BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Ciki ta koma kai tsaye tai d’akinsa ta fara shirya mai kayansa cikin trolley back bayan ta gama ta gyara mai d’akin ta duba agogo taga har k’arfe tara da rabi don haka ta koma d’akinta ta kwanta cike da tunanin irin salon soyayyan Bilal mirmishi tai ta mik’e taje kitchen bayan sun gaisa dasu ta shaida musu ” Don Allah ina son Ku shirya min snacks kamar kala uku amma cikin awa biyu zuwa uku”
Cikin girmamawa suka amsa nan ta fice ta koma d’akinta.
Bai dawo gidan ba sai da yai sallar jumma'a k'arfe d'aya da kwata, da murnarta ta tareshi ya d'agata sama ya cafe yana juyi da ita dariya take sosai tana" broth karna fad'i ka rik'eni sosai"
Kwantar da ita yai k'irjinsa shims yana dariyan " To kwanta tunda naga ke matsoraciya ce"
Kwantar da kanta tai a k'irjin tai luf, shi kuma yaita shafata yana sun sunarta,
Cikin kunnanta yace”bamu da ishashshan Baby muje d’aki ki shiryani “
Ruwan wanka ta had'a mai ta fito"Broth ka shiga kayi"
Ido ya kashe yana magana da shagwab'a kamar ita " in shiga inyi ko mu shiga kiyimin"
Juya baya tai tace”um um nidai bazan shiga ba kai dai kaje kayi “
“To ciremin kayan”
Taimaka mai tai ya cire kayan ganin yana shirin janta zuwa toilet d’in yasa ta fice da gudu tana mai gwalo,
Bayan ya fito ta taimaka mai ya shirya suka fito don yaci abinci suna zaune a dinin ma zunzurutun k’auna yake nuna mata yana fad’amata kalamai masu sanyi da sanyaya rai ita kam yau jinta take wata iri kamar asama take wani farin ciki yake sata ashe haka soyayya take da dad’i Kai masha Allah da lamarin k’auna ????
Dad yana kiransa taji gabanta ya fad’i don tasan tafiyar tazo, bayan ya gama amsa wayan ya juyo ya kalleta yace “To Dad yace in fito “
Marairàice fuska tai har k’walla tazo idonta ya kamota yasata ajikinsa yana fad’in “karkiyi haka Baby karkiyi kuka zaki kashemin jiki ki mana addu’a Allah ya kaimu lafiya ya dawo damu lafiya, kinji”
Kuka take sosai tana tura kanta tsakanin wuyansa dik shima jiyai jikinsa ya mutu d’agota yai yasa bakinsa kan fuskanta yana lasar hawayen cikin wani salo me shiga jiki hannunta ita ma tasa tana shafa bayansa shikam dikkan sassan jikinta ba inda bai kai hannun dik sun shiga shock ganin yana shirin fad’uwa yasa yayi saurin jingina da jikin bango itama ta fad’a ya matseta tsam sunata kissing juna a rud’e kamar wanda zasu shanye bakin juna sun d’au tsawon lokaci suna abu buwa tunowa da yai jiransa Dad yake yasa ya zame jikinsa ya ruk’o hannunta suka zauna bakin gado ” My blood bazan gaji da baki hak’uri ba bari in tafi,”
Tashi tai ta jawo mai trolley d’in ya amsa yakai parlour ya dawo kud’i ya nuna mata a cikin bedside yacemata dik abinda take buk’ata ta d’auka, yasa hulanshi da takalmi yaja trolley back d’in suka fita driver ne zai kaishi gidan sai ya dawo da motan, sanda zai shiga motan ya damk’e hannunta sosai sannan ya d’agashi zuwa bakinsa yai kissing d’insa sannan ya cikata yana d’aga mata hannu, itama hannun take d’agamai idonta cike da kwalla ganin motan ta fita a gidan ta koma ciki da gudu hawaye nabin idonta,
Tana shiga taji wayanta nata ringing ta d"auka Islam ce " hello sis ya kike"
” lafiya qlau ya gida”
“Meya faru naji muryanki kamar na kuka”
“Isy wai Dad ne zaiyi tafiya harta sati kuma yace broth be zai rakashi yanzu hakama ya tafi yana hanyar zuwa gidan”
Ta karashe da kuka, mamaki ne ya kama Islam yanda taji Baby na kuka bayan tasan ba wani zaman dad’i suke ba toko an dai daita ne oho”
” meye na kuka haka Sis ai kamar yau zakiga sun dawo kiyi hak’uri kinji”
Share hawayen tai tace “sis kuka kinga ya barni inje gida in zauna harsu dawo Dad d”in ya hana”
“Kiyi hak’uri ba komai tunda ga soul ai zaman bazai miki yawa ba”
Haka dai Islam taita rarrashinta harta warware sannan sukai sallama.
Haka ta yini ba dad'i tanata tunaninsa ita kanta mamakin kanta take wai meke damuntane akan Bilal jinsa take aranta sosai gashi yau ya gwada mata k'auna da salon so me tsayawa arai ,
Tana sallar isha’i ta kwanta har bacci ya fara d’aukanta taji muryan wayanta cikin bacci ta d’aga ” hello bloody nah “
“Na’am my broth kunje lfy inata kiran numbobinku bai shiga ba”,
“Eh yanzu muka sami network ne tun d’azu nima nake son jinki, ya gidan ya kewana?”
” hhhmmm gani ni kadai ya ina Dad d’in?”
