo kirakani d’aki in huta.
Bayan yai wanka ya fito kaya kawai yasa ya kwanta, taje dukinta tana dawowa taga yai bacci kawai sai taji ranta ya b’aci juyawa tai ta koma d’akinta tana zuwa ta fad’a gado zuciyanta a dagule ko mene dalili oho, ta dad’e batai bacci ba tana juyi ,hak’ik’a tsakanin jiya da yau tasa aranta zata gwadawa mijinta k’auna da kulawa tasani sarai kullum saiya nuna mata yanada buk’atarta amma take kaucewa shi kuma don kar ranta ya b’aci saiya hak’ura amma dai zai raba dare yana wasa da dik inda yaso ajikinta Wanda ita kanta in yanayi sata yake cikin dad’i, Gashi a irin haka ciwo ya kamashi ta sanadinta kuma sanda taso faranta mai shi kuma bai buk’ata ba ko d’an wasan ma da yakeyi jiya da yau baiba kodake tasan rashin jin dad’in ne ya hanashi nema amma tasan ko gobe muran da kan sukai mai sauk’i zai buk’ata tunda ta fuskanci me buk’atar ne, da wannan tunanin bacci yai gaba da ita itama.

 Bayan ya dawo sallar asuba kai tsaye d'akinnata yai ya sameta zaune kan prayer mat tana addu'a, zama yai kusa da ita bayan ta shafa ta juyo ta kalleshi"Barka da asuba, ya kan da muran?"

“Kin tashi lfy da sauk’i naji dad’in maganin nan fa a bani na k’ara”
“To amma saikayi breakfasts zakasha kaga jiya bakaci abinciba kai bacci”
“Eh shine don kinga bacci ya d’aikeni kika gudo baki tasheni munzo mun kwanta ba jiya da yau duk ad’akina na kwana”
Batace mai komai ba sai mirmishi da tayi ya ruk’ota suka zauna bakin gado ya kalleta sosai sannan yace”kiyi hak’uri Baby jiya wajan sha d’aya Dad ya kirani don kiranne ma ya farkar dani naga bakya d’akin, ya sanar dani yau zamuyi tafiya zuwa Adamawa kuma zamu samu kamar kwana hud’u ko sati d’aya dama ya dad’e yana sanar dani tafiyar to bata taso ba sai jiya da dare ya sanar dani tunda ya kirani ya fad’amin na shigo in sanar dake naga kinyi bacci don haka na kyaleki “
Jitai gaba d’aya kanta yai mata nauyi taji zuciyanta ba dad’i tadai daure tace”me zakuyi a Adamawa “
“To nima ban saniba amma dai ko menene na fuskanci me mahimmanci agun Dad don ya dad’e yana fad’amin zamuje garin dik sanda tafiyar ta taso, yacemin k’arfe biyu zamu tafi in munyi sallar jumma’a”
“Shiru tai tana tunani aranta tace”broth to don Allah in koma gida kafin ku dawo kaga zaman ni kad’ai wlh bazanji dad’i ba “
Shiru shima yai yana tunani sannan ya nisa yace”To Baby in kinga hakan zai saki kwanciyar hankali ba matsala farin cikinki shine nawa”
Wani dad’i taji ya kamata ta ruk’o hannunsa”yawwa broth na gode kaga in ina kusa da mami nah zanji dad’i”
Lakace mata hanci yai yace “ke wai baki gajiya da gidane bikisan kin girma bane komai kice mami komai mami kamar bata yaye kiba.”
Dariya tai tace”wa yacema me uwa yana girma ni dik sanda nake kusa da ita ji nake kamar yar Baby”
“To ai dama y’ar Babyn ce”
Dariya tai don tasan me yake nufi dan had’e rai yai yace”wato Baby ko kewana bazakiyi ba ko”
“Haba wa yace bazanyi kewanka ba?”
“A ‘a naga alama ne da Dana fad’a miki naga kin canja fuska nai zaton don baki son in tafi in barki ne amma kinajin zaki koma gun mami kika saki fuska alamar daman hade ran na tsoron zama ke kad’aine”
Ganin yanda yake magana seriously yasa ta d’ora kanta a k’irjinsa cikin shagwab’a tace” Allah broth zanyi missing naka,kawai don ba yanda zanyi ne yasa na nunama ba komai amma k’asan raina ni kad’ai nasan me nakeji”
Wani farin ciki ne ya lullub’eshi ko ba komai yasan yanzu ya sami wani matsayi a zuciyar Baby ya k’ara sata a k’irjin nasa yace ” Karki damu insha Allah ma bazamuyi satinba zamu dawo ni kaina don tafiyar ta Dad ce da ba’inda zani, amma ina tausayin kaina na irin halin da zan shiga in ina nesa dake, zanyi missing d’in kwalliyar nan me Jan hankali zanyi missing wannan k’amshin me rud’ani sannan zanyi missing d’in twins d’ina”ya fad’a yana shafa Boob’s d’inta. Tura kanta tai sosai cikin k’irjin don taji kunyar abinda yace, hannu yasa ya zame hijab d’in jikinta ya shiga shafa gashinta daketa k’amshi zuwa gadon bayanta, cikin sanyin murya yace”My blood naji labarin Islam nada ciki ko?”
D’agowa tai ta kalleshi cikin alamar Tambaya ganin kallon da take Maine yasa yai mirmishi yace”meye kike kallona kamar baki San maganarba bayan kuma nasan dik Wanda zai fara sani bayan su saike ko ba haka ba?”
“Um haka ne amma kai waya fad’a maka?”
“Ya kike tanbayana waya fad’amin tunda dai ke biki fad’anba ai shi kenan”
“Sorry ita tace Karna fad’awa kowa fa, don Allah a ina kaji sis ta banu da rashin sirri”
“Ah meye abin rashin sirri to ba a duniya naji ba Wanda yai cikinne ya fad’amin”
Da sauri ta rufe idonta da hannayenta biyu” kai broth ya da wannan maganar k’anwarka ce fa”
Dariya yake sosai ya jawota jikinsa “meye abin rufe ido ke bakece me cikinba kuma dan nace Wanda yai cikinne ya fad’amim sai ya zame miki abin jin kunya?”
“Don Allah kayi shiru haka ni ba ruwana wlh”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button