” bama kusa waje na fito don nafi samun sakewa”
“Hhhmm mene don kayi waya gabansa”
“Um um ina son fad”in abubuwàne”
“Name ?”
“Na k’auna, na gode naga ansamin snacks ajakana har munci nida Dad yayi dad’i”
“OK”
“Bari in koma d’aki miyi chart.
“Um hmmm ka gaida Dad d’in”
Kuyi hakuri da wannan????…
Taku ce
Layuza kabir Adam ????♀
0 ????????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate, motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????✍
1⃣1⃣4⃣
Soyewarsu sukeyi
chatting sosai sabida waya bazata yuyu gaban Dad ba don haka suke kwashe lokaci suna shan k’auna ta chart har sukai kwana biyu kullum inta dawo skul bata komai sai k’auna ranar kwanansu na uku take tanbayarshi wai ba aiki sukeyi acan d’inba taga koda yaushe yana free dariya yai ya bata amsa da ziyara kawai suka kaiwa abokan Dad, b’ata fuska tai kamar yana kallonta tace”yanzu kai ziyaran abokan shine Dad sayya d’auke ka”
Y’ar dariya yai yace”To dawa zai tafi in bani ba ko d”an wani zai aro ya rakashi”
Tura baki ta k’arayi tace”Nidai Wlh wannan tafiyan bata minba”
Mirmishi ya k’arayi sannan ya k’ara rubuta mata amsa” meyasa bikiji dad’inta ba ko dan an rabaki da masoyinki”
“Hhhhmm” kawai ta rubuta mai,
” Ko nima kullum saina shiga kewanki in na kwanta intajin ba dad’i na saba in kwanta ina jin d’iminku ina wasa da twins d’ina koda baza abarni nakai ga gaci ba”
” ???? rife ido ta tura mai alamar taji kunya,
“Mene abin jin kunya bud’e idonki kawai aiba wannan a tsakanin mata da miji “
“Hhhmmm”
“Wai mene ma’anar wannan hmmm d’in daga nai magana ace hhhhmm”
“Ba komai”tace yace “OK bari anjima ma had’u naga kamar Dad zaiyi magana dani.
Ranar kwanansu na hud’u a yola Su Baby na skul Islam ta kirasu bazata shigoba tana fama da zazzab”i sannu sukai mata sannan suka fara mata tsiya wai laulayi ne na masu ciki sai tai hak’uri,
Nan Aisha taje office d'in doct Amin take shaida masa ya barta in sun tashi taje gidan Islam ta dubo ta kafin ta wuce gida ya amsa mata da taje jin haka yasa Baby kiran Bilal itama ta nemi izinin zuwa shima ba musu ya barta.
K”arfe biyu suka gama lecture suka wuce gidan Islam d’in da sauk’i suka sameta nan suka ci abinci suka baje hira,
Suna nan wata mak’ociyar Islam d’in sameera ta shigo bayan sun gaisa ta fito da magunguna a Leda take ce musu na sayarwa ne in zasu siya, Islam ta siya Aisha ta siya don su sun San ingancinsa tunda sun siya sosai awajanta,
Baby ce ta kalli Islam tace”sis meya had’aki da wannan aikin kina fama da yaron ciki”
” ba nawa bane ke nasiyawa ki gwada kiji yanada kyau”
Kawai tsintar kanta tai da amsa har tana fad’in” To amin bayanin yanda ake amfani dashi”
Bayan ta gama jin kan zancan ta gutsura taji kallon Aisha tai tace ” kai sis kinji dad’i kuwa”
dariya suka fara mata Islam tace” a Wanda mami ta had’a mana na aure akwai way’anda sukafi wannan dad’i kije kiji”
Hhhhhhhmmmnnm Baby sarkin son dad’i taji gumba me gard’i nan tasa agaba tai ci harda k’ara siyan wasu kalolin ta cika jaka,
Sukuwa sabida tsabar mugunta sai tunzurata sukeyi tana sha Aisha harda tashi ta deb’o madara ta had’a mata wani a k’aida d’aya bisa uku ake sha amma saita had’a mata biyu bisa uku tace shima da gard’i ai kuwa baby kamar an mata baki taita sha,
Tashi tai zuwa d'auko wayanta data sa a charge cikin d'aki tana shiga sukasa mata dariya Islam tace" ai k'ara taji yanda broth yakeji in yana buk'atarta don Wlh wannan da kika bata ba k'aramim hautsina ni yaiba lokacin da nasha gashi yak'i dawowa da wuri naita juyi agado koshi kansa daya dawo saida ya gane ina cikin feeling"
Dariya Aisha tai tace ” ke nima dana fiki hauka kamar yanda na had”a mata haka nasha ai kuwa Kafin dare haka naita liking ina k’walla sabida feeling”
Dariya suka kyalkyale Islam tace”kai abin tausayin gashi broth baya gari daya kwashi gara yau”
Dai dai nan ta fito hannunta rik’e da waya tasa a kunne tana fad’in ” wai don Allah broth har yanzu Baku gama ziyaranba ya kamata Ku dawo haka”
Kafin ya bata amsa Islam tace”kai sis wannan zalama har ina ki barshi ya gama abinda yaje yi”
Dariya yai don yana jin abinda Islam tace yace”kicewa Islam ina jinta tana tsokanarki zamu b’ata, kinga Wanda muke jira yazo zamu ci gaba da tafiya don a hanya muke zuwa wani k’auye acikin garin bari sai munje ko”
“OK” ta kashe wayan tana hararansu don dik sun zubo mata ido